HANYOYIN DAINA ISTIMNA'I GA MATASA:


MASTURBATION (ISTAMINA'I):

HANYOYIN DAINA ISTIMNA'I GA MATASA 🙍 

SHARE 💧

Biyawa kai bukata ta hanyar istimna'i wato masturbation da turanci, nufin duk wata hanya da mutum zai bi don ya samarwa kanshi biyan bukata wato zubar da maniyyi ba tare da saduwa tsakanin jinsin mace da na miji ba. 

A likitance masana sun bayyana cewa istisma'i ba za'a kira shi da suna ciwo ba, haka kuma babu takamammen maganin da zai kawar da wannan al'amari kai tsaye illa canza ko sauya tunanin jama'a musamman wadanda suka rigaya suka afka cikin wannan dabi'ar.

illar istimna'i (masturbation) ga lafiyar bil'adama:
💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧
🌿 Masanan har ila yau, sun bayyana cewa wannan dabi'ar kan jawo ciwon zuciya ga mai yin ta. 

🌿 Ya kan jawo rashin karfin gaba. Duk mai wannan dabi'ar yau da gobe zai rasa karfin gabanshi kwata-kwata.

🌿 Yana haifar da kiyayya ga ma'aurata.🤦🏾‍♀️

🌿 Masana sun kara bayyana cewa wanna dabi'ar a bisa binciken su kan iya hana haihuwa.

👴Shawara ta yadda za'a iya gujewa dabi'ar istmna'i:

(1)_Da farko in mutun ya tsinci kanshi cikin wannan dabi'ar kuma yana bukatar dainawa, to, sai ya kudurta a cikinn zuciyarsa cewa zai daina sabili da dabi'ar na da makutar wuyar dainawa muddin ta yi wa mutun katutu.

(2)_Mutum yayi kokarin aure idan da haliyin sa.

(3)_ A daina kadaita a dakinka ko gidanka, ka rika shiga mutane dan mafiyawa kadaita ke sa wasu mutane wannan dabi'ar

(4)_ A guji shan kwayar da zata tada sha'awar jima'i

(5)_A guji yawan kallon ababen da zai tada sha'awa, hoto ko bidiyo, kana a guji yawan zantutukan batsa.

(6)_A yawaita jin karatu ko wa'azi a ko da yaushe.

Idan aka kiyaye wadannan abubuwa, Insha Allahu za'a Sami saukin abin.
🍵🍵🍵🍵🍵🍵🍵🍵🍵🍵🍵🍵🍵🍵🍵
Copyright BY: Sirrin rike miji
FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji
EMAIL: sirrinrikemiji@gmail.com
FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji
WhatsApp: +2348037538596

https://wa.me/message/2JY5R7B25CTJE1

Post a Comment

0 Comments