Amfanin Namijin Goro:
Namijin goro dai wani nau’i ne na goro wanda akasari ake amfani da shi a kasashen Afrika. Turawa na kiransa da suna “bitter kola”
Masana a fannin kiwon lafiya sun bayyana namijin goro da antibiotics mai matukar amfani ga rayuwar bil’adama. A nazari da aka gudanar daban-daban a sassan Afrika da ma na Turai, an tabbatar da cewa namijin goro na da amfani kamar haka:-
Kamar yadda kwararriya a fanin nazarce-nazarce a sashin kiwon lafiya na Nijeriya Natural Medicine Debelopment Agency (NNMDA), Mrs. Chinyere Nwokeke ta tabbatar da cewa, namijin goro yana taimakawa masu dauke da cutar HIB ko kanjamau ta hanyar rage radadi da gubar da cutar ta HIB take dauke da shi saboda sinadarin “antibacterial” da kuma chemical na “Saponin” da yake cikin ta.
A wani nazari da masana suka gudanar a sashin horar da likitoci na jami’ar tarayya dake Lagos, masanan sun bayyana kamar yadda aka wallafa a mujallar “Middle East African Journal of Opthamology” cewa, namijin goro na kashe cutar Glaucoma wacce take lalata idanun bil’adama.
Har ila yau, masana a fannin kiwon lafiya sun tabbatar da cewa, namijin goro na maganin cutar cizon sauro wace ake kira da “malaria” saboda sinadarin “kolabiron” da ke cikin ta.
Kwararru a fannin nazarce-nazarce a sashin kiwon lafiya na jami’ar Obafemi Awolowo dake Ile’ifi, sun tabbatar da cewa, namijin goro na magance amosanin gabbai (arthritis). Har ila yau, a nashi jawabi Dr. Olayinka O. Adegbehingbe ya jaddada hakan a wani nazari da ya gabatar kuma aka wallafa a mujallar, issue of the Journal of Orthopaedic Surgery and Research, a watan Juli na shekarar 2008. Kwararren ya tabbatar da cewa namijin goro na matukar magance cutar gabobin jikin.
Har ila yau, an tabbatar da cewa namijin goro na karawa maza kuzari.
0 Comments