Alamomin Ciwon Sanyin Mara Na Maza:

Alamomin Ciwon Sanyin Mara Na Maza:


Sanyin Mara:

Ciwon sanyi wata cuta ce wadda tafi yaduwa ta hanyar jima’i saboda su kwayoyin halittun da suke sanya cutar ana yada sune daga wannan mutum zuwa wancan mutum, ta jini, maniyyi, ruwan farji ko ruwan jiki. Alamomin ciwon sanyi ga maza sun sha banban tsakanin mutane wadanda suka riga suka kamu da cutar.

Wannan kuma ya danganta ne da irin nau’in kwayar halittar cutar wacce ita ce take haddasa ciwon da kuma matakin da cutar ta takai a jikin mutum, wato wannan yana nufin, alamomi ko matakin farko da kamuwar cutar ko alamomi na gaba bayan ta dade da jimawa a jikin maras lafiyar.

Haka nan kuma, su ma yanayin alamomin sun sha banban ta fuskar tsanani ko kuma saukin su, koda kumada akwai rashin ganin alama ko daya duk da cewar, ko akwai cutar a jikin marar lafiyar. Maza da yawa na zargin suna da ciwon sanyi ne kawai a lokacin da suka ga wasu alamomi da basu saba da gani ba (baki) ga al’aurarsu, misali , kamar: feshin kananan kuraje ko kaikayi, ko fitar da farin ruwa, jin radadin zafi daga maraina da dai sauransu. A takaice dai, alamomin ciwon sanyin maza za su iya buya amma gwaji a asibiti zai iya nuna akwai cutar idan da akwai ta.

Ciwon sanyi an fi yada shi ne ta hanyar jima’i kuma maza na iya harbin mata da ciwon ko kuma su matan masu dauke da ciwon su sakawa maza mararsa ciwon. Ciwon yafi yaduwa kuma anfi samunsa ga maza masu neman mata ko mata masu bin mazaje. Haka kuma mutum zaya iya kamuwa da ciwon ta wasu hanyoyin na daban daba na jima’i ba.

Kuma lallai ciwon nada wuyar magani , musamman ma idan mutum bai samu magani ingantacce ba. Zai iya yin wuyar magancewa saboda rashin samun sahihin magani ko dadewarsa cikin jiki ba’a magance ba. Sau da yawa zaka ga cewa mutane su kan sha magunguna domin kaiwa ciwon hari da sukar alluran , amma hakan ba kasafai ya kan canza komai, ba sai kaga yana ma mutane jeka-ka-dawo tsawon watanni koma shekaru ba a samu waraka ba.

Alamomin ciwon sanyin maza wanda aka fi samu bainar mutane (game gari):

□ Kananan kuraje akan zakari, ko maraina ko kasansu.

□ Kaikayi akan zakari (kan hular).

□ Fitar da farin ruwa daga zakari, mai kalar madara ko dorawa, mai kauri ko wanda ya tsinke.

□ Jin zafi lokacin yin fitsari.

□ Jin zafi lokacin fitar maniyyi.

□ Kuraje masu durar ruwa da fashewa akan zakari.

Alamomi ciwon sanyin maza wanda ba duk wanda ya kamu da ciwon bane yake ganin su:


□ Rauni (gyambo) ga zakari ko maraina.

□ Zafi da kumburin maraina.

□ Zafi da kumburi daga kwararo da fitsari da maniyyi suke fitowa daga cikin zakari.
Zazzabi

1.Matsalolin jima’i da ciwon sanyi zai iya haddasa ma maza: Bincike ya nuna cewa cutar ciwon sanyi mai suna da turanci “Chlamydia” (kilamiidiya) zata iya sanya matsalar rashin karfin mazakuna idan ciwon yayi kamari ba’a magance shi ba.

 Cutar mabannaciya ce da take illa a boye kuma mafi yawanci bata nuna wata alama a zahiri ga mai dauke da cutar. Ana samunta bainar mutane da yawa. Rashin karfin mazakuta na nufin matsalar rashin cikakken karfin al’aurar namiji ko raguwar karfin al’aura yayinda aka fara saduwa ko kuma rashin mikewar al’aura lokacin da ake bukatar fara yin jima’i.

Bugu da kari, matsalar na iya zuwa da saurin kawowa/inzali. Rashin karfin maza zai iya saka magidanci cikin damuwa da tawayar jin dadin rayuwarsa ta jima’i, ko jin cewa bai cika mutum namiji ba, ko rashin haifuwa kasancewar ba zai iya yiwa iyalinsa ciki ba, saboda rashin mikewar al’aura. Zuwa asibiti da wuri ko cibiyar lafiya zai iya tsiratar da mai wannan matsala.

2 Rashin haihuwa:. Cutar sanyi mai suna “Gonorrhea” (Gonoriya) , kamar dai kwayar cutar “Chlamydia”, cuta ce daga halittar “bacteria” kuma zata iya labewa a cikin jiki ba tare da wasu alamomi ba. Duk da haka, tana zuwa da alamomi kamar fitar farin ruwa, mai kalar madara daga farkon cutar, daga nan sai ya koma dorawa, mai kauri da yawa, wani lokacin harda dan jini-jini.

 Yin fitsari da zafi da yawan yin fitsari, kaikayin dubura, zubar jini, murar makoshi/makogwaro, jan- ido ko kananan kuraje, ciwon gabobi da dai sauransu. Idan ba’a lura da cutar da wuri ba kuma aka magance ta, zata iya sa rashin haihuwa ga namiji ko mace.

Nau’in ciwon sanyi (ire-irensu) suna da yawa kuma ko wanne iri akwai kwayar halittar dake haddasa ciwon da alamomin sa da kuma matakan cutar a jikin ‘dan Adam. Sunayen cututtukan da turanci suna da yawa kamar yawan cututtukan. Cutar sida/Kanjamau (AIDS/HIB) tana daga cikin manyan su saboda ita ma anfi yaduwa ta jima’i, kuma sau day awa ita ce ke gayyatar sauran cututtuka a jikin ‘dan Adam.

Kankancewar Azzakari; Duk da dai cewa babu wani ingantaccen bayani a kimiyyance da yake nuna cewa ciwon sanyi yana sa azzakarin namiji baligi ya koma karami, akwai rahotanni da yawa daga mutane na korafin cewa sanyi ya sace masu girman zakari. Wannan zance haka yake a zahiri, masu ciwon sanyi sune suka fi lura da damuwa akan kankancewar alkalumman su.

Wasu daga cikin cututtukan sanyin da ake samu ta jima’i da kwayoyin halittu wadanda suke haddasa su (a yaren turanci):

a) Chancroid (bacteria) Cuta ce wacce ke zuwa da yanayin gyambo wani lokacin tare da kululu a hantsa.

b) Crabas (parasite), ‘yan kananan halittu sosai , yanayin kwalkwata, masu cizo da tsotsar jini mai sanya mugun kaikayi. Ana samunsu daga gashin mara inda suka maida gidansu, ana kuma iya daukarsu daga gashin gaban wani mutum zuwa na wani lokacin jima’i. Ana kuma iya samunsu ta kayan sawa, gado da sauransu.

c) Genital Herbs (birus) Cuta wacce take zuwa da kuraje masu durar ruwa a baki ko kan zakari, kurajen masu kama dana zazzabin dare (feber blisters). Idan kurajen suka fashe sai su zama gyambo. Haka kuma za’a iya samun kurajen a duwawu, cinyoyi, ko a dubura. Ciwon kai ko baya, ko mura (flu) mai dauke da zazzabi, ko kaluluwa da raunin jiki/kasala.

d) Syphilis (bacteria), anfi samunta wajen ‘yan luwadi. tana da matakai bayan shigar ta a jiki. Misali, matakin farko (1): fitowar wani irin gyambo (chancre), wannan gyambon shi ne wajen da cutar ta shiga jikin mutum. Gyambon mai tauri, mai zagaye marar zafi. Wani lokacin a bude yake kuma da lema, ko zurfi musamman a hular zakari, wanda zaka ga wurin ya lotsa.

 Ana samun sa a zakari ko dubura ko lebe (a baki). Ana kuma iya samun gyambon a boye wani wajen cikin jiki. Mataki na biyu (2): kuraje a tafin hannu ko karkashin tafin kafa ko wani sashen na jiki. ‘Yar mura, zubar gashi, zazzabi marar tsanani, kasala, murar makoshi, ciwon kai ko ciwon naman jiki da dai sauransu. Mataki na gaba:

 mataki na gaba ko karshe shi ne wanda cutar zata iya boyewa a jiki, ‘buya idan ba’a magance taba, kuma zata iya sanya kululun kansa/ciwon daji (tumour), makanta, mutuwar sashen jiki, matsalar kwa kwalwa, kurumta, ciwon mantuwa mai tsanani (dimentia). Ana iya magance cutar cikin sauki da idan an lura da ita, da wuri, cikin ikon Allah.

e) Da sauransu, suna da yawa kuma alamomin wani ciwon yana yin kama da na wani ciwon wani lokacin. Don haka yin bincike a asibiti shi ne zai nuna nau’in ciwon.

Ciwon sanyi yana da hadari sosai. Ya zama dole ga mutane su tsaya ga matan su na Sunnah idan har suna son lafiyarsu.

 Ciwon sanyi yana nan akan hanyar mai neman mata da zinace-zinace, zai same su. Akwai cututtuka masu hadari sosai kamar AIDS/HIB, wadanda za su iya wargaza iyali. Don haka mai son zaman lafiyarsa da rayuwa mai kyau sai ya ji tsoron Allah.

Post a Comment

0 Comments