Irin Mazan Da Duk Wata Mace Ke Burin Ta Aura:
SHARE 🌼
#TsangayarMalam
Maza suna dauka cewa mata sun fi burin auren mai kudi, mota, gida, matsayi ko mukami. Sai dai wannan kuskuren fahimta ne.
Mace tana bukatan wanda take aure ya kasance da wadannan amma ba su bane ginshikin da zaka iya jawo soyayyar mace na gaskiya da su ba.
Ga wasu halayen da duk mace take burin auren namiji mai irinsu.
1: Namiji Mai Kamun Kai: Duk mace na burin ganin wanda zata aura namiji ne mai kamun kai bai da biye biye ko kula mata.
Namiji da ba a jinsa ko ganinsa a inda bai dace ba. Irin wannan namijin matan har ribibinsa suke yi.
2: Namiji Mai Saukin Kai: Duk mace tana burin rayuwa ne da namiji mai saukin kai ba mai wuyan sha'ani ba.
Mace tana son rayuwa da namijin da idan ya bata mata zai bata hakuri. Idan ta masa kuskure zai mata gyara ya yafe mata.
Namiji nara girman kai ko mai yawan fushi ko fada ba.
Wadannan mazan da zaran mace tayi dace da irinsa bata bari a rabasu sai aure.
3: Mai Taimakamata: Duk mace tana so tana ta auri na mijin da zai rika taimaka mata a aiyukan gida saboda sha'awar da yake da shi ko soyyyar da yake mata. Ba wanda zai harde kafa ba yana kallonta tana komai babu yabo sai mutan a gama da wuri.
4: Namiji Mai Rarrashi: Ba mai duka ka fada ba. Mace tana son ta auri namiji wanda ya iya rarrashinta koda itace da laifi ko da ita aka yiwa laifi.
Mata suna son auren namijin da zai fahimcesu a matsayin mata ba namijin da zai rika musu hukuncin irin yadda zai yiwa maza 'yan uwansa ba.
5: Na Mijin Da Yake Da Lokacinta: Ba duk lokacinda yake tare da ita ba wayarsa yake hira da ita ba. Ba kullum ya dawo gida ko ya zo wajenta hira aikin daya baro a ofis ko kasuwa sune zai ci gaba da yinsu ba.
Mace na son namijin da yasan lokacinta kuka yake bata shi yadda ya kamata.
Wadannan sune mazan da duk wata mace take burin samu a rayuwarta. Ta kuma dace yana da abun hannunsa da hakan zai zamemata gyara akan wadannan da muka lissafo.
Allah Ya kawo mazajen aure na gari.
0 Comments