AMFANIN ZA'AFARAN DA AMBAR DA KUMA ALMISKI WAJEN KYAUTATA LAFIYA.
1) ZA'AFRAN.
Shi Za'afaran wata ciyawa ce ko kuma tsiro mai ɗauke da launi mai abin sha'awa, galibi jar ciyawa ce ko yaluwa. Da akwai man Za'afran, da akwai turarensa kuma ana samun ciyawar tasa ma.
Ana amfani da shi wajen sinadarin girki kuma yana maganin cututtuka da dama yana kuma kyautata lafiya.
An fara noman Za'afaran ne a wajejen Greece. Sannan a kayi Safararsa zuwa Yammacin Amurka da kuma ƙasashenmu na Afrika.
Za'afaran yana maganin cututtuka kamar:
★Zubewar Gashi.
Shafa Man Za'afaran a fatar kai yana maganin sanƙo. Haɗa Za'afaran da madara a shafa a kai yana maganin zubewar gashi kuma yana ƙara yawan gashi.
★ Gyaran Fuska
Haɗa Za'afaran da madara a shafa a fuska a hankali amma a kaucewa ido. A bar shi tsawon minti goma sha biyar sannan a wanke da ruwa yana sa fuska tayi kyau da sheƙi. Ana yin wannan haɗin sau ɗaya a sati.
★ Matsalolin fata.
A jiƙa ciyawar Za'afaran a ruwa tsawon awa biyu zuwa uku. Sai a shafe fatar jiki da shi. Yana bada fata mai laushi da taushi. Ana yin haka sau biyu zuwa uku a sati.
★ Maganin ƙuraje.
A haɗa Za'afaran da Ray'han a kirɓa a shafa a kan fata sai a wanke bayan minti goma. Wannan haɗin yana maganin ƙuraje, ƙyasbi, makero da tabo da kuma sauran cututtukan fata.
★Ƙwayoyin Cuta.
Zuba ko fesa Za'afaran a waje yana maganin ƙwayoyin cututtuka da ba'a iya ganinsu kuma yana kyautata lafiya.
★Kyautata Bugun Zuciya.
Za'afaran yana da sinadarin potassium wanda ke kyautata bugawar zuciya da kuma bata damar yin aikinta yadda ya kamata.
★Zagayawar jini.
Za'afaran yana da sinadarai irinsu coper, potassaium, calcium, manganese, iron, magnesium, da zinc da kuma selenium. Wasu daga cikin waɗannan sinadarai suna taimakawa wajen daidaita yanayin jini a jikin mutum.
★Rigakafin Cutar Kansa (cancer).
Za'afaran yana ɗauke da wasu ƙananan sinadarai kamar zea-xanthin da lycopene waɗanda ke kare jikin mutum daga kamuwa da cutar Kansa wato Daji.
★Sauƙaƙa Narkewar Abinci.
Za'afaran yana da muhimmanci wajen sauƙaƙe narkewar abinci a jikin mutum saboda sinadarin anti-cinvulsant da sauran sinadarai dake cikinsa.
★Ciwon Haƙori.
Shafa Za'afaran haɗe da Zuma yana taimakawa wajen maganin cututtukan dasashi da haƙori.
★Cututtukan Cikin Baki.
Idan aka haɗa Za'afaran da Zuma da Graceline ana shafawa a cikin baki yana maganin ƙuraje da sauran cututtukan da kan iya samuwa a cikin baki.
★Gyaran leɓe.
Za'afaran yana cikin tsirrai kadan waɗanda ke samar da sinadarin vitamin B2 mai yawa. Amfani da shi yana gyara laɓɓa da kuma kyautata haɗiyar abinci daga baki zuwa maƙogwaro.
★Maganin Sanyi da Tari.
Idan aka haɗa Za'afaran 1grm da ruwa 1 Litter aka sha yana maganin Sanyi da kuma Tari.
★Jini lokacin Al'ada.
Za'afaran yana da kyau wajen daidaita zuwan jini yayin al'ada.
★Maganin Maza.
Amfani da Za'afaran yana taimakawa mazaje su dawo da ƙarfinsu. Hatta tsofaffi yana ba su kuzari sosai.
★Maganin Aljanu da Sihiri.
Haɗa Za'afran da Jan Almiski da Ambar, a dinga shafawa a fata, yana maganin cututtukan Aljanu kuma yana taimakawa wajen ɓata sihiri da ke jikin mutum.
★ Amma a kula ★
☆Yin amfani da Za'afaran ba bisa ƙa'ida ba zai iya sawa mutum:-
* Mura
*Ciwon Kai
da kuma
*Ɗaukewar Miyau a baki.
★ Masana harkar lafiya ba suyi bayanin illar Za'afaran ga mace mai ciki ba, sun ma dai ce yana taimaka mata.
2)AMFANIN AMBAR GA LAFIYAR AL'UMMAH.
Ambar wani magani ne da ake samun sa daga jikin wata bishiya. Wato kamar irin farin ruwan nan dake fita daga jikin bishiya. Shi ne ake haɗa
shi da wasu sinadarai a samar da Ambar. Kuma ana samunsa a jikin bishiyoyi da dama. Idan ku ka duba wannan hoton za ku ga hoton Ambar kamar ƙaro.
Bayan amfanin da Ambar yake da shi wajen kiwon lafiya, haka ma yana taimakawa wajen magance cututtukan jiki da na jinnu ko sihiri.
Ana iya haɗa Ambar da wasu magunguna kamar zuma, miski, habba, zaitun, da dai sauransu, ayi amfani da shi don samun ingantacciyar lafiya
Yi amfani da Ambar kaɗan ka samu lafiya mai yawa da yardar Allah.
Ana samun Ambar na gari, ana samun na ruwa, ana samun na turare, ana
samun kwaɓaɓɓe na shafawa .
★ Sanya nishaɗi.
Ambar yana sanya nishaɗi idan aka sha kilogram ɗaya tare da zuma cokali ɗaya.
★Ƙara ƙarfin haƙora.
Ambar yana ƙara ƙarfin haƙori idan ana goge haƙora da man sa, wato Amber oil.
★Gyara ƙwaƙwalwa.
Man Ambar yana maganin cututtukan ƙwaƙwalwa idan ana shan sa tare da Man zaitun
da Habbatussaudaa.
★Maganin ciwon Hauka.
Ga mai lalurar hauka sai adinga tofa ayoyin Ruq'yah a cikin Ambar, a zuba a ruwa, a ba shi, ya sha kuma a dinga yi masa hayaki da shi musamman a
haɗa da miski wajen hayaƙin.
★Ciwon kai.
Ciwon kai ɓari guda sai a haɗa Ambar da jan miski da Man juda a kwaɓa, a dinga shafawa a kan kuma ana yin hayaƙin sa.
★Lalata sihiri.
Ana amfani da Ambar ta hanyoyi da dama wajen ɓata sihiri wanda mutum ya ci ko ya sha.
★Hawan jini.
Masu hawan jini su sha Ambar kaɗan a cikin ruwa.
★Gyaran fata.
Don gyaran fata da jin daɗin jiki, sai a diga Ambar kaɗan a cikin ruwan wanka ayi wanka da shi.
★Daɗin bacci.
Mai son yin bacci mai daɗi shi ma sai ya zuba Ambar kaɗan a ruwan wankansa.
★Hutawar ƙwaƙwalwa.
Ambar yana taimakawa ƙwaƙwalwa wajen samun hutu mai daɗi.
★Lafiyar zuciya.
Amfani da Ambar yana ƙara kyautata ƙarfin zuciya.
★Asthma.
Masu cutar Asthma su ma Ambar yana taimaka musu idan suna amfani da shi.
★Gudanawar jini.
Amfani da Ambar yana ƙara kyautata gudanawar jini a jikin mutum.
★Ƙarfin jima'i.
Yin amfani da Ambar yana kuma ƙara ƙarfin jima'i ga maza da mata.
★Narkewar abinci.
Amfani da Ambar na sauƙaƙa narkewar abinci a cikin ciki, yana hana kumburin ciki, tusa da sauran matsalolin ciki.
★Daɗin jiki.
Yana ƙara soyayya tsakanin miji da mata, idan ɗayan su yana amfani da
shi.
★ Warkewar ciwo da kashe ƙwayoyin cuta.
Sai a zuba man Ambar a kan
ciwon bayan a wanke shi. To zai warke cikin sauƙi insha Allah.
★ Amma a kula ★
.
Duk da amfanin Ambar kuma zai iya cutarwa .
★Mata masu ciki su guji amfani da Ambar, musamman sha a ciki.
★Ambar ɗin da ba a gauraya shi da wani abu ba kamar ruwa da makamantansu, to a guji shan sa kai tsaye.
★Ba'a sa Ambar a cikin ido.
★A guji ajiye Ambar kusa da yara.
3) AMFANIN ALMISKI
Shi Miski ba tsiro ba ne, ana samar da shi ne daga jikin Barewa, kuma Allah ya faɗe shi a Alqur‘ani.
AMFANIN SA
★ Yana maganin dafi kowanne iri.
★ Yana ƙara ƙarfin jiki.
★ Yana maganin hawan jini idan an sheƙa a hanci
★Yana maganin Aljanu, ya kan ma iya kashe Aljani idan an haɗa shi da Za‘afaran ana shafawa, ana kuma iya zuba shi a garwashi a dinga hayaƙi.
★Yana maganin warin gaba idan ana shafawa.
★Yana maganin namijin dare.
★Yana taimakawa masu matsalar haihuwa idan suna matsi da shi bayan gama al'ada.
Akwai jan Miski, akwai baki da kuma farin Almiski akwai kuma miski na ruwa.
Copyright BY: Sirrin rike miji
FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji
EMAIL: sirrinrikemiji@gmail.com
FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji
WhatsApp: +2348037538596
https://wa.me/message/2JY5R7B25CTJE1
0 Comments