Wasu Abubuwa Guda 10 Da Suka Fi Soyayya Mahimmanci A Zamantakewar Aure:
SHARE 🔔
#TsangayarMalam
Akwai masu ganin cewa da zaran mutane suna son junansu, to da za a zauna lafiya idan sukayi aure, wanda a zahirance ba haka abun yake ba.
Masoyan da suka tsananta son junansu ma basu cika dadewa ba idan sunyi aure saboda shi soyayyar kadai suka saka a gaba ba tare da fahimtar akwai abubuwan da suka fi soyayya mahimmanci ba a zaman aure.
Ga wasu abubuwa nan guda 10 idan ma'aurata harma da masoya zasu shigo dasu cikin soyayyar su, zasu zauna Lafiya da juna.
1:Yadda:
Duk ma'auratan da basu amincewa junansu ba duk yadda suke son junansu bazasu zauna lafiya da juna ba.
Yadda da amincewa juna yafi soyayya juna tasiri a rayuwar aure.
2: Tausayawa Juna:
Duk soyayyar da babu tausayawa juna shirme ne.
Idan ma'aurata suna burin zaman aure na har abada dole ne su rika tausaya junansu a duk lokacin da guda yake cikin abun a tausaya masa ko mata.
3; Hakuri Da Juna:
Hakuri da juna shine kan gaba wajen inganta zaman aure. Duk irin soyayyar da ma'aurata zasu yiwa junansu muddin bazasu iya hakuri da juna ba to babu inda aurensu zai je.
4; Yiwa Juna Uzuri:
Dole ne ma'aurata su rika yiwa junansu uzuri idan suna burin samun zaman lafiyan aurensu.
Tsananin soyayya babu uzuri ba zai samar da zaman aure mai dorewa ba.
5:Kyankyawan Zato:
Dole ne ma'aurata su cire dun wani zargi a junansu idan suna son zaman aurensu yayi inganci. Duk wani soyayyar da za a surka shi da zargi babu inda zashi.
6: Ganin Mutuncin Juna:
Duk auren da kowa zai mutunta juna suna su biyu ko a gaban mutane wannan auren sai mutuwa zai raba shi.
7: Kula Da Hakkin Juna:
Soyayya tsagoro amma ba a damu da hakkin juna ba bazai aamar da zaman aure na gari ba.
Dole ne kowa yasan hakkinsa, ya kuma Kiyaye hakkin nasa muddin ana burin samun zaman aure mai kyau.
8: Baiwa Juna Hakuri:
Ya zama dole ga ma'auratan da suke son zaman lafiya a aurensu su baiwa junansu hakuri a lokacinda guda yayiwa daya laifi.
9: Yafiya:
Kada wani ya kullaci wani muddin ma'aurata suna fatan zaman lafiya a aurensu.
10: Kiyaye Abunda Guda Baya So:
Yanada kyau ma'aurata su fahimci abunda guda yake so ko take so da abunda yake bata masa rai ko mata rai.
Muddin ma'aurata zasu kiyaye wadannan abubuwan, babu tantama zasu ci ribar zaman aurensu. Amma duk masu tunanin tsabar son juna ne zai sa su samun zaman aure na gari yaudaran kaine kawai.
0 Comments