AURAN MARA LAFIYA.
Mal.Aminu Ibrahim Daurawa
Bincike akan lafiyar maaurata da bayyana gaskiya idan akwai wata larura ko wani ciwo yana cikin abin da ake bukata a sani kafin aure.
Gwajin lafiya kafin aure da tabbatar da lafiyar maaurata yana cikin manyan abubuwa da ake so a tabbatar da su kafin aure, domin kada sai anyi aure wani abu ya bayyana wanda zai iya kawo wa auran cikas.
Idan mace ko namiji bashi da lafiya, wajibi a bayyana haka kafin lokacin aure, akwai wasu cututtuka da wasu larurori da malamai suka bayyana, kamar kuturta, hauka, farfaɗiya, da bugun aljan, ko waɗanda suka shafi mu'amala ta aure ga namiji ko mace, sun faɗi larurori da yawa da suke samun maza da wasu da suke samun mata, wacce idan ba a bayyana ta ba, ga ma'aurata za ta iya zama anyi ha'inci da zamba da ɓoye aibi. Kuma za a biya shi dukkan abinda ya kashe idan aka yaudare shi aka ɓoye masa aibi, haka shima zai yi idan ya yaudare ta, ya ɓoye mata wani abu da ya ke da shi na aibi.
Daga cikin abubuwa da ake samu daga ɓangaran maza akwai :
1. Mutuwar gaba.
2. Rashin lafiyar gaba.
3. Ƙanƙancewar gaba
4. Girman gaba da yawa.
5. Gutsirewar gaba.
6. Rashin haihuwa.
7. Rashin sha'awa.
8. Rashin marena.
Gamai da mata kuma ana samun kamar haka :
1. Toshewar gaba.
2. Haɗewar gaba da wajan fitsari yoyan fitsari.
3. Farkewa da ƙaruwa.
4. Warin gaba.
5. Fitowar ƙashi a tsakiyar gaba.
6. Rashin sha'awa.
7. Rashin lafiya mai tsanani
8. Zubar jini mai tsanani
9. Rashin zuwan al'ada.
A kwai larura ta fili, kamar makanta gurguntaka, ido ɗaya, ko rashin wata gaɓa, duka wannan ya kamata asan da shi, kafin aure, domin wani mutum ya je neman aure amma yana da larura ta rashin gutsirewar gaba, sai S. Umar yace masa ka gayawa matar,? Domin wajibi ta san da wannan domin kada ka yaudare ta.
0 Comments