Wasu Halayen Maza Da Matan Suka Tsana A Zamantakewar Aure:
SHARE 🔔
#tsagayarmalamtonga
Akwai wasu halayen da maza suke maidasu tamkar dabi'a ko dole duk namiji sai yayi hakan ne kamin ake ganinsa a namiji.
Irin wadannan halayen suna matukar kuntatawa mata. Wasu matan haka suke hakura idan sukayi magana suka gaji. Wasu kuwa basa iya hakura kullum matsala suke samu da mazajensu masu irin wadannan halayen.
Ga wasu halayen da duk wata macen datake son mijinta ta tsani mijinta ya matasu.
Hiran Dare
Wasu mazan sun maida fita hiran dare tamkar wani ibada ne da dole sai sunje.
A daidai lokacinda mace take son zama tayi hira da mijinta shi kuma a wannan lokacin zai fice abunsa sai lokacinda matarsa ta soma bacci zai shigo.
Abun haushi irin wadannan mazan wasu tafiya suke wajen wasu matan acan zasu raba dare kamin su dawo gida.
A gaskiya ya kamata maza su fahimci cewa duk wata mace ta tsani wannan bakar dabi'ar na hiran daren
Rashin Bada Hakuri:
Wasu mazan suna da girman kan da zasu yiwa matansu laifi amma suke jiran matan nasu su basu hakuri. Wannan zalunci ne ba Zamantakewar aure bane.
A zaman aure duk wanda yayiwa guda laifi ya ajiye girman kai ya bada hakuri.
Akasarin maza masu irin wannan bakar dabi'ar basa girman kai a lokacinda suke bukatar mace, amma wajen bata hakuri anan ne suke ganin sun isa. Amma da watace ta waje zata bata masa rai shi zai bata hakuri bayan itace ta bata masa rai.
Tabbas wannan dabi'ar mata sun tsaineshi. Kayi mata laifi kuma kaki bata hakuri sannan kana jira ita ce zata baka hakuri.
Rashin Cin Abinci A Gida;
Duk wata mace ta tsani ta bata lokaci tayi girki amma mijinta ya dawo yace mata akoshe yake.
Wadansu mazan haka nan kawai sunsan gidansu zasu dawo amma sai suje gidan abokai ko 'yan uwa wasu ma gidajen 'yan matansu suke zuwa su take cikinsu da abinci su barwa matansu wahakar girki data shafa awanni tana yiwa miji yazo yaci.
Muddin ba wani horo bane da ya kamata ayiwa mace hakan. Wannan ba daidai bane ana zaune kalau.
Kin Yaba Kwalliyar Ta:
Akwai mazan da duk irin kwalliyar da matansu zasu yi bama zasu daga idanuwa su kalla ba bare ma suce mata tayi kyau.
Wannan kalmar na "Kinyi kyau" babu wata kalmar da mace take son jin sa da ya wuce shi.
Amma idan da wata can zata yi ba matarsa ba za aga yanata yaga baki yana ta zugata tayi kyau koda kuwa ba hakan bace.
Maza masu irin wannan halin ya kin yaba kwalliyar matansu hakan ba daidai bane su gyara.
Kin Daukar Wayarta:
Haka nan kawai mace tayi ta kiran mijinta yana ganin kiran yayi banza da ita. Amma yana ganin kiran wata wanda bai aura sai yayi wuf ya dauka.
Amma da shine matarsa zata ki daukar wayarsa a wannan ranar sai an shiga tsakaninsu idan auren yana da sauran rai.
Ya kamata ka sani yadda kake da hakki a wajen matarka ita ma haka take dashi. Yadda idan taki daukan wayarka abun zai maka zafi ita ma hakan. Don haka a mutunta juna zaman aure ake yi ba akasin hakan ba.
Sai dai kuma da akwai wasu dabi'un da wasu matan suke bijirowa dasu da ake samun wasu mazan suna musu hakan.
A darasi na gama zamu kawo irin dabi'u da mata suke yi da suke jawo samakon hakan daga mazajensu.
Mazan da sukasan babu wani matsala tsakaninsu da matansu su dubi Allah su gyara.
0 Comments