DAUSAYIN RAMADAN (DARASI 3)
RAMADAN WATAN NASARA NE AKAN MAƘIYA
20. Watan Ramadhan wata ne na samun nasara a kan maƙiya saboda addu'o'in da ake yi domin samun nasara, domin a zamanin Ma’aiki ﷺ, musulmai sun fita yaƙi su ɗari uku da 'yan kai, mutum biyu ne akan doki; saba'in kuma suna kan raƙuma, amma duk da haka Allah ﷻ ya ba su nasara, a kan mushrikai wanda adadin su ya kai kimanin mutum (1,000) wasu suna kan dawakai, guda ɗari bakwai (700) suna kan raƙuma, wannan kuma ya faru ne a cikin watan Ramadhan a shekara ta biyu bayan hijrah. Wannan shi ne yaƙin Badar.
21. Haka nan Allah ya taimaki muminai a cikin yaƙin Fatahu Makkah, shi ma da aka yi shi a cikin watan Ramadhan a shekara ta takwas (8) bayan hijrah, domin Manzon Allah ﷺ ya shiga garin Makkah ba tare da yaƙi ba, ya yi kuma nasara. (14)
22. Sannan ana ninninka lada da kuma ninninka sakamakon duk wani abin alkhairi da aka aikata a cikinsa, Manzon Allah ﷺ ya fi kowa alkhairi ya fi kuma ninka alkhairin da yake yi a cikin watan Ramadhan a yayin da ya haɗu da Mala'ika Jibril. Manzon Allah ﷺ ya fi kowa alkhairi da kyauta fiye da iska ko tattacciyar iska mai wucewa.” (15) Wato saboda kyautarsa da alkhairinsa.
23. Watan Ramadhan wata ne na karanta Al-Ƙur'ani, Jibrilu yakan zo wajen Ma’aiki ﷺ a cikin kowacce shekara a cikin watan Ramadhan suna yin bitar karatun Al-Ƙur'ani tare. Manzon Allah ﷺ shi ne mafi kyautar mutane, kuma ya fi
yin wannan kyautar tasa ne a cikin watan Ramadhan a yayin da ya haɗu da Jibrilu. Lallai haƙiƙa Manzon Allah ﷺ shi ne mafi kyauta fiye da iska wacce ta taso. (16)
24. Azumin watan Ramadhan rukuni ne daga cikin rukunnan musulunci, wanda musulunci baya cika sai da shi. Haka kuma imanin bawa ba ya cika sai da shi, saboda hadisin Abdullahi Ɗan Umar RA, inda yake cewa, Manzon Allah ﷺ ya ce, “An gina musulunci a bisa abu biyar; na farko: shaidawa babu abin bautatawa da gaskiya sai Allah, sannan kuma Annabi Muhammadu ﷺ Manzon Allah ne, na biyu: tsayar da sallah, na uku: bayar da zakkah, na huɗu: azumin watan Ramadhan, na biyar aikin hajji ga wanda ya sami iko.” (17)
25. Shi watan Ramadhan wata ne na i’itiƙafi da lazumtar masallaci da niyyar neman kusanci ga Allah ﷻ, dalilin yin nafilfili da karatun Al-Ƙur'ani da ambaton Allah ﷻ da salati ga Annabi ﷺ da yin tasbihi da istigfari a cikinsa, shi ne hadisin Nana A’ishah RA, inda take cewa, "Manzon Allah ﷺ ya kasance yana yin i’itiƙafin goman ƙarshe na Ramadhan." Ma'ana, ya kasance ya kan tare a masallaci yana ibada a goman ƙarshe har Allah ﷻ ya karɓi ransa. Daga nan kuma matansa sun cigaba da yi a bayansa. (18) Akwai kuma hadisin da ya zo daga Abu Huraira RA, cewa, Manzon Allah ﷺ yana yin i’itiƙafi a cikin watan Ramadhan na kwana goma, amma a shekarar da Allah ya karɓi ransa ya yi i’itiƙafin kwana ashirin (20). (19) Don haka, ya kamata 'yan uwa musulmai a riƙa ƙoƙari a zage ɗantse idan watan Ramadhan ya zo a ƙara ƙoƙari fiye da wanda ake yi kafin zuwan watan Ramadhan wajen yawaita karatun Al-Ƙur'ani da sallah da salati ga Annabi ﷺ da istigfari da yawaita kyauta da sadaƙa da sada zumunci da makamantan su.
Zamu ci gaba insha Allah.
0 Comments