Gyaran Jiki Da Azumi



Ya kamata Uwargida ki kasance mai gyaran jikinki da azumi kar ki ce wai don azumi ne idan kin yi wanka da safe shike nan haka za ki shiga kitchen sannan kuma idan kika fito haka za ki kwanta da warin hayaki ko kuma na abinci.

Da azumi ma yana da kyau ki zama mai kula da jikinki, za ki tsara yadda za ki yi aikinki saboda ki fito a kicin da wuri saboda ki samu damar gyara jikinki kafin magariba, idan kin gyara jikin ki ke kanki za ki ji wani dadi, kin yi wanka kin yi kwalliya, amma ba ki zauna dagajaja ba idan maigida ya kalle ki baya so ya kara kallonki, saboda ke ga ki kin yi azumi wai kin gaji ba za ki iya gyara jikinki ba.

Yadda Ake Hadin Body Spray (Turaren Jiki)
Yadda za ki tsara shiga kicin, ya kamata a ce kin shiga kitchen kamar karfe biyu na rana wato bayan azahar kenan, da zar kin shiga sai ki fara da abinci, sai ruwan shayi, idan shayi za ki yi ranar, idan ma kunu za ki yi duk za ki iya farawa da su ki yi kina zubawa a flask.

Post a Comment

0 Comments