Hanyoyi 8 da za ka bi don samun gamsuwa da gamsar da iyali a lokacin Saduwa:
Sakamakon bincike ya nuna cewa matsalar rashin haihuwa kan shafi ma’aurata shida a cikin ma’aurata 10 a duniya.
Binciken ya kuma nuna cewa mafi yawan lokuta akan samu magidanta uku daga cikin magidanta shida dake da matsalar rashin haihuwa.
Likitoci sun yi kira ga ma’aurata da su rika zuwa asibiti don ganin likita a maimakon su zauna a gida ana ta zarge zarge da ba haka ba.
Jami’an lafiya sun ce ana iya warkewa daga wannan matsala idan har an gano da wuri.
Ga hanyoyi
1. Rage Shan giya da taba
Baya ga cutar da lafiyar mutum da shan giya da taba ke yi wadannan abubuwa na hana namiji haihuwa.
Domin guje wa irin haka ya kamata maza su rage Shan giya da taba ko su daina sha gaba daya.
2. Samun hutu
Yawan yin aiki ba tare da samun hutu ba na cutar kwakwalwa sannan da hana namiji iya gamsar da iyalinsa inda haka ke hana namiji iya yi wa mace ciki
3. Shan vitamin C
Vitamin C sinadarin ne dake taimakawa wajen warkar da rauni a jikin mutum sannan yana taimakawa wajen warkar da mura.
Vitamin C na hana rashin haihuwa a jikin namiji domin yana inganta karfin maniyi.
4. Motsa jiki
Matsa jiki na da mahimmanci ga jikin namiji domin yana taimakawa wajen inganta kuzari a jikin namiji.
5. Kiba
Yawan kiba a jiki na cikin matsalolin dake hana namiji iya yi wa mace ciki
Yawan kiba a jiki na hana zuciyar mutum bugawa yadda ya kamata sannan yana rage wa namiji shi’awa.
6. Samun sinadarin Vitamin D
Cin abinci dake dauke da sinadarin Vitamin D na hana namiji samun matsalar haihuwa.
Kifi, hanta, kwai, naman sa na cikin abincin dake dauke da sinadarin Vitamin D.
7. Cin Almonds, hazelnuts da walnuts na kwar da matsalar haihuwa a jikin maza domin suna dauke da sinadarin Vitamin E, zinc, foliat, omega-3 dake inganta kuzarin namiji.
8. Gujewa amfani da magunguna feshi na gonna.
Wasu masana kimiya a kasar Amurka sun gano cewa maganin feshi da ake amfani da shi domin kashe kwari a gonaki na hana maza haihuwa.
A dalilin haka likitoci suka yi kira ga maza musamman manoma da su rika yin la’akari da yadda suke amfani da magungunan feshi a gonakinsu domin guje wa matsalar rashin haihuwa.
SHARE.
0 Comments