Nazari A Kan Cutar Fitsarin Jini (I)



Nazari A Kan Cutar Fitsarin Jini (I)
  

Kumburi na glomeruli (cibiyar sadarwa ta magudanun jini) na koda yana haifar da yanayin da aka sani da glomerulonephritis. Kyakkyawan glomerulus yana ba damar futar gurbatattun kayan jiki kamar fitsari ta hanya mai sauki don wucewar fitsari kuma sannan yana ba magudanun jini na mara damar tsayawa a inda yafi da cewa dasu. Duk da cewa acikin glomerulonephritis, sunadarai kamar protein da kwayar jini sukan iya futa batare da an basu dama ba daga cikin glomeruli sukan iya jawo wata cuta ko matsala.

Nephron shine mafi karancin mataci na koda. Kowane nephron ya kunshi corpuscle na koda da renal tubule, shi kuma wannan renal corpuscle yana haduwa ta hanyar glomerul da Bowman. Shi kuma glomerule daya ne daga cikin nephron wanda yake bada damar tace gurbatattun abubuwan da jiki bayaso kuma ya zubar da ruwa wanda yayi yawa a mara. Don bincike kan lafiyar matarar fitsari ana bincikar shi wannan glomerula din ne.

Ciwon Glomerulonephritis na iya kasancewa mai muni na kullum kuma yana iya lalacewa saboda wasu dalilai da dama wadanda suka hada da cututtukan da ke kama da cutar siga. Idan yanayin ya kasance ba ayi magani ba kuma kumburin ko ciwon ya dade na tsawon lokaci, hadarin lalacewar koda yana karuwa sosai.


Menene Alamun Cutar glomerulonephritis?

A wasu yanayi daban-daban, glomerulonephritis yakan iya zama bai da wata alama sai dai shi irin wannan yanayi ana iya ganin shine kwatsam yayin binciken wani ciwo lokacin da aka dauki sanfurin jini da fitsari. Ire-iren alamun cutar da akan iya gani ko mai cutar yakan iya fuskanta sun hada da:

Kumfa ko tafarfasar Fitsari saboda yawan proteinuria: Glomerulonephritis yana canza yanayin ta cewar fitsari, wanda yake sa hauhawar yawan protein acikin fitsari. Kuma yawan protein acikin fitsari yakan jawo kumfa ko tafarfasar fitsari.
Haematuria: a cikin glomerulonephritis, jini yakan iya wucewa cikin fitasri. In yayi kamari, akan iya ganin jinin da kwara-kwaran idanuwa, lallai kuma ana iya yin bincike don sanin tabbacin jinin.
Edema: Shi protein alhakinsu ne ajiki su tabbatar da ruwa ko lema acikin magudanun jini don suke da alhakin lemar jini. A yanayin da protein yayi karanci ajiki, to lallai jini yakan iya diga cikin mafi tsara sannan ya ca kudu da fitsari,wanda wannan shi ke jawo Edema.

Hawan Jini: Lallai koda itace ke kula da bugawar jini ta hanyar boyayyar hanyar kwayar hormones wacce akafi sani da Renin-Angiotensin, wanda ke kula da bugawar jini. Kuma yana karfafa cewa, shi samun canji cikin koda tsarin koda saboda ciwon glomerulonephritis yakan iya jawo Hawan Jini.

Rashin samun garkuwar jiki: akan iya jin yanayi irin na Anaemi saboda rashin jini. Irin wadannan alamu sun hada da rashin samun garkuwar jiki.
 

Me ke Jawo Cutar Glomerulonephritis

mafi yawancin ciwukan glomerulonephritis suna zuwa ne sanadiyyar kwayoyin dake kula da garkuwar jiki. A wasu lokuta kuma hakan nan suke babu wani sanadi sananne. Su kwayoyi masu kula da garkuwar jiki sukan zama suna aiki fiye da yadda ya dace har su zama sun taba glomeruli. Wadannan na daya daga cikin manyan abubuwan dake sanadin cutar glomerulonephritis:

Cutar kwayoyin garkuwar jiki: lallai cutar kwayoyin garkuwar jiki wanda zaisa suyi aiki dakansu ba lokacin da ake bukatar aikinsu ban a daya daga cikin babbar alamar cutar glomerulonephritis. Lupus, muguwar cuta ce dake kama koda tare da mahadar zuciya, huhu da gabobi.
Cutar Infection: Garkuwar Jiki tana karyewa saboda aikin da takeyi yayi yawa har tana taba inda bai dace a taba ba. Irin hakan yakan jawo glomerulonephritis. Sai dai a bangaren shakewar wuya, jiki yana haifar da maguguna har suyi yawa. To wannan yawan da maganin yayi zai taru a glomeruli sannan ya jawo kumburi. Sannan wani infection kuma daka iya jawo glomerulonephritis sun hada da ciwon hanta Hepatitis B, Hepatitis C, HIB da dai sauransu.
Basculities: shi wannan bangaren ankamanta shine da kumburin jijiyoyin jini. Kamar polyarterities wanda ke janyo glomerulonephritis.
Magunguna: glomerulonephritis zai iya afkuwa sanadiyyar yawan shan wasu magunguna kamar NSAIDs(kwayar Nonsteroidal anti-inflammatory).
Kwayar halitta(Genetic): a wurare kadan, glomerulonephritis zai iya kasancewa cikin dangi. A irin wannan yanayi akan iya samun mutane dake da karancin ji da gani.
Idiopathic glomerulonephritis: a wasu kuma yanayin, asalin sanadiyyar cutar ta glomerulonephritis tazama boyayya.
Menene Rabe-raben Cutar glomerulonephritis?

Akwai hanyoyi da dama wadada za a iya bi akasafta cutar ta glomerulonephritis. Yakan iya zama ta dai-dai hanyar da yake habaka:

Chronic glomerulonephritis: shi wannan bangaren yana samuwa ne domin dade wa da yayi tare da mutum na tsawon shekaru. In alamun basu bayyana akan karamin lokaci ba, to wannan yakan jawo matsalar da zata lalata koda gaba daya.
Acute glomerulonephritis: shi kuma wannan bangaren an kasa shine sakamakon yawa ko saurin bayyanar alamun cutar ta glomerulonephritis. Wannan watakila yana biyo bayan infection ne ko kuma wasu dai sababin. A wasu lokuta, ba a bukatar yin wani magani don yanayin yakan komawa ya zama dabi’ar mutum. Amma a wasu lokuta kuwa dole ne anema magani.
Classification may also be done based on the cause of glomerulonephritis:

Glomerulonephritis na matakin farko: Shi wannan mataki yana faruwane akan kanshi ba wai sai da wani daliliba kamar ace akwai wata cuta acikin mutum.
Sannan kuma akan iya kasafta ciwon ta hanyar sanin abinda ya jawo cutar ta glomerulonephritis.

glomerulonephritis mafi shuhura: shi wannan bangaren yana faruwa ne akan kanshi ba wai saboda wata cuta data ke jikin mutum ba.

Glomerulonephritis mai mataki na biyu: shi kuma wannan matakin yana faruwa ne saboda wata cuta datake cikin jikin mutum. Su kuma wannan cututtukan dasuke janyo wannan cutar sun hada da: infection, lupus, da ciwon siga.
IgA glomerulonephritis: shi kuma wannan matakin na glomerulonephritis wata kila yana faruwa ne saboda taruwan kwayoyi masu fada da IgA a cikin glomeruli. Glomerulonephritis za a iya kasafta shine a wannan yanayin ta hanyar lura da inda ko wurin da ya taru da kuma girman barnar da yayi a cikin glomeruli.
Membranous glomerulonephritis: a acikin irin wannan bangaren, kawai fatar daki kula da glomerulus ce kawai take tabuwa amma sauran jiki baya tabuwa yananan a yadda akasanshi.
 

Post a Comment

0 Comments