Kurakurai 5 Da Zaku Kauce Musu A Lokacin Zaben Wanda Za A Aura:


Kurakurai 5 Da Zaku Kauce Musu A Lokacin Zaben Wanda Za A Aura:

SHARE 💞
#TsangayarMalam 

Zaben mace ko namijin da za kuyi rayuwa na aure, abune da yake bukatar natsuwa da addu'a. Sai dai wasu da dama suna ganin hakan ba wani abun damuwa bane sai sunyi son ransu daga bisani kuma sai su dawo suna da sun sani.

Ga wasu kurakuren da akasarin mutane suke yi a lokacin zaben wanda ko wacce zasu aura.
 
1: Kada ku sake ku shigo da son rai wajen zaben abokin ko abokiyar rayuwa na aure.

Wasu da dama saboda tsabar soyayyar da suke yiwa wanda ko wacce suke son aure zasu maida matsalolin da suka gani a tare da shi ko ita tamkar ba matsalar da zasu iya jawo masu matsala bane bayan aure.

Kada ku sake ku shigo da son ranku komai kankantar sa a irin wannan yanayin saboda shi aure abune na har abada bana wani lokaci bane ake yinsa. Da zaran kun fahimci wata matsalar da bazai gyaru ba hakura da auren wannan shi yafi.

2: Manema da dama suna kuskuren zaban wadannan zasu aura tare da tunanin cewa zabin nasu shine yafi na shawaran da wasu manya ko makusanta zasu basu.

Duk mutumin da ya taba aure koda kuwa na mako guda ne yana da ko tanada abun da za a iya koya ko saurara na shawara a wajensu.

Kuyi shawara dana kusa daku da kukasan suna da kwarewa a fahimta da Zamantakewar aure akan zabin wadanda kuke so ku aura.

Kada ku kaucewa duk wani abun mara dadi da bako son ji akan wadannan da kuke son aurensu saboda soyayya.

Kuyi shawara da manyan da zasu iya fadamuku gaskiya komai dadinta wajen zaben wadanda zaku aura ba tare da daukar naku tunanin ya isa ku aiwatar ba.

3: Sau tari masu neman aure suna la'akari ne da wanda zasu aura kadai ba tare da dauko gaba dayansa ko dayanta sun duba ba.

Rashin asali na gari, ko rashin surukai masu inganci. Ko matsalar cuta ta gado duk wadannan abun dubawa ne wajen zaban wadannan zaku aura.

Kada ku dauka cewa tunda aboki ko abokiyar da za a yi rayuwa da ita babu wani illa a garesu. Illar wani nasu zai iya shafar Zamantakewar auren ku nan gaba. 

Don haka ajiye soyayya a gefe ku dauka wanda ake son aure a sekili harda tarihi da zuriyarsu domin kaucewa matsalolin da zasu iya tasowa a gaba.


4: Tabbas rayuwa cikin wadata akwai dadi, sai dai zaben namiji ko macen aure saboda kudi ko kyau babban kuskure ne.

Wasu sunyi aure suna matsiyata, yau sun zama miloniya. Wasu sunyi aure sunada miliyoyin kudi, yau sai an basu abunda zasu ci.

Babban abun la'akari ga mace shine abunyi ga wanda zai aureta. Kuskure ne ta auri namijin da bai aikin kome ko tace sai mai kudi zata aura.

Haka shima namiji ya ajiye zancen kyau ko kira a gefe, abubuwa ne da suke da takaitancen lokacin da zasu amfani maisu.

 Kula da hali gami da tarbiyar wacce kake so ka aura yafi neman mace mai kyau fuska.

5: Babban kuskuren da mata suke yi musamman zaurawa shine rashin fitowa fili suyi maganar Jima'i da mazan da suke so su aura.

Idan namijin da bazawara zata sake aure bai taba aure ba, kuma bai shahara a harkar zina ba, wannan babu matsala tana iya dai-dai tashi. Amma namijin da yake da iyali, ko ya taba aure ko yake zina. Fitowa fili kuyi zancen Jima'i yanada alfanu.

Mata zaurawa da dama sun kasa zaman aure saboda mazan da suka aura basu kai matsayin bukatarsu ba. Haka wasu sun gujewa zaman auren saboda mazan da suka aura sunfi karfinsu a Jima'ince.

 Wannan ne yasa dole ne ki fito ki sanardashi irin yanayinki tun kamin aure domin ku fahimci juna.

Su kuma samari da 'yan mata kuskuren da suke yi shine na kaucewa zuwa asibiti domin yin gwajin lafiyarsu.

Ana samun wasu mazan da suke da matsaloli na haihuwa da yadace su samu shawaran likita. Akwai wasu matan kuma tsabar zubar da ciki har mahaifarsu ya tashi daga aiki, hakan za ayi aure sai kuma ayi ta kukan rashin haihuwa bayan tun farko aka kaucewa ganin likita.

Ga matsalar haihuwa kadai ba. Akwai matsaloli da dama da suka danganci rayuwar ma'aurata da yakamata kamin suyi aure suyi gwajinsu.


Wadannan wasu ne daga cikin dubannin kurakuren da maza da mata suke tafkawa a wajen zabin wanda zasu yi rayuwar aurensu dasu.

Babban abun la'akari a harkar aure shine, muddin namiji ya saba da saki, haka zai tayin rayuwar aure na auri saki. Haka itama mace idan ta saba da sauya maza, haka rayuwarta zai kare.

Haka kuma yana faruwa ne tun a kuskuren farko na auren farko. Da fatan Allah Ya zaba mana abokan rayuwanmu na har abada.

Post a Comment

0 Comments