Wasu 'yan mata suna rasa samarinsu ne a lokacin da suke soyayya dasu akan wani dan kuskure kadan da suka musu.
A wani lokacin sai dai kawai suga samarin nasu sun daina zuwa ba tare da sanin dalili ba. Wasu lokutan kuma sukan sanar dasu amma a kurenren lokaci.
Ga wasu kurakuren da yawancin 'yan mata suke yi a lokacin da suke soyayya da masu nemansu da aure:
1: Rashin Iya Magana:
Magana shine tushen sa namiji ko mutum yaji yana kaunar mutum ko kuma ya tsaneshi.
Ana samun wasu 'yan matan da sam basu iya magana ba. Duk kalmar da zata fito daga bakinsu furtata suke ba tare da sun aunata ba.
Duk macen da take gudun koran mazan da suka zo nemanta da aure, dole ne ta yi kokarin iya magana. Idan kuwa ba haka ba zata wayi gari taga babu wani namijin dake kulata. Kuma ko aurenta aka yi da yiwuwar a korota saboda kalamanta.
2: Roko-:
Akwai matan da suka kwarai wajen rokon samari kudi ko wasu bukatu. Wannan kuskure ne da zai iya koran namijin da yake son aurenki. Sannan kuma zubda mutunci ne.
Tabbas yau da kullum ya wuce wasa, akwai lokacinda zaki shiga wata matsalar da kike son saurayinki ya taimaka miki, a irin wannan yanayin dole ne ki hada da hikima da dabarun da ba zai fahimci kai tsaye roko kike masa ba ko kin dogara akansa a wannan bukatar taki.
Yawan roko wajen mace bayaga zubar mata da mutunci da yake yi, yakan cusa shakku a zuciyar mai sonki na rashin tabbas na shi kike so ko abun hannunsa, wanda hakan zai sa ya sake tunani ko niyar da yake da shi akanki.
3: Saurin Fushi-:
Wasu 'yan matan sukan dauka cewa idan suna nunawa maneminsu fushinsu akai akai wannan zai sa ya kara sonta. Abun ba haka yake ba. Saurin nunawa namiji fushi yana koran namiji ne amma ba jawoshi kusa ba.
Duk namiji yana fatane da burin auren macen data fishi hakuri, don haka da zaran yaga macen da yake son ya aura tanada zafi da saurin fushi, gaba yake karawa ba tare da yayi sallama ba.
4: Tara Samari-:
Wasu 'yan matan sukan dauka cewa tara samari da yawa tamkar wani abun burgewa ne. Wasu ma dauka suke cewa sunada farin jini ne. Amma a mahanga na maza masu hankali, suna ganin duk wata budurwa da take tara samari mayaudariyace. Kuma da yiwuwar mazinaciya ce ba auren a gabanta ba. Don haka duk wanda yazo mata da maganar aure zai hakura ne da zaran ya fahimci hakan. Daga karshe za a barta da tarin masoya amma ba manema ba.
Don haka duk budurwar da take burin ganin bata kori mai sonta da aure ba, ta kasance ba mai yawan tara samari ba.
5:Zafin kishi-:
Nunawa namiji zafin kishi a lokacin soyayya yana iya koran namiji.
Wasu matan suna dauka cewa, hanyar da zasu nunawa namiji suna sonsa shine ta hanyar nuna masa zafin kishin da suke da shi akansa.
Tabbas nunawa namiji kina da kishi abune mai kyau. Amma tsananta kishin kuma na iya koran miki saurayi kamin ki ankara. Don haka sai ki kula da irin kishin da zaki nunawa namiji da kuma inda ya dace ki nuna masa, akan kuma wacce ya dace idan ba haka ba zaki yi biyu babu.
Wadannan wasu kananan kurakure ne da akasarin 'yan mata suke tafkawa a bisa rashin sani. Da fatan za a gyara.
0 Comments