MINENE ALAQAR QANQANCEWAR MAZAKUTA KO GABA SAKAMAKON BASUR KO DANKANOMA:


MINENE ALAQAR QANQANCEWAR MAZAKUTA KO GABA SAKAMAKON BASUR KO DANKANOMA:

 BABBAR DA'AWAR MASU TALLAN MAGANIN ZAFI.

Da farko dai basur ko kuma haemorrhoid matsala ce mai zaman kanta. Basur yana faruwa ne ta dalilin kumburewar jijiyoyin dake daukar jini daga qarshen babban hanji da kuma dubura zuwa mayas dashi cikin jiki. Sannan su wadannan jijiyoyin basu da alaqa da jijiyoyin dake daukar jini daga mazakutar mutum.

ABUNDA KE SAKA QANQANCEWAR MAZAKUTA:-

Da farko dai tsawon mazakuta ahalin mutum ba yana cikin sha'awa ba kada ya kasa 3.66 inches,idan kuma yana cikin sha'awa zata kai har 4.59 inches zuwa sama. 

QANQANCEWAR TA YANA FARUWA TA DALILAI KAMAR HAKA:-

1,Yawan shekarun mutum wanda ke haifar da koma bayan halittar jiki.

2, yanayin kitsen da ya taru ga jijiyoyin jinin mazakuta sakamakon qibar jiki ka kuma rashin motsa jiki.

3, ga mutanen dake da teba ko tumbi,suna nasu ba qanqancewa bane,mazakuta tana jikin bangon cikin mutum ne to idan cikin mutum ya kumburo sakamakon qibar dake saka tumbi to sai yasaka mazakuta ta noqe cikin ciki amman ba rage girma tayi ba a zahiri amman a ido tunda ta noqe saikaga kamar rashin lafiya ne.

Mu daina damuwa da abunda masu tallan magani zafi suke da'awa akai sannan mudaina damuwa da kallace kallacen fina finan tsiraici zasu hana mu zama lpy.

Post a Comment

0 Comments