Guji Yin Wadannan Abubuwan Idan Kina Ganin Wata:
#TsangayarMalam
SHARE 🔊
Mata da dama suke haddasawa kansu ciwo ko wari a lokutansu na al'ada ta hanyar aikata wasu abubuwan da basu dace ba a wannan lokacin.
Ka wasu jerin abubuwan da masana suka shawarci mata su kula dasu a lokutansu na al'ada. Musamman ga yan matan da yanzu suka soma al'ada.
#Shawara:
1: Kada ki yawaita cin duk wani abu mai yawan gishiri a cikinsa a cewar likitoci.
A fadarsu, gishiri zai jawo yawan zubar miki da jini, zai kuma rika haddasa miki ciwo na ciki ko na mara.
2: Duk wata macen da take ganin wata ta guji shan coffee da yawa. Nazari ya gano shan shi da yawa ga irin wadannan matan yana jawo ciwon mara da kuma sa nonuwan mace yayi tauri yana mata zafi idan an taba.
3: Yiwa gabanki turare a lokacin al'adar mace na iya jawo mata kwayukan cuta su shiga gabanta. Hakan nan kuma zai busar da ruwan gabanta dake Yi mata garkuwa wajen hana kwayar cuta shigan farjinta.
4: Kada ki dauki lokaci mai tsawo baki sauya audugar aladarki ba.
A kalla ana bukatar mace ta sauya kunzugunta kamar sau uku zuwa 5 a kullum bayan tayi wanka.
#alada
5: Kada kice zaki yi askin gabanki a lokacin da kike al'ada. Masana suka ce wajen nada matukar hadarin da za ayi sakaci ko wasa da shi domin muddin mace ta jiwa kanta ciwo ta baiwa kwayoyin cutuka shiganta nan take kenan.
6: Wasu matan sunfi sha'awar Jima'i a lokacin da suke al'ada. Baya ga haramcin saduwa da jinin al'ada, haka nan ma masana sunce akwai hadarin kamuwa da cuta ga matar da take Jima'i a lokacin ganin wankinta.
7: Bama sai kina al'ada ba, shan taba sigari abune mai matukar cutarwa. Yafi cutar da mace a lokacinda take al'ada don haka sai mace mai sha ta hakura a lokacin da take al'ada ko tama hakura da sha gaba daya domin lafiyanta.
8: Wasu matan idan suna ganin wata basa son kwanciya da kunzugu. Hakan ba daidai bane. Duk mace mai ganin wata ta tabbatar da cewa kamin ta kwanta bacci ta saka kunzugu domin hana kwayoyin cuta shiganta cikin sauki.
9: Ki daina cin abincin gwangwani ko irin nasu manyan gidajen abinci irinsu Mr Big saboda mafi yawan irin wadannan gidajen abincin suna saka gishiri da barkono da yawa a abincinsu wanda hakan zai jawo miki ciwo idan kina al'ada.
10: Yana da kyau ki rika kwanciyar bacci da wuri kina samun hutu sosai idan kina ganin wata.
Da fatan mata musamman sabbin soma al'ada zasu kiyaye wadannan abubuwan.
0 Comments