#Nazari
Duk irin saukin dana miji ya samu wajen jawo hankalin macen da yake soyayya da ita koma aurenta, da akwai wani abu guda da zai tsaya mata a rai da take tunanin namiji zai iya mata su duk yadda take da shi.
Hakan yake sa wasu matan suke daukan lokaci kamin su baiwa namiji soyayyar su da yardarsu.
Ga wasu abubuwan da duk yadda zaka yi sai ka samu mace tana kokwantoka saboda abu guda daga cikin wadannan abubuwan:
#tsagayarmalamtonga
1; Duk wata macen da namiji ya soma nemanta abu na farko da zai fara zuwa mata a rai, da aure kake sonta ko da lalata.
Wannan kokwanto baka rasa mata dashi a zuciyarsu koda kuwa gemunka na malunta na jan kasa.
2: Mata suna tunanin duk lokacinda suka baiwa namiji kansu yayi lalata dasu, to daga wannan lokacin zai rabuda ita.
Wannan tunanin na mata yasa suke da shakku akan maza da har basu sakin jiki dasu musamman mazan da suke nuna kwadayinsu na son yin zina da 'yan matan da suke soyayya dasu.
3: Mata sunada kokwanto hade da shakku cewa duk irin son dana miji zai nuna mata yana da wata a gefe da yake so.
Yana da wahakar gaske ka cirewa mata tunanin baka kula kowa da ita.
4: Duk irin kalaman soyayyar da zaka furtawa mace, bazaka cire mata shakkun kana amfani da irin wadannan kalaman wajen wata macen ba.
Mata na yiwa maza kallon abunda aka furta mata na soyayya ana can ana zuga wata ma da irin kalmomin.
5: Mata suna da shakku cewa namiji zai iya sauyawa bayan ya aureta.
Duk irin soyayyar da zaka nunawa mace kamin aure, a zuciyarta tanada shakkun zaka ci gaba da nuna mata irin wannan soyayar bayan aurenku.
6: Mata suna da shakkun namiji zai iya ci gaba dasu idan ya tabbata basa haihuwa.
Hakan yasa mata kamin suyi auren farko suke zullumin yadda zata kasance bayan auren ya zamanto bata haihuwa.
7: Mata suna da shakku cewa da zaran namiji ya gano wani mugun abu da wacce yake so ta taba yi zai rabu da ita.
Wannan yasa wasu matan suke boye wani abunda suka san sun yi a baya. Masu wayon cikinsu kuma tun a farkon haduwa suke labartawa mai sonsu rayuwar su na baya.
8: Mata suna da shakku duk hakurin talaucin da sukayi da namiji idan ya samu budi zai kuntata musu.
Bazaka cire wannan shakkun na mata ba, da suke ganin zaman lafiyar su da mazan da suke soyaya ko aure rashin wadata. A mahangarsu muddin namiji ya samu budi, sai wulakanci ya biyo bayan hakan.
9: Mata basa cire shakkun namiji ba zai karo wata mata ba sai har sun tabbatar da cewa baida lafiyan da zai iya karo aure.
Wannan yasa duk wata macen da bata da Kishiya, bata da kwanciyar hankalin baza a mata ba muddin namiji yana da hali da lafiyan kara wata matar.
10: Mafiya yawan mata sun tafi akan cewa maza basu da tabbas.
Mata na ganin namiji yana iya yin abunda mace bata zato a ko yaushe. Wannan yasa akasarin mata sunka dauki maza a marasa alkibla.
#Nazari
Ko kai wanenen wajen iya magana da misali baka iya cirewa mata shakkun wadannan abubuwan game da maza.
Duk kuwa da ana samun maza masu irin wadannan halayen da mata suke gudu. Kada ku manta mata, da akwai maza birjib da basu hada hanya ba da wannan kokwanton naku.
A kullum shawaran mu gareku shine ku saka Allah akan dukkanin lamarin ku kamin aure da bayan aure. Bazaku yi danasani ba.
0 Comments