A darusan mu na baya mun yi darasi akan istimina. Kama daga ma'anar sa, zantukan Malamai na addinin musulunci. Alfanu da kuma rashin alfanunsa. A wannan darasin zamu kawo hanyoyin da mutum zai bi domin daina istimina idan yana son dainawa.
A cikin abubuwan da muka kawo da suke jawo istimina da akwai yawan Sha'awa. Shi sha'awa kamar yadda muka fada a baya halitta ne. Duk Dan Adam yana da sha'awa dai dai nasa, duk kuwa da ana samun wasu da basu da shi saboda wasu dalilai da sai an gano.
Da yake sha'awa halitta ne, kunga kenan abune mai matukar wuya ace mutum ya hana kansa yin sha'awa. Ko ya rage ko kuma ace yama kawar gaba daya daga jikinsa. Wannan ba abu bane mai yiwu amma da akwai abubuwan da sune suke motsawa mutum sha'awa har ma yake son ganin ya kauda wannan sha'awar ta hanyar istimina. Ga duk wanda yake son ya daina Istimina abu na farko da zai soma yi shine ya guji duk wani abu da zai motsa masa sha'awar sa.
Da akwai wasu abubuwan dake motsawa mutum sha'awa kamar haka:
1: Zance-Akwai wasu kalamai ko zantuka na musamman da Idan mutum na jinsu sha'awar sa na iya motsawa.
Idan mace tana jin hira daga namiji musamman zatuka ko kalamai na batsa nan take tana iya kamuwa da sha'awa. Haka shima namiji idan yana sauraron irin wadannan zantukan daga wajen mace zai motsa masa sha'awa.
Don haka duk mai son ya daina Istimina to ya kaucewa sauraren hira, zantukan ko duk wani sautin da kan iya motsa masa sha'awa.
11: Kalle Kalle- Kallon fina finan batsa da kuma fina finan da suke dauke da soyayya suna iya motsawa mutum sha'awa. Don haka duk mai son ganin ya rabu da istimina to ya kasance ya kauracewa kallon irin wadannan fina finan.
Haka ma yawan kallon mata ga maza, ko kallon maza ga mata yana iya motsawa mai karfin sha'awa, sha'awar su.
Wasu mazan irin shigar da mata suke yi wanda yake bayyana surarsu yakan motsasu. Ita kuwa mace kwalliyar namijin daya kwanta mata a rai kawai ya isa ya motsa mata sha'awar ta.
Don haka duk masu son ganin sun kauracewa istimina dole ne su kiyaye wannan.
111: Hotuna- Akwai hotunan tsairaici da dole mai son daina Istimina ya kauracewa kallon su.
Wasu maza ko zane suka kalla bama hoto ba sai sun motsa. Wasu matan ma haka.
Wadannan sune wasu hanyoyin da suke motsawa mutum sha'awa. Wadanda dole sai mai son daina Istimina ya ki yaye su kamin zai cimma burinsa.
Hanya na gaba a kokarin ku na ganin kun rabu da istimina shine kadaici.
Ta yaya kadaici ke haifar da istimina?
Mu hadu a darasi na gaba.
0 Comments