Rashin sha’awar iyali da dalilansu 1


Rashin sha’awar iyali da dalilansu 1


Daga BILKISU YUSUF ALI


Tambaya:

Malama Ina da tambaya. Wai shin me yake hana sha’awar iyali shekararmu biyar da matata amma daga baya sai na ji sam ba na sha’awarta.

Amsa:

Wannan matsale ce da abu biyu yake kawo ta. Na farko dai akwai yanayin zamantakewa inda kuma na biyun zai iya kasancewa rashin lafiya ce ke haifarwa. Katsewar sha’awar miji ga matarsa ko mace da mijinta yana hana zama lafiya a zamantakewar aure sannan ya hana al’amuran rayuwa na yau da gobe gudana, saboda al’amuran aure kaso ma fi rinjaye ya ta’allaƙa ne a kan sha’awa tsakanin iyali. Amma kafin mu fara faɗin dalilan da ke kawo rashin sha’awa ta ɓangaren lafiyar jiki bari mu ɗau kason farko na yanayin zamantakewa. Wanda wannan yanayi, yanayi ne ko aiki ne na ƙwaƙwalwa.


 
Rashin kwanciyar hankali:

Duk lokacin da ya kasance babu kwanciyar hankali tsakanin ma’aurata ba yadda za a yi sha’awa ta gitta. Rashin kwanciyar hankalin nan, ko dai ta ita matar da mijin ko mijin da iyayenta ko da yanayin gari ko matsugunni da dai duk wani nau’in rashin kwanciyar hankalin da zai janyo rashin nutsuwa da fargaba ko zulumi. Hatta a wurin aiki in har namiji yana fama da fargaba da rashin nutsuwa to tabbas zai iya neman sha’awa ya rasa. Sannan ga macen da take da yawan ƙorafi da daddare sawa’un matsalarta ko ta kishiya ko ta ‘ya’yan miji a lokacin da namiji ya zo da buƙatarsa ita ma kan haifar masa rashin kwanciyar hankali wanda duk wannan yana iya janyo rashin sha’awar Maigida ga iyalinsa.


Talauci:

Talauci ko rashin abin hannu shi ma babban makami ne da ke yanke sha’awa. Duk lokacin da samun mutum ya yi ƙasa kuma buƙlatunsa suka ninka har ya shiga saƙe-saƙen mafita to fa zai yi wuya duk maganin da zai sha ya yi masa tasiri kan wannan matsalar, dole makarin matsalar shi ne a samu abin da ake buƙata. Hatta rashin muhalli mai kyau da nutsuwa shi ma kan zama barazana ga sha’awa tsakanin iyali.

Roƙo:

 
Akan samu mata masu roƙe-roƙe ga maigida kuma sukan riƙe makamin roƙonsu shi ne lokacin da maigida yake da buƙatar kasancewa da su. Daga lokacin da wannan ya zame wa mace al’ada kuma miji ya tsani hakan to yana iya zama wani sanadari na kashe masa sha’awar maiɗakinsa.

Ƙazanta:

Duk lokacin da Maigida zai kalli abin da ba ya son idonsa ya kalla, ko ya shaƙi abin da ba ya son hancinsa ya shaƙa, ko ya taɓa abin da ba ya son ya taɓa, to tabbas a sannu Uwargida za ta gusar masa da dukkan sha’awarsa. Don haka tsafta tana da matuƙar tasiri wajen ƙarfafa sha’awar Maigida. Haka ƙamshi na cikin sinadaran da ke ƙarfafa sha’awa.

Biyayya:

Duk lokacin da mace ta zama ba ta biyayya ga mijinta , kullum tana cikin ɓata masa rai nan ma zai yi wuya yake sha’awarta. Ita irn wannan biyayyar ba sai iya kansa ba hatta iyayensa in ya lura ba ta mutuntawa ko darajjantawa to tana iya fita a ransa.

Rashin ni’ima ga mace:

Akan samu mata marassa ni’ima da iya sarrafa maigida yayin mu’amalar aure wannan nau’ikan matsalolin sukan shafi zamantakewa da kuma sha’awa tsakanin iyali. Haka ma idan namiji ya fuskanci cewa matar ba ta sha’awarsa ko ma ba ta son kasancewa tare da shi, irin wannan matsalar kan kawo matsalar.

Ha’inci da ƙarya da cutar da abokin zama ko ’ya’yansa:



Waɗannan dalilan kan sa mace ta fita a zuciyar namiji har ya ji ba ya son ko ganinta bare sha’awarsa ta kai gare ta.


Akwai dalilai da dama wanda na zamantakewa ne ke kawo wannan matsalar ba wai rashin lafiya ba.Za mu ɗora daga inda muka tsaya a mako na gaba in sha Allah.



Share this: 🔔

Post a Comment

0 Comments