Idan Kina Son Namiji Yayi Kewarki:



 
Suma mata yana da kyau suyi amfani da dabarun da zasu rika saka samarinsu dake sonsu da aure kewa. Ba wai kawai shi namiji ne kadai zai cusa miki kaunarsa ke kuma baki da hanyar sa shi ya soki.
Ga wasu dabarun da duk budurwa zata rika sa mai sonta kewarta.
 
Idan kina son namiji ya rika kewarki kada ki zamemasa mace mai arha. A duk lokacinda yake son ganinki ya ganki.
Dole ne ki rika takaita yawan baiwa mai sonki lokaci domin rashin samun lokacinki a yadda yake so ne zai sa kiyi daraja a wurinsa kuma ya rika doki da kewarki.
Wasu lokacin ki nuna masa aiyuka ne na gida a gabanki koda kuwa baki aikin komai. Wani lokacin kuma ki nuna masa baza a barki ki fito ba. Wasu lokutan kuma nuna masa karatu kike tare da bashi hakuri da sabon lokacin da zaku sake haduwa.
 
Duk lokacin da kuka hadu da mai sonki ki tabbatar masa babu namijinki da kike so a duniya sai shi. Ki nuna masa idan dai maganar soyaya ne babu wani namiji da yake so sai shi.
Hakan zai rika tabbatar masa da cewa baki takaita kanki a wajensa bane saboda bakison shi. 
 
Idan kina son ki rika sa mai sonki kewa da kuma ganin da daraja ki takaita yawan daukan wayarsa, yi masa reply a lokacin da yake so. Da kuma doguwar hira da shi a waya.
Idan saurayinki ya kiraki to ki dan bada lokaci kamin ki kira shi ko sai ya sake kiranki sannan ki dauka 
Haka kuma ko sako ya turo miki manta da sakon zuwa wani dan lokaci kamin ki bashi amsa cikin girmamawa da kuma mutuntawa.
Haka idan ya kira waya kada ki bari ya jaki da hira har sai zancen da yake son yi miki ya gaba. Bar shi sai ya gangaro a bayanin nasa sai kice masa yayi hakuri zaku ci gaba da maganar koda kuwa maganar da yake miki tana miki dadin ji fiye da shi mai baki labarin
 
Idan kin tashi kiran saurayinki a waya kada ki bar shi ya fahimci wani lokaci na musamman da kike kiranshi. Ya zamanto a kowani lokaci kina iya kiranshi a lokacin da baya zato. Kuma kada ya zama kina kiransa fiye da sau daya a rana, wata ranar ma shareshi kawai kamar kin manta da shi.
Idan kika tashi tura masa sakon text kada ki rika tura masa doguwan hira ko labari. Yi masa gaisuwa ko bayani a taikace yadda zai so ya samu karin bayani.
Muddin zaki kula da wadannan dabarun, zaki yi mutunci a wajen maisonki da aure, kuma a kullum zai rika kewarki.

Idan kina son namiji yayi kewarki ki samu wani lokaci kina likes na post dinsa ko yin koment. Wani lokacin ma ki tura masa sako a inbox dinsa musamman idan yayi abunda ya burgeki.
Can kuma kawai sai ki dauke wuta duk abunda zai yi posting ko zai fada kama tagging zai miki kada ki ce komai kaman baki gani ba.
Wannan yakan jawowa mace kima da cusawa namiji kokarin ganin kada ta kubuce. Don haka a kullum zai yita kewarta.
Wani lokacin dif zaki yiwa saurayinki ya kasa samun ki a waya ko kuma ganinki. 
 
Ita mace tana kara daraja ne a wajen namiji gwargwadon karancin da take masa. Idan mace ta zama available awajen namiji ba zata yi darajar da ya kamata tayi ba.
Sai dai wannan ba yana nufin cewa mace zata kauracewa mai sonta bane har yadda zai ga tamkar bata son sa ne.
A zahiri da kuma badini ya tabbatar kina sonsa. Amma ki zama baki bada kanki arha yadda zai ji tamkar shi yake da Iko dake kamar matarsa.
Dole ne ki rika cusa masa shakku a ransa na kina sonsa ne ko baki sonsa. Tare kuma da nuna masa cewa har yanzu fa yana da sauran aiki a gabansa muddin yana so ya rika ganinki yadda yake so a lokacin da yake so.
A kewa, shi namiji yana kokarin kara kusanci da mace ne. Ita kuma mace idan tana son namiji yayi kewar ta zata rika masa rowan kanta ce. A haka sai kuka kowa yana dokin kowa, kowa yana marmarin ayi aure. 
Da fatan samari da yan mata sun fahimci wannan karatun.
#TsangayarMalam
#sirrinrikemiji  

Post a Comment

0 Comments