Yawaitar Mutuwar Aure Sanadin Cikin Farko:




Yawaitar Mutuwar Aure Sanadin Cikin Farko:

Mutuwar Aure
Ana samun yawaitar mutuwar aure cikin al’umma, amma wannan karon zan duba ta bangaren masu sabon shigar cikin ne. Wannan yana daga cikin matsalolin da ‘yan uwa mata ke fuskanta. Mace tana marmarin an yi mata aure sai kuma bayan kwanaki kadan ko watanni sai a ji aure ya mutu saboda wasu matsaloli da ke faruwa wanda ita ma ba a son ranta ba.

 

Ma fi aksari maza kan kasa yi wa mata uzuri a lokacin da su ka fara ganin wasu bakin dabi’u ko wani canji a tare da su. Wanda wannan canzawar dabi’a ga mace na faruwa ne daga lokacin da ciki ya shige ta akwai abubuwan da ke canzawa a jikinta. Wannan zai jawo ta bar asalin yanayin ta ta koma wani.


 

Kadan daga ciki za ku ga a lokacin wata ba ta son tsabta ta jiki da muhali, ba ta son kamshi, yawan fada da miji, makwabta da duk wanda zama ya hada su, bakin hali, yawan zubar da yawu ko tara yawu a baki, kwadayi da zabe wurin abinci, rashin son kitso, kin yarda da miji a lokacin da ya bukaci ce ta, da sauransu.

 

To dukka wannan abin ita kanta mace ba ta na yi ba ne don son ranta ba, sai dai don haka abin ya zo mata. Mata da yawa kan shiga damuwa a daidai wannan lokaci musamman masu cikin fari saboda rashin sanin yadda abin yake da kuma yadda za a shawo kan matsalar. To daga nan in abubuwa sun cigaba da tafiya a haka sai a yi ta samun matsaloli daga karshe ya jawo mutuwar aure.

 

Ina Mafita? 

Mafita a nan ita ce:

Daga lokacin da mace ta tabbatar ta na da shigar sabon ciki to ta zama me kulawa da kanta sosai.
 

Ka da ta yarda cewar kasalar ciki za ta iya raba ta da maigidanta.
 

Idan me yawan zubar da yawu ce ko tara yawu a baki ta nemi wani abu da zai rage mata yawun kamar alawa ko gauta ko dai wani abu.
 

Ki zama mai tsabtace daki da muhalli saboda yawu na haifar da wani karni a duk in da aka zubar da shi.
 

Tsabtar gashin kai, ki daure ki rinka wanke kai da yin kitso duk sati.
 

Maigida ya zama me hakuri da kawar da kai ga mace a daidai wannan lokacin.
 

Ya zama me tattalin ta a wannan lokaci ya fahimci meye ta ke so, meye kuma ba ta so.
 

A lokacin da ta yi fushi kar ya biye ma ta balle ta kai su ga hayaniya.
 

Idan da hali a daidai wannan lokaci a nema mata mataimakiya wacce za ta dauki nauyin tsabtace wuri yadda ya kamata.
 

Shawara.:

 

Shawarata ga sababbin ma’aurata ita ce ku sa ni cewar wannan canji da ke faruwa ga mace ba abu ne da zai dauwama ba, abu ne da ke tafiya bayan wasu ‘yan lokuta. Wata mace har ace aljanu gare ta alhali shigar ciki ne. Maza ku rinka yi wa mata uduri a wannan lokaci, rashin yiwa juna uduri shi ya ke jawowa ayi ta samun matsaloli daga karshe a zo ana da sa ni. Musamman cikin fari ku yi la’akari da cewar matar ba ta taba yin ciki ba, kuma ba ta san irin matsaloli da ake fuskanta ba a lokacin shigar sabon ciki. Daga karshe wadannan matsaloli na iya faruwa ga duk mace mai ciki amma tafi tsanani ga masu cikin fari.

Post a Comment

0 Comments