Yadda Ake Hada Lemon Na’a-Na’a Da Kokumba:
Rahima Shehu Dokaji
Gurji, wanda aka fi sani da Kakumba, da Na’a-na’a nau’in kayan abinci ne da suka kunshi sinadarai masu amfani sosai ga lafiyar jikin dan Adam.
Kakumba na dauke da wadataccen ruwa a cikinsa, da ke taimakawa wajen rage kiba da bai wa jiki ruwan da yake bukata.
Girke-girken Azumi: Yadda ake yin Tsiren Dankali
Yadda ake girka Alalen Doya
A hannu guda kuma na’a-na’a na taimaka wa jiki magance matsalolin magwas da kumburin ciki tare da taimaka wa kwakwalwa da kuma hana warin baki na larura.
Kun ga ke nan hada wadannan abubuwa biyu a waje guda, ba karamin lafiya zai kara wa jiki ba.
Kayan hadi:
💧-Na’a-Na’a
💧-Kokumba
💧-Dafaffen sukari/Syrup
💧-Filebo
Yadda ake yi:
Da farko a samu Na’a-na’a koriya sosai sai a wanke ta tas.
Sai a markada ta daga nan sai a tace a ajiye ruwan a gefe guda.
A samu Kokumba mara daci a yayyanka ta a markada a tace.
Sai a dafa sukari har sai ya narke ya zama tsararo (syrup).
A juye tattaccen ruwan Na’a-Na’a da na Kokumba a kofi.
Dag nan sai a dauko syrup din a zuba a kan hadin.
A zuba filebo na ruwa, dandanon da ake so, a ciki.
Sai a sa a firiji, ko a jefa kankara a ciki, idan ya yi sanyi sai sha.
0 Comments