GASKIYAR ABUBUWAN DA KE HAIFAR DA QARANCI KO RASHIN SHA'AWA A TSAKANIN MA'AURATA:
SHARE 🔔
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
Duba da yawan wasikun da nake samu akan matsalar rashin Sha'awa a tsakanin ma'aurata, yasa na yi dogon nazari akan wannan matsalar.
Kamar yanda muka Sani rashin Sha'awa a tsakanin ma'aurata yana haifar da lalacewar aure.
A gaskiya matsalolin sun kasu ne gida biyu;
1. Akwai matsalolin da yanayin rayuwa da zamantakewa ke haifarwa.
2. Akwai wayanda larura ko rashin lafiya ke haifarwa har a kai ga an rasa sha’awa tsakanin iyali.
Kamar yanda muka Sani Cututtuka da daman gaske kan shafi matsalar sha’awa har ya zamana tun ana fama da kaɗan-kaɗan har ya kai ga sha’awar ta fita gaba ɗaya.
Akwai matsala da larura ta rashin lafiya akwai kuma wadda ta shaiɗanu ce wanda wannan wani fage ne daban idan lokaci ya bayar za mu yi bayanin su anan gaba.
Amma a yanzu zan yi cikakken bayani ne kan matsalar rashin lafiya da wani ciwo ya haddasa.
Hanyar rabuwa da wannan matsala kuwa shi ne neman magani a cikin lokacin da ta dace
Yan uwa yana da kyau neman maganin rashin Sha'awa a tsakanin ma'aurata.
Kuma ayi a hankalli domin da yawa mutane suna afkawa a cikin wannan matsala sanadiyar magungunan da ake ake amfani da su.
Ba ko wane magani ya kamata macce ta yi amfani da shi ba.
MATSALAR QARANCIN KO RASHIN SHA'AWA.
Kamar yanda muka Sani Akwai matsala da larura ta rashin lafiya akwai kuma wadda ta shaiɗanu ce wanda wannan wani fage ne daban wanda masana wannan suna nan. Ni zan yi bayani ne kan matsalar rashin lafiya da wani ciwo ya haddasa. Makarin wannan matsala kuwa shi ne neman magani.
1. Ciwon sanyi. Shi ciwon sanyi yana hana sha’awa kwata-kwata. Ciwon sanyin nan kala-kala ne, akwai sanyi na jiki kuma akwai na mara. ko irin wanda ake ɗauka yayin amfani da banɗaki marar tsafta ko a jikin abokin mu’amala da sauran nau’ikan sanyi da ke sa zubar farin ruwa ko bushewar gaba ko zafi yayin kusantar juna. Kowanne yana da tasiri a jikin ɗan’adam da mu’amala ta aure. Wannan yana hana sha’awa da gamsar da abokin zama.
2.Ciwon basur shi ma yana hana sha’awa wanda ya kamata mutane su kula da abunuwan da suke ci saboda yawanci matsalar kan taso daga ci ma da yanayin tsarin rayuwa.
3.Ciwon damuwa ko fargaba shi ma yana ɗauke sha’awa.
4. Ciwon suga yana hana sha’awa kuma ko da sha’awar ta samu to za a ga namijin ba shi da cikakkiyar lafiyar kusantar iyalin.
5. Yin istisma’i (amfani da hannu) shi ma yana hana sha’awa. Haka amfani da wasu abubuwa da mata kan yi don biya wa kansu buƙata shi ma yana kassara sha’awa.
6. Ga matar da aka taɓa yi mata fyaɗe musammam in har ba ta sami kulawar jami’an lafiya ba shi ma yana haifar da matsaloli ciki kuwa har da akwai wannan matsala ta rashin sha’awa.
7. Yawan amfani da magunguna musamman na mata barkatai marassa inganci haka su ma mazan akwai waɗanda suke mayar da magunguna musamman na maza wata ƙa’ida kullum sai sun sha , to wannan kan haifar da matsaloli musamman na ɗaukewar sha’awa ga kowanne ɓangare..
Copyright BY: Sirrin rike miji
FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji
EMAIL: sirrinrikemiji@gmail.com
FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji
WhatsApp: ☏+2348037538596
https://wa.me/message/2JY5R7B25CTJE1
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
0 Comments