Wasu Hanyoyi Guda 4 Da Zaki Iya Farantawa Mijinki Rai Dasu:


Wasu Hanyoyi Guda 4 Da Zaki Iya Farantawa Mijinki Rai Dasu:

#TsangayarMalam 
Burin duk wata mace taga tana farantawa mijin ta rai a koda yaushe.

Wasu matan suna burin yin hakan sai da matsalar basu san yadda ko abunda zasu yi su saka mazansu cikin farin ciki ba.

Ga wasu hanyoyi masu saukin gaske da duk wata mace zata iya sa mijin farin ciki da ita.

 
1: Godiya: Babu wani Dan Adam da baya son a masa godiya a duk wani lokacin da yayi abun a gode masa.

Yawan yin godiya abune da Allah (SWT) da kanSa yake son gani mutum yayi masa. Da wannan ne shima Dan Adam yakan ji dadi a duk lokacin da yayi abun godiya aka gode masa 
Wasu matan basu iya nunawa mazansu farin cikin abunda aka musu na alheri ba bare ma suyi godiya.

Mata musamman wadanda suke da raina kyauta, ko wadanda suke burin suga an musu kyauta da abu mai tsada, muddin akasin hakan aka yi basu taba yiwa mazansu godiya ba.

Duk macen da take yiwa mijin ta godiya a duk kankantar abunda zai bata, tana sashi farin ciki ne tare kuma da karfafa masa gwaiwa na yi matan abunda yafi wannan.

 Don haka duk matar da take da burin ganin ta saka mijinta cikin farin ciki, to ta kasance mai yi masa godiya ako yaushe.

2: Amince Masa: Akwai wani kuskure da mutane suke yi na nunawa mutum rashin aminta.

A duk lokacin da ka nunawa mutum baka amince da shi ba tamkar kana bashi damar yin abunda kake gudun yayin ne.

Nunawa miji yarda da kuma amince masa yakansa namiji yaji kunyar aikata wani abunda zai ji matukar kunya da damuwa da ace matarsa ko matansa zasu ji.

Amma idan kika nuna masa baki yarda da shi ba bazai taba damuwa ba don yayi abunda zakiji saboda daman kina masa kallon zai iya ko yanayi.

Don haka ne mata masu dabara suke nunawa mazansu matukar yarda da amince musu ba tare da zargensu akan komai ba har sai abunda ya bayyana ya bayyana kamin suke sauya tunani. Amma baza zargin mazansu a bisa zato.

Mata masu wannan dabi'ar suna saka mazansu cikin farin ciki a koyauahe kuma suna taka musu burkin aikata ba dai-dai cikin hikima.

3: Ladabi Da Biyayya: Duk inda aka samu zaman aure na gari tabbas akwai ladabi da biyayya da matar take yiwa mijinta wanda ya jawo hakan.

Ladabi shine mace ta girmama mijinta a inda ya dace a kuma lokacinda ya dace ko a gaban mutane ko kuma suna su biyu.

Shi kuma biyayya shine kiyaye dokokin ko ka'idojin daya shinfida mata domin samar da zaman lafiyar zamantakewar aurensu.

Wasu matan suna ganin cewa ta hanyar tsageranci da rashin kunya ne zasu iya samun hankalin mazajensu. Shi namiji ba a masa gadara ko ka'ida a gidansa. Amma ta hanyar ladabi da biyayya idan ma akwai wasu abubuwan da yake yi marasa kyau zai gyara. Hakan Kuma yana sa duk wani magidanci farin ciki yaga iyalinsa na girmama shi a matsayinsa na shugaban gidansa.

 
4: Rashin Shiga Harkarsa: Matan da basu shiga harkokin mazansu da ba a gayyacesu ba sunfi mutuncin a idanuwan mazan fiye da matan da komai mijinsu yake yi sai suce dole sai sun sani.

Shi namiji a matsayinsa na shugaba yana so yaga yana da 'yancin yin abunda yake da ra'ayin yi. Daga lokacinda kike neman shiga harkar mijinki ba tare da ya shigo dake ba. Ko neman yi masa iyaka da abokansa ko 'yan uwansa ko bashi ka'idar da zai rika dawowa gida. Daga wannan lokacin kin jawa kanki da kanki matsala.

Mazan da matansu basu sa musu ido maza ne da suke cikin farin ciki da walwala a gidajensu sabanin mazan da matansu ke akasin hakan.

5: Mai Alkitawa: Maza suna son ganin sun samu dacen auren mace mai sanin duk wani darajar abunda aka kawo mata a gida. Mace wacce zata yi amfani da kayan gida dai-dai da bukata ba tare da tayi almubazaranci ba.

Wadannan matan sukan saka farin ciki a zukatan mazajensu da kuma sanya alnuri a fuskokinsu. Muddin kina son ganin mijinki cikin farin ciki. Ki zama mace mai alkitan kayan gida da aka kawo domin bukatar ku.
 
Wadannan wasu ne daga cikin abubuwan da mata zasu suyi muddin suna son ganin mazajensu cikin farin ciki.

Post a Comment

0 Comments