Hanyoyin da zaka rabu da yin Istimna'i, wasa da Al'aura:




Hanyoyin da zaka rabu da yin Istimna'i, wasa da Al'aura:


Yadda zaka rabu da yin Istimna'i, wasa da Al'aura

Mutane da dama sun Dauki istimna'i a matsayin hanyar gamsar da Kan su ba tare da sanin illolin da Yake dasu a jikin su ba musamman bayan sun yi aure domin Yana jawo tarin matsaloli bayan Mai yi yayi aure ko mace ne ko namiji.

Duk da tarin illolin shi bai Hana wasu aikatawa saboda Dan jin dadin dake Ciki, abunda ya kamata ka Sani shine Bayan haramtawa da Allah yayi toh a likitance ma Yana da illoli masu tarin yawa

Duk dai a cikin wannan rubutu za kaga illolin shi, hanyoyin da za kabi har ka daina da taimakon Allah, Hukuncin da ma'anar shi.


Menene Istimna'i?

Istimna'i shine Mutum ya biyawa Kan shi bukata da Kan shi ta hanyar wasa da Gaban shi har ya kawo ruwa ne Mace ko namiji

Wannan shine ma'anar Istimna'i a saukakakken Harshe Kuma na San Mai karatu ya fahimta ko da bai Sani ba a da.

Menene Hukuncin shi a addinin musulunci?

Hukunci a addinin musulunci haramun ne bisa ga Ijtima'in malamai, wasu 'yan kadan daga cikin su sun karhanta shi.

Menene illolin Istimna'i?

Istimna'i Yana da illoli masu yawan Gaske shiyasa ake Yawan tsawatarwa a Kai domin gujewa haduwa da illolin na shi.

Daga cikin illolin Zan ambaci wasu a Nan;

🍀 Yana sa yawan ciwon Kai.
🍀 Yana jawo ciwon sanyi Mai tsanani sosai.
🍀 Yana sa yawan mantuwa da Rashin rike karatu.
🍀 Yana haifar da ciwon gabobi da kafadu Mai tsanani.
🍀 Yana jawo ciwon Daji wato cancer kenan a turance.
🍀 Mai Istimna'i Yana kasancewa da Yawan mantuwa.
🍀 Yana jawo cututtukan mafitsara ga Mai yin shi namiji ko mace.
🍀Idan Mutum Yana Istimna'i bazai iya biyawa aboki/abokiyar zaman shi bukata ba.
🍀Yana Sanya zuciya ta Rika bugawa da Karfi.
🍀Yana sa mutum Yawan damuwa, kullum xai kasance cikin Rashin natsuwa.
🍀Yana jawo Gaban namiji ya zama kankani.
🍀Yana sa Gaban mace ya bushe.

Wadannan wasu ne Kuma kadan daga cikin illolin Istimna'i, illolin suna da Yawan Gaske Kai dai idan kana cikin masu yi Kayi kokarin dainawa saboda kar lokaci ya kure maka.


Ta wace hanya zaka rabu da aikata Istimna'i?

Wannan tambayar tana da matukar muhimmaci domin mutane da dama suna yin ta, idan kana cikin masu tambayar tabbas ka samu maganin matsalar idan Allah Yaso.

Hanya ta farko itace Mutum yaji tsoron Allah ya bari tun kafin fushin Allah ya riske shi.

💧Ka daina kallon fina-finan Batsa.
💧Ka bar kebewa Kai kadai.
💧Ka nisanci duk abunda zai iya tayar maka da Sha"awa.
💧Kayi aure, Idan ba kada Halin yin aure ka yawaita yin azumi.

wadannan sune hanyoyin da za kabi ka rabu da Istimna'i insha Allah.

Post a Comment

0 Comments