MAGANIN BASUR IRIN NA KASASHEN LARABAWA :


TAMBAYA TA 2790
*******************
Assalam alaikum...
Malam barka da wannan lokaci...malam don Allah ina neman temakon maganin basur..

Wallahi ina fama dashi sosai kuma bana Nigeria ina Masar (Egypt) wannan yasa yawancin magungunan da nake gani duka bamu da mahadansu a nan kusa, anyi min aiki amma sbd akoi bayan gida me tauri to basir din yasake dawowa.

To dan Allah malam idan akoi wani maganin wanda Allah ya sanar daku, kuma akan iya samunsa anan qasashen larabawa ina roqonku da ku sanar dani dan Allah....

Allah yaqara lpy albarkacin manzon Allah (SAW) Yasa agama da duniya lpy

AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Malam Abdullahi akwai nau'o'in maganin basur wadanda zaka iya samunsu cikin sauki anan inda kake, kuma in sha Allahu suna da amfani sosai wajen magance chutar basur kala-kala. 

Misali idan basu din naka mai tsiro ne, ka nemi danyar tafarnuwa (1 bulb) ka dakata gaba daya, sai tayi laushi sosai, ka kawo cokali biyu (babban cokali) na man kwakwa (Coconut oil) ka chakudasu tare, sannan ka rika liqawa awajen tsiron basur din yayin da zaka kwanta barci. 

Bayan minti biyar ko goma sai ka wankeshi. In sha Allahu basur din zai motse, kuma ba zai sake fitowa ba. 

2. Ka nemi man kwakwa din mai kyau, ka rika shan cokali guda, minti 15 kafin kowanne cin abinci. Wato kafin karyawar safe (breakfast) da kuma kafin abincin rana, da kuma kafin cin abincin dare. To in sha Allahu wannan zai warkar maka da basur din dake cikin hanjinka, kuma zai hana ba-hayarka yin taurin dake wahaltar dakai. 

Sannan ka nemi auduga (Cotton) kana dangwalar man kwakwar ajikinsa, sannan ka sanya a wajen da basur din yake, zaka barshi awajen har tsawon daqiqah goma (10 seconds). Zaka maimaita haka kamar sau uku a kullum. To in sha Allahu koda jijyar basur ya kwantar da mutum, zai tashi da izinin Allah. 

3. Kitsen shanu : Kitsen shanu yana maganin ciwon basur mai tsiro. Ka wanke duburarka da ruwan zafi, ka wanke sosai ka tabbatar wajen ya wanku, sannan ka shafe wajen da narkakken kitsen saniya. Zaka maimaita haka har sau uku a kullum. In sha Allahu zaka rabu da basur mai tsiro, har abada. 

4. Ka nemi ganyen na'a-na'a ka rika yin shayi dashi, kana sanya cikin karamin cokali guda na man kwakwa acikin shayin sannan kasha, safe da yamma. Shima yana kashe basur na cikin ciki in sha Allahu. 

Daga karshe ina yi maka fatan dukkan alkhairi, Allah shi baka lafiya, tare da sauran majinyatanmu damu baki daya. 

Post a Comment

0 Comments