Wasu Samfuran Sakonnin Waya Da Zaki Turawa Saurayinki Da Kuka Bata Domin Neman Sulhu:


Wasu Samfuran Sakonnin Waya Da Zaki Turawa Saurayinki Da Kuka Bata Domin Neman Sulhu:

#Tsangayarmalamtonga 
SHARE 💞

Ba duk namijin da kuka bata bane zaki samu lokacinsa cikin sauki na ku tattauna ba. Sai dai cikin dabarun shawo kansa akwai aika masa da text domin rage zafin fushin da yake yi na rabuwa dake.

Ga wasu samfuran sakonnin fa zaki iya turawa tsohon saurayinki domin dawowa da hankalinsa gareki.

 
1: Assalamualaikum!
2: Ina Kewarka.
3: Zamu Iya Magana?
4: A Kullum Dad Shiga Raina Kake Yi. 
5:Mun Hadu Da (sunan mutum) Yace Na Gaisheka.
6: Naji Labarin Abun Alherin Daya Sameka Ina Tayaka Murna.(idan ma jaje ne sai ki masa).
7: Ko Kasan Daga LokacinDa Muka Bata Zuwa Yanzu Nan Na Kasa Ganin Namiji Irinka A Kyau, Hali, Dabi'a Da Tsoron Allah.
8: A Duk Lokacinda Na Tuna Rashin Kyautawar Dana Maka Bana Sanin Lokacinda Nake Kwalla.
9: Ka Yafemini Koda Bazaka Soni Ba.
10: Ko Ka Taba Tunanin Cewa Akwai Wata Rana Da Za Kwana A Yini Ni Da Kai Bamuga Juna Ba?


Ki tabbatar duk sakon da zaki tura masa sakone da kike bukatar ya amsa miki. Misali sallama da kuma sanin lafiyarsa.

Wadannan sakonnin zasu rage kaifin fushin da yake dake. Zasu kuma zamemasa hujjar soma kulaki idan a baya ya ci alwashin ba zai sake nemanki ba.

Post a Comment

0 Comments