Kamin Mace Ta Amince Maka Sai Tayi La'akari Da Wadannan Abubuwan:


Kamin Mace Ta Amince Maka Sai Tayi La'akari Da Wadannan Abubuwan:

 
Ba duk mace bace da zaran ka furta mata kana sonta zata soma rawan jiki tace maka ta amince ba.

Akwai matan da kamin su amsa maka sai sunyi maka nazari na tsanake.

Cikin nazarin da irin wadannan matan suke yi suna yi ne domin kokarin gano wasu abubuwa game da kai kamar haka:

#tsangayamalam 
1: Matsayinka; Wasu matan sai sun yi nazarin matsayin ka a rayuwa kaf kamin nan su bude maka kofar soyayya. 

Irin wadannan matan zasu tabbatar da abunda kake yi a rayuwa ya dace su aureka. Da zaran sun samun amsar wannan tambayar suna iya amince maka.

2: Yadda Kake Mu'amala Da Mutane: Mata masu wayo sukan baiwa wanda ya nuna yana sonsu da aure tazara na rashin tabbatar masa da soyayyar su nan take har sai sunyi nazarin yadda mutumin yake mu'amalar sa da mutane a zahiri da kuma badini.

Akwai wasu mazan ta waya ma yake kasa cinye jarabawan da mace zata masa.
Irin mazan nan masu yiwa mutane tsawa ko fada a waya da nuna musu isa, mata sukan gujewa irin wadannan mazan. Bare kuma su gani ko a zahiri baida mu'amala mai kyau.

3: Zurfin Hakurinka: Mata masu dabara suna gwada mazan dake sonsu da aure ta hanyar jimriya na hakuri da suke da shi.
Akwai hanyoyi da dama da mata suke yin amfani dasu domin gwada zurfin hakurin namijin da yake son aurenta. Da zaran ta fahimci ba mai hakuri bane zata koreshi da kalmar an mata miji.

4: Kwalliya Da Ado: Mata masu dabaran zaben mijin aure sukan yi la'akari da yadda wanda yazo nemansu da aure yake kwalliyarsa da adonsa.

Wasu matan basa son ganin namiji mai shafe shafe irin na mata. Haka akwai matan da basu son ganin wanda zasu aura da shiga irin na yarinta. Haka nan mata basa son auren namiji wanda bai iya kwalliya ba. Don haka kwalliya da adon namiji zai iya bashi macen da yake so ko kuma ya hanashi.

5: Yadda Ka Damu Da Ita: Nunawa mace kula shine abunda take dauka da mahimmanci fiye da komai. Mata masu dabara suna nazarin yadda namiji ya damu da rayuwarsu kamin su amince masa.
Kula shine abunda mace take sma daura namijin da furta yana sonta a sikeli kamin ta amince masa. #tsangayarnalam 
Da fatan samari da mazan da suke neman karin aure zasu kiyaye Wadannan abubuwa muddin wajen macen datasan abunda take yi suka je, zai yi wuya farat daya ta amince masu da zancen aure ko soyayya ba tare da ta daura su akan sikeli ba.

Post a Comment

0 Comments