Hanyoyi 7 da Za Ka Iya Faɗaɗa Kasuwancinka:




Faɗaɗa kasuwanci abu ne da yake da matuƙar girma domin yana buƙatar ƙwarewa, sanin madafun aiki, dabaru da kuma kuɗaɗe. Akwai mutanen da aikinsu kawai shi ne tsara wa kamfani yadda zai faɗaɗa kasuwancinsa duba da yanayin kamfanin da kuma inda yake, sannan da kayan da yake sarrafawa. Ke nan wannan aiki ne na ƙwararru.

Amma duk da haka, waɗanda za su fara faɗaɗa da bunƙasa kasuwanci su ne masu shi, saboda su suka san yanayin kasuwancinsu a karon farko da kuma adadin tattalin arziƙinsu. Don haka a nan ana buƙatar wasu dabaru da tsare-tsare na faɗaɗa kasuwanci daga wajen wanda ya kafa kasuwancin. Waɗannan hanyoyi guda 7 za su taimaka wajen haɓɓaka kasuwancin mutum:

1. Tsarin kasuwanci
Mataki na farko da ake ɗauka don faɗaɗa kasuwanci shi ne tsara tsare-tsaren kasuwanci don dacewa da ƙudirin dan kasuwa, kasuwa da kasuwanci, kwastomomi, wurin kasuwanci da kuma kuɗaɗen jari da na shiga. A nan ɗan kasuwa zai tsara kamar a kundi, duk yadda kasuwancinshi zai kasance, kamar:

Sunan kamfani
Taƙaitaccen bayani a kan kamfani
Cikakken bayani a kan kamfani
Dabarun kasuwanci na karan-kanka
Dabarun shiga kasuwa
Yanayin tafiyar da kamfani da tsarukansa
Cikakken bayani a kan kayan kamfani
Dabarun sayar da kaya
Dabarun faɗaɗa kasuwanci
Kuɗaɗen jari da na shigarwa
Hanyoyin samu
Ma’aikatan kamfani
Daga littafin Zo Mu Gina Kamfani

2. Ingantattun kaya
Mafi girman abunda yake janyo wa ɗan kasuwa kima a idon kwastomominsa da kuma sauran al’umma shi ne inganta kayanshi sai na gaba kuma kyautata mu’amala da su. Kevin Systrom, maƙirƙirin manhajar Insttgaram ya ce, “ingantattun kaya su ke sayar da kansu.” Ke nan, matuƙar ɗan kasuwa ya inganta kayanshi to ba ya buƙatar sake tallata su, waɗanda suke sayensu su za su janyo wa ɗan kasuwa kwastomomi.

3. Kyautata mu’amala da kwastomomi
Abunda zai fi farantawa kwastoma rai kuma kullum ya kasance tare da ɗan kasuwa shi ne samun kyakkyawar mu’amala tsakaninshi da ɗan kasuwan. Ka da ka nuna ɓacin ranka ga kwastoma, ka da kayi wani abu da zai sosa zuciyarsa domin shi kwastoma kullum janyo shi ake a jika.

4. Tallata kaya da kasuwa
Duk bunƙasar kamfanin Facebook, ko Dangote Group har yanzu ba a daina yi musu talla ba. kusan kullum sai ka ga ana tallan kamfanin MTN ko Airtel. Haka nan kake ganin ana tallata manyan kamfanoni da gidajen jaridu da bankuna. Ba don komai ba sai don ƙara jaddada wa kwastomomi da ma sauran al’umma cewa wannan kamfanin yana nan akan bakarsa ta biya wa kwastomominsa bukƙatunsu. Har yanzu suna amfani da wasu kamfanoni domin tallata nasu don ƙara bunƙasa. Ke nan, kai ma ba tsayawa za ka yi ba, tallata kayanka za kayi da kamfaninka ko kasuwarka a wasu kamfanoni domin kai ma ka ƙara shiga kasuwa.

5. Zamanantar da kasuwanci
Kada ka kasance irin ‘yan kasuwan da ake ƙira “drone entrepreneurs” – waɗanda ba sa buƙatar wani cigaba na zamani a cikin harkokin kasuwancinsu. Wataƙila hakan yana da nasaba da rashin wayewar zamani da fa’idodin haɓɓaka kasuwanci a zamanance. Amma kai da kake harkokin yau da kullum ya kamata ka ɗauki wasu muhimman matakai da hanyoyin da za ka bunƙasa kasuwancinka a zamanance. Misali dandulan sada zumunta na yanar gizo, cinikiyya a yanar gizo, karɓan kuɗaɗen lantarki, kasuwancin gida-da-waje na yanar gizo, da dai sauransu. Ya kamata ka yi duba da waɗanan hanyoyi da ma wasu da za ka iya zamanantar da kasuwancinka domin yanzu, ba kai kaɗai ba, manyan kamfanoni sun fi mu’amala da kwastomominsu da waɗannan hanyoyin.

6. Haɗin gwiwa
Ka nemi haɗin gwiwa da wasu kamfanoni don bunƙasa naka. Misali wasu kamfanonin da suke sama da naka da kuma waɗanda kuke kamanceceniya, zai fi kyau idan ku ka yi haɗin gwiwa don shigar da naka kasuwa. Amma mafi yawan lokuta wasu ba sa yarda a haɗa gwiwa da kamfanoninsu don wani ya tashi, idan hakan ta faru da kai ka share wannan kayi sha’anin gabanka kawai.

7. Neman shawara
Abu na ƙarshe shi ne neman shawarar masana, ƙwararru ko kuma ma’abota harkar da kake yi, bugu da ƙari kuma kula da buƙatun kwastomomi ta hanyar ji daga bakinsu akan abunda suke da ra’ayi. Kasuwancinka ba ra’ayinka ko abunda kake so za ka sayar ba, abunda kwastoma yake so ne.

Rubutawa: Mohiddeen Ahmad

#ZoMuGinaKamfani

Post a Comment

0 Comments