AMFANIN TAFARNUWA GA DAN ADAM:
🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄
1.Bunkasa Garkuwar Jiki.
🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄
A wani bincike da manazarta su ka gudanar kan kwayoyin halittar dan-adam (cells) dangane da amfanin tafarnuwa ga lafiya, sun gano cewa, tafarnuwa na inganta kwayoyin halittar jini, da ake kira "White blood cells" da turanci, ta hanyar kara adadin wani sanadari da ake kira 'glutathione' a turance.
To su Kwayoyin halittar jinin da ake kira 'White blood cells' su ne ke samar wa jiki kariya daga cututtuka. A takaice, ka iya cewa, su ne garkuwar jikin dan-adam.
Wannan ya sa tafarnuwa ke taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa garkuwar jikin dan-adam ta samu damar fatattakar duk wata cuta da ka iya kai wa jikin farmaki.
2. Maganin Mura
Daga cikin amfanin tafarnuwa ga lafiyarmu, akwai maganin mura.
🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄
Binciken masana kiwon lafiya ya tabbatar da yadda ake amfani da tafarnuwa wajen samun saukin mura da dangoginta da kan shafi makogoro, kirji da hanci da sauran su.
Wani nazari da aka gudanar kan wasu mutane 120, ya nuna cewa baya ga maganin mura da tafarnuwa ke yi, hakanan yawan amfani da ita na bai wa jiki riga-kafin kamuwa daga murar.
Ga duk mutumin dake fama da mura, kuma ya ke son amfani da tafarnuwa don samun sauki, sai ya ci salar tafarnuwa 2 zuwa 3 a rana, ko kuma ya hada shayin tafarnuwa.
Abubuwan da zai hada shayin sun hada da tafarnuwar ita kanta, da kuma citta, da zuma. Zai sha wannan shayi sau biyu a rana, da safe da yamma kenan.
3. Rigakafin Kamuwa Da Cututtukan Zuciya: 🫀
🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄
Yin amfani da tafarnuwa a kullum, a cikin abinci ko kuma danyarta, na taimakawa wajen rage yawan adadin sanadarin' cholesterol' saboda ta na aiki irin na 'anti-oxidant' sakamakon sandarin 'Allicin' da ta ke kunshe da shi.
Har ila yau, tana da amfani sosai wajen daidaita hawan jini da kuma daidaita yawan sukari dake cikin jini..
Sakamakon haka ne ya sa masana kiwon lafiya su ka nuna tafarnuwa na inganta lafiyar zuciya da kuma ba ta rigakafin kamuwa da cututtukan da kan shafi zuciya.
4. Gyaran fata Da Kuma Gashi.
🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄
Daga cikin amfanin tafarnuwa ga lafiyar dan-adam, har da gyaran fata da kuma gashi. Bincike ya nuna cewa, tafarnuwa na da wasu sandarai da ke dakile yamushewar fata, sannan kuma wasu sanadaran na tafarnuwa na da amfani wajen hana zubewar gashi.
Kamar yadda masanan su ka bayyana abubuwan ban al'ajabi da albasa ke yi dangane da gyaran gashi, sun bayyana cewa, amfanin 'yar uwarta, tafarnuwa ya zarta na albasa. Mutum zai samu fa'idar tafarnuwa dangane da gyaran fata da gashi ta hanyar shafa dandakakkiyar tafarnuwar, ko kuma shafa man tafarnuwar a gindin gashi don hana zubewar gashi ko karyewarsa.
🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄
Hakanan, wannan hadin na kara yawan gashi da kuma hana shi karyewa.
Ki samu man tafarnuwa, ki hada shi da man kwakwa da man zaitu ki rinka shafawa a kanki. Ana son ki tabbatar kin game kanki da wannan hadi ta hanyar murzawa yadda zai samu matsirar gashinki. Za ki ga abin mamaki.
Baya ga gyaran fata da tafarnuwa ke yi, hakanan, ta na bayar da kariya ga fatar wajen kamuwa daga wasu cututtukan fata.
5. Saukar Da Hawan Jini:
🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄
'Angiotensin II', wani sanadari ne dake haddasa matsewar jijiyoyin jini, sakamakon haka sai ya haifar da hawan jini. To akwai wani sanadari dake cikin tafarnuwa mai suna 'Allicin' wanda ke hana aikin sandarin Angiotensin II, wanda hakan ke taimaka wa wajen rage hawan jini.
Baya ga haka akwai wasu sanadari dake cikin tafarnuwa mai suna 'polysulphi' da kwayoyin halittar jini mai launin ja(Red Blood Cells) ke rikidar da shi zuwa wani sanadari da ake kira 'hydrogen sulphide. Shi wannan sanadarin ne ke sassauta matsewar jijiyoyin jini, sakamakon haka sai ya taimaka wajen saukar hawan jini.
6. Taimakawa Matsalolin Numfashi.
Kamar yadda mu ka ambata a sama cewa yin amfani da tafarnuwa yau da kullum na rage wa tare da maganin mura da sanyi. Baya ga maganin kaikayin makogwaro.
Kari kan haka, tafarnuwa na iya maganin cututtukan da ke da alaka da numfashi. An tabbatar da cewa, tafarnuwa na taimakawa mutanen da ke shan wahalar numfashi, kamar ma su cutar Asma ko kuma murar da ta yi tsanani har ta haddasa shakewar hanyar numfashi da sauran su.
Karanta: Amfanin Jima'i Ga Ma'aurata.
7. Ciwon Hakori.
Sanya dandakakkiyar
🦷🦷🦷🦷🦷🦷🦷🦷🦷🦷🦷🦷🦷🦷
tafarnuwa a kan hakorin da ke ciwo zai iya taimakawa wajen samun saukin ciwon hakori, sakamakon aikin 'antibacterial da 'analgesic' da tafarnuwar kan yi..
Amma ya na kyau ka san cewa, tafarnuwa kan haifar da radadi kan dasashi.
8. Riga-kafin Ciwon Daji:
🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄
Har ila yau dai, daga cikin amfani tafarnuwa ga lafiyarmu, akwai riga-kafin kamuwa daga cutar daji. Masana sun ce, amfani da tafarnuwa yau da kullum na rage hadarin kamuwa da ciwon daji.
Tafarnuwa na taka wannan muhimmiyar rawa ne, sakamakon sanadaran 'allyl sulphides' da tafarnuwa ke da su. Su wadannan sanadarai ne ke aikin samar wa jiki riga-kafin kamuwa daga cutar daji.
9. Ciwon Ciki Bayan Haihuwa.
🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄
Wasu mata kan fuskanci matsalar ciwon Ciki Ko kullewar mara bayan sun haihu, kuma wannan matsala kan ci mu su tuwo a kwarya, har su galabaita. To ga matar dake fama da wannan matsala, sai ta yi amfani da tafarnuwa. Ta samu man tafarnuwa babban cokaki daya, sai ta zuba cikin ruwan zafi kofi daya. Za ta sha sau uku a kowacce rana har tsawon kwanaki uku.
10. Ciwon Mara Lokacin Jinin Al'ada:
🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄
Tafarnuwa na da amfani ga mata, musamman ma matan da ke fama da ciwon mara a duk lokacin da jinin al'ada ya zo mu su. Ga macen da ke fama da ciwon mara ko ciwon ciki lokacin al’ada, ta samu man tafarnuwa ludayi guda, da zumarta mai kyau wacce ba ta da algus ludayi biyu, sai ta hade su waje guda a mazubinta mai tsafta ta adana shi. Daga nan sai ta ke shan cokali biyu da safe, cokali biyu da yamma.
Hakazalika, wacce jinin al'adarta ya ke ma ta wasa, ita ma wannan hadin za ta yi, kuma yadda mai waccar matsalar ta sha ita ma haka za ta sha.
11. Tafarnuwa Na Taimaka Wa A Samu Isashen Barci
Ga mutanen da ke fama da rashin samun barci, sai su yi amfani da tafarnuwa don su samu isasshen barci. .
Ga yadda za su yi, tun farko su samu zumarsu mai kyau da kuma tafarnuwa, amma sai su daka tafarnuwar don su samu garinta, sai su zuba garin tafarnuwar rabin ludayi cikin zumar su gauraya yadda za su hadu sosai, suke shan babban cokali daya sau uku a kullum.
Sannan kuma su samu man tafarnuwa su ke shafewa jikinsu..
ALLAH SHINE MASANI.
🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄🧄
0 Comments