Dalilin da yasa baka jin dadin jima'i,mace ko namiji:
SHARE 🔔
Matsalar Rashin jin dadi lokacin jimai,ko rashin gamsarwa
Rashin jin dadin jima'i ko rashin gamsar wa yayin saduwa ko rashin jin sha'awa yayi saduwa wanda ake kira da sexual disorder,matsala ce wacce take kasancewa mutum baya jin dadin jima'i,ko baya iya gamsuwa koda kuwa ba mace daya ko namiji daya aka tana saduwa dashi ba.
Hakan kuma yana iya samun mace ko namiji.
Kadan daga abubuwan da suke jawo wannan matsala akwai.
1. Tilastawa yayin jima'i,mutum baya ra'ayin yayi jimai a matsa masa Dole sai yayi.
2. Matsalolin kwakwalwa,kamar gajiya,damuwa,bacin rai da sauran su.
3. Matsalar ciwon suga.
4. Matsalolin ciwon zuciya.
5. Shaye shayen kwayoyi
6. Yawan shan giya.
Abubuwan da suke bayyana kana da matsalar sexual disorder (rashin gamsarwa ko jin dadin jimai):
1. Karancin shaawa ko rashin Shaawa baki daya.
2. Rashin motsawar Sha'awa,saka ji kana son jima'i a zuciyar ka amma kuma zaka ji a jikin ka babu wannan yanayin.
3. Rashin yin inzali lokacin saduwa,shine koda awa nawa zaai ana jima'i,baza a kawo ba ko a gamsu.
4. Jin zafi lokacin jima'i.
Rashin sha'awa ga namiji yana iya sakuwa Sanadiyyar karancin hormones wanda ake kira da testosterone wanan hormones shine yake bayar da shaawa da kuzari hatta bangaren samar da ruwan maniy.
Ta bangaren mace kuma takan samu wannan matsala idan tana da hormonal inblance ko tana lokacin shayawarwa,ko Luka in da mace ta dena ovulation da dena ganin al'adar ta.
Bayan wannan matsaloli kamar su:
1⃣ Hawan jini
2⃣ Ciwon zuciya
3⃣ Kwayoyi
4⃣ Yawan gajiya
5⃣ Damuwa
6⃣ Matsalar a zamantakewar aure
Suna iya jawo wannan matsala da rashi ko daukewar shaawa baki daya.
Saboda haka domin magance wannan matsala dole ne mutum ya ziyarci likita ta yadda za'a gane ainihin abunda yake damun sa sannan a bada magani ko shawarwari.
Allah yasa ku dace
SHARE ⏰
0 Comments