Amfanin kubewa guda 5 a jikin Dan Adam:



 

Kubuwa wata nauyin kayan lambu ne da akan yi amfani wajen yin miya. 

Hasashe sun nuna cewar Kubewa ta samo asali ne daga kasar Habasha wato Ethiopia da kuma Masar wato Egypt tun karni na 12.

 Mutane da dama na shan miyar kubewa don dandano da dadinta ne kawai ba tare da sanin tarin alfanun da ke tattare da ita ba.

 Hakan yasa muka binciko maku kadan daga cikin amfaninta a matsayin magani ga garkuwar jikin Dan Adam. 

Amfanin kubewa guda 5 a jikin Dan Adam Source: UGC Ga su nan kamar haka:

 1. Ana amfani da kubewa wajen maganin cutar siga wacce ta zamo ruwan dare a tsakanin al'umma a yanzu.

 Tana dauke da sinadarin fibre a cikinta, wanda ke taimakawa wajen daidaita yawan siga a cikin jikin dan Adam, wanda kuma ke rage karfi ciwon siga ko ma maganinsa. 

2. Kubewa na matukar tallafa wa masu juna biyu wajen inganta lafiyarsu da kuma na jaririn da ke ciki domin kubewa na kunshe da dimbin Vitamin B da ke samarwa da kuma inganta sabbin kwayoyin halitta na gina jiki da. lafiyarsa. 

3. Ta na kuma maganin cutar wahala wajen fitar da numfashi wato Asthma, saboda sinadarin Vitamin C da ke tattare ta ita. 

4. Ga mai son kara inganta fatan jikin sa ya yi laushi da santsi kamar yaukin kubewar toh ya lazumci amfani da ita. 

5. Yana matukar maganin karancin jini a jiki domin kubewa na kunshe da sinadarin Iron sosai.

 Kuma yawan amfani da kubewa na sanya idan ka ji rauni jini ba zai zuba da yawa har ya yi wa mutum lahani ba. 

Post a Comment

0 Comments