Abincin Ci Da Sha Ga Macen Da Take Neman Haihuwa Da Wuri:


Abincin Ci Da Sha Ga Macen Da Take Neman Haihuwa Da Wuri:

SHARE 🌾
#Cikidahaihuwa

A ci gaba na darasin mu na ciki da haihuwa. Zamu ci gaba ne da irin abincin ko abun sha da magidanta musamman mata zasu maida hankali akansu domin samun ciki da wuri.

Cikin wadannan abincin da zamu kawosu dayawa daga cikinsu basu da tsadar da magidanta zasu ce bazasu iya saye ba.
Irin wadannan abinci dana sha sun hada da:


🍏🍍🍋🍏🍍🍏🍍🍏🍍🍏🍍🍏🍍🍏
1: Kayan Marmari:

Ana son mace mai burin samun ciki ta yawaita cin kayan lambu.
Hakan yasa masana sukace yana da kyau duk lokacinda mace mai burin samun ciki take cin abinci, ta maida kayan marmari ruwan shanta irin wadanda za a iya markadasu.

Inji masana, cinsu na karawa mace yin kwan haihuwa da wuri yadda zata iya samun ciki. 

Kankana da sauran na'in duk kayan lambu suna samar da wani sinadarin samar kwan mace mai lafiya. Glutathione, shine sinadarin da cin kayan marmari ke samarwa. Samar da shi kuma hanyace na samun ciki da sauri.

2: Fats: Abincin dake samar da sinadarin fat jikin mutum shima yana kara baiwa mace damar yin ciki da wuri.

Abinci irinsu Fiya, da man zaitun suma suna daidaitawa mace lafiyar jikinta tare kuma samar mata kwan haihuwa da wuri. 
Muddin mace zata maida hankali wajen cin abu mai maiko wanda ba a masa gauraye ba kamar man zaitun da muka ambata, zai taimaka mata sosai wajen yin ciki da wuri.

3: Bitamen B Da E: Duk wani abincin dake dauke da wadannan sinadaren mace mai son haihuwa ta kasance tana cinsu.
Mangoro, kwakwa, ganye da kuma cin duk wani abincin da aka yishi da hatsi irinsu gero, dawa das suna karawa mace lafiyan Kwan halittan ta a binciken da muka gano.

4: Proteins: Duk wani abincin dake jawowa mutum kuzari a jiki yana da kyau mata masu neman juna biyu su yawaita amfani dasu. Sai dai masana sunce banda jan nama, ma'ana naman shanu.

Kifi, Tolotolo, kaji, duk abinci ne dake samar da sinadarin zinc da iron sukan sa mace tayi ciki da wuri, kuma suna karawa jaririn lafiya idan cikin ya shiga.

Haka nan ma masana sukace cin kifin gidan sanyi irinsu salmon, sadin suna samar da sinadarin DHA da kuma Omega 3 wajen sa mutum ya samu karfi a jiki, ya kuma karawa jaririn lafiya tare da magancewa mace hadarin yin barin ciki idan ya shiga.

Sai dai masanan sun gargadi mata wajen cin Irin Wadannan cimakan, su kuma kiyaye nauyinsu saboda gudun yin jiki.

5: Madara Da Zuma: suma dai masana sun baiwa ma'aurata masu neman haihuwa shansu domin dacewa da samun juna biyu cikin lokaci.

Sai dai kuma akwai gargadin kada mace ta yawaita shan madara ko nonon shanu da aka gurbata su. Sai suka bada shawaran yana da kyau ma'auratan su hada madaran da kansu idan sunsan inda zasu samu danyen madara.

Ga masu sha a cikin shayi kuma, su tabbatar da duk wani kofin shayin da zasu sha madara yaji sosai.


Wadannan sune wasu ci makan da mace zata maida hankali wajen amfani dasu a burinta na neman haihuwa.

A darasi na gaba idan Allah Ya nuna mana, zamu ci gaba ne akan yanayin kwanciyar Jima'i da za ayi domin samun ciki ya shiga cikin sauki. 

Masu neman haihuwa, Allah Ya basu masu albarka. Mu da muke dasu Allah Ya shiryemu dasu gaba daya.

Post a Comment

0 Comments