AMFANIN ALMISKI DA SABULUN ALMISKI:


AMFANIN ALMISKI DA SABULUN ALMISKI


SHARE 🤶

_Turaren almiski turare ne mai ɗimbin tarihi da asali.Ya kasance turare mafi shahara a duniya da ya yiwa dukkanin sauran turaruka fintinkau kama daga fannin ƙamshi, yin suna, da kuma amfani._

_Yana da matuƙar amfani musamman ga mata domin yana sanya nishaɗi da annashuwa, haka kuma yana janyo hankalin magidanci zuwa ga uwargida,_

_A ƙasashen Larabawa amfani da almiski ya zamo al'ada a garesu domin duk wata matar da zata yi aure ko wacce tayi aure zaka tarar tana mai amfani da almiski (Musk ɗahara) wannan baya rasa nasaba da sanin muhimmancinsa,_

_Shi Miski ba tsiro ba ne, ana samar da shi ne daga jikin Barewa, kuma Allah ya faɗe shi a Alqur‘ani._

_Shi dai miski turarene me ƙamshi ƙamshin kuma mai sa nishaɗi da annashuwa._

_Yana da kyau ƙwarai da gaske ace amatsayinki na mace koda yaushe yakasance kina da miski a ɗakinki domin anaso koyaushe kirinƙa amfani dashi._

_Mun riga munsani shi ƙamshi abune dayake ƙara danƙon soyayya kuma yake dawwamar da ita, sannan miski yana ɗauke da sinadarai da dama dasuke bawa farjin mace kariya daga cututtuka, saboda haka anaso kullum mace tarinƙa amfani dashi._

_*Amfanin sa.

1️⃣ Yana maganin dafi kowanne iri.

2️⃣ Yana ƙara ƙarfin jiki.

3️⃣ Yana maganin hawan jini idan an shaƙa.
 
 4️⃣Yana maganin Aljanu, ya kan ma iya kashe Aljani idan ana haɗa shi da Za‘afaran da man zaitun ana shafawa, ana kuma iya zuba shi a garwashi a dinga hayaƙi.

5️⃣Yana maganin warin gaba idan ana shafawa. 

6️⃣Yana maganin namijin dare. 

7️⃣Yana taimakawa masu matsalar haihuwa idan suna matsi da shi bayan gama al'ada. 

7️⃣Yana tsftace gaban mace,

8️⃣Yana ƙara danƙon soyayya tsakanin ma'aurata.

9️⃣Yana maganin ƙaiƙayin gaba da kashe ƙwayoyin cututtuka.

  ️ *_Kalolinshi guda huɗu ne._*

_Shi Turaren almiski launinsa ya kasu a gida huɗu akwai fari mai kamar madara mai kauri (white musk) baya saurin narkewa kuma kuskure ne mace ta sanya shi a gabanta._
 _Idan ko aka saka shi to bazai narke ba kuma wasu illolin zasu iya faruwa, sai dai a shafa shi, a saman farji da matse matsi_
_shi wannan ba'a sashi a cikin farji saboda a daskare yake bai fiya narkewa ba, sai dai ashafashi daga wajen farji, ko ƙasan hammata._

_Akwai fari ƙal kamar ruwa ƙamshinsa kusan ɗayane da mai kaurin shima yana da kauri amma yafi wancan danƙo sosai, to shi za'a iya "inserting"(matsi) dashi tabbas yana taimakawa har aɓangaren auratayya kuma duk sanda mijinki yaji wannan ƙamshin ko bakwa tare to zai tunaki Zaiyi sauri_sauri ya dawo,_

_wannan zai baki wani sirri na musamman domin a duk inda mijinki yake da zaran yaji ƙamshin wannan turaren koda a kasuwane ko a cikin jama'a ne to zai tuna dake kuma zai ji sha'awarki, kinga kenan zaiyi zumuɗin ya dawo dan saduwa dake._
_a nan miski yayi amfani kenan._

_domin miskin yana matuƙar Motsa sha'awa ga ma'aurata, yana kawar da duk warin da zai iya fitowa daga gabanki.%

_Akwai jan miski wannan masu fama da matsalar aljanu suke shafashi domin yana fatattakar aljanu da iznin ALLAH_

_sai dai shi wannan jan miski ana son idan me aljanu yanson ya shafashi to ana buƙatar a ringa yin ruƙiyya. domin idan ba ayi Ruƙiyyah ba mutum ya shafa shi alhalin yana da matsalar jinnu to zakaga mutum ya ƙyamaci ƙamshinsa gaba ɗaya._

_Ana haɗashi da man zaitun sai a karanta ayoyin Ruƙuya a ciki, Yana shaƙe aljani ya hanashi sakat, yana kawar ɓacin rai, ciwon kai, faɗuwar gaba, riƙewar ƙirji ko ƙafa, yawan mafarkai, da dai sauransu. mutum yana iya rabuwa da shi inshaAllah._

_Shi ana shafashi ne a duk jiki sau biyu safe da yamma._

_Akwai kuma bakin almiski wanda shi kalarsa baƙi ne kuma ƙamshin sa yana da matuƙar daɗi domin yana ƙashi ririn ƙamshin da ake ji a jikin ɗakin KA'ABA ne, ga duk wanda ya taba zuwa aikin hajji ko umrah to da zarar yaji ƙamshin baƙin almiski zai tuna da ɗakin KA'ABA mai tsarki._
_Kuma shine turaren da mala'ikun Allah suka fi jin daɗin ƙamshin sa._

_Shi ana shafawa ne a duk jiki da kuma kayan sawa musamman a ranar juma'a._

_Sai kuma sabulun Miski shi ana wanke farji dashi ne a duk lokacin da zakiyi wanka ko bayan kin gama jinin haila,_

_Ba'a son mace ta ringa amfani da sabulu kai tsaye a gabanta domin kuwa yana da sinadarean da suke cutar da mace kuma yana ɗauke mata sha'awa._

_wannan sabulun shi yakamata mace ta ringa amfani dashi wajen wanke gabanta._

_Yana da kyau mace ta haɗa waɗannan collection ɗin na Almiski wato turarensa da man shafawa, da kuma sabulunsa zaki fita daban a cikin mata._

_To anan idan za ayi amfani da Almiski to sai ayi amfani da Musk ɗahara) a nemi wanda aka kawo daga Macca ko Pakistan ko India._

_Akwai sunaye daban daban da ake yiwa musk ɗahara kamar musk Aljism. Haka kuma akwai musk Aishat wanda aka ruwaito Aishat(R.A) tayi amfani da shi kuma ta kwaɗaitar da amfani da shi._
_Musk ɗahara ko musk Aishat Shi yafi dacewa mata suyi amfani dashi dan ƙarin tagomashin zamantakewa da kuma tsabatace jiki._

_Idan aka tafasa lalle aka ɗan ɗiga miski sai ayi sith bath da shi hakan zai magance warin gaban mace,_ _ƙaiƙayin gaban mace, yana kashe ƙwayoyin cuta a gaban mace._
_yana rage yawan majinar gaba a sanadin wata cuta._
_Yana tsabtace mahaifa musamman idan aka dage amfani da shi._

_Idan kuma mace ta haihu to zata iya neman ganyen magarya sai ta tafasa ta ɗiga miski ta ringa amfani da shi._

_Turaren almiski ana maganin farfaɗiya da shi._

_Yana maganin cutukkan ƙwaƙwalwa(brain diasoders)yana maganin bibiyar aljannu._

_Yana sanya mai gida sha'awar matarsa._
_Yana maganin warin ƙashi ga maza da kuma mata._

_Yana hanawa aljannu bibiyar mace musamman waɗanda ke saduwa da mace,_

_Kunsan fa miski asali ya samo yana da kyau ayi taka tsantsan gurin amfani dashi domin bawai kawai dangwalawa mace zata yi da yatsantan ba, a'a,_

_Zaki nemi ruwanr ɗumine bamai zafi sosai ba kije ki kama ruwa dashi ki wanke gurin sosai, sannan ki sami hand kechief me kyau ki goge ko da tissue, daganan sai ki sami *"cotton bud"* wato abin sosa kunne,_

_Sai ki dangwalo dashi sannan ki turashi agabanki ki ɗan matse ƙafarki sai ki cire ki jefar._

_to wallahi ko fant ɗinki kika cire ƙamshi zakiji bazaiyi wari ba._

_Babu kunya cikin neman ilmi musamman ilmin addini babban abun kunya ace mijinki zai kusanceki kuma yaji farjinki yana wari._

_Zaki iya dafa ganyen magarya inya huce ki zuba miskin kina kama ruwa dashi._

_Sannan anaso duk sanda zaki saka pant ɗinki to ki shafa miskin akai duk wasu ƙwayoyin cuta zasu mutu da yardar Allah._

_Ana kuma shafa miski ajiki ana kuma haɗashi a cikin Humra yana kuma taimakawa macen data haihu ƙwarai da gaske._

_Kamar yadda muka faɗa a baya Akwai jan Miski akwai baƙi, akwai fari mai kamar koko da kuma farin Almiski garai gari mai kamar ruwa akwai kuma miski na ruwa. sannan sai sabulu, da kuma cream._

_sai dai kuma duka waɗannan kayayyakin ana samun jabun su sune ma suka fi yawa a kasuwa, don haka a kula sosai kada garin neman araha a yi amfani da abin da zai cutar da mutum._

_Yana da kyau ace amatsayinki na mace kar arasaki da waɗannan abubuwan

~MISKI
~GANYEN MGARYA
~HULBA
~HABBATUSSAUDA
~MAN ZAITUN
~MAN TAFARNUWA
~KHALTUFA 
~LALLE
~ZUMA
~SABULUN MISKI

Post a Comment

0 Comments