Sau tari wasu idan zasu yi aure hankalinsu na komawa ne akan wasu halitttu dake burgesu daga halittar wanda zasu aura. Don haka basu damu da su kula da dabi'u ko halayen wanfa suke son aure ba.
Duk da yake halin mutum na gaskiya baya bayyana ne sai bayan da aka yi aure, zama yayi zama, aka shiga lokacin jarabawa na rashi da babu. Lafiya da rashinta, a wannan lokacin ne mutum zai iya fahimtar ainihin wanda suke zaman auren da su.
Ga wasu halayen macen da aka yi dacen aurenta idan tanada wadannan halayen kamar haka:
1: Mace Mara Mita- Yawan mita da tashin tashina wajen macen da ake aure ba karamin masifa da bala'i bane wajen mai aurenta. Don haka duk namijin da yayi sa'ar macen da batada mita tabbas yayi dacen samun mata.
2: Mara Gori- akwai wasu matan masu son taimakawa miji na wasu fannoni rayuwar iyali, kama ga abinci ko kudin makarantar yara koma taimakawa mijin shi kansa da wani abun. Amma suna yi zasu soma gorantawa da zaran zance ya taso ko kuma an samu wani sabani zasu soma ihun abubuwan da suka yi.
Don haka duk namijin daya yi dacen auren macen da batada hali na gorantawa a rayuwa tabbas yayi dacen aure.
3: Bata Hana Miji Yin Alheri- Akwai matan da babu abun da suka tsana a duniya irin suga mazansu na yiwa wasu alheri. Irin wadannan matan da zaran sunji miji zai yi abun kwarai burinsu kawai su lalata ko kuma suyi ta murtuke fuska. Musamman idan kyautan ko alherin da za ayi ba nasu bane zai mora ba.
Duk namijin da ya samu matar dake karfafa masa yiwa wasu abun alheri tabbas yayi dacen aure.
4: Macen Da Bata Tozarta Miji- Wasu matan sunada son ganin sun tozarta miji a gaban idanuwansa ko a bayansa. A gaban wasu mutanen ko a gaban 'ya'yansu. Irin wadannan matan basu ganin darajar miji sam wajen kalamansu idan zasu yiwa miji.
Don haka idan Allah Yasa namiji yayi dacen samun mace mai mutuntashi a gaban idanuwansa ko a bayansa, tabbas yayi dace aure.
Allah ka hadamu da Alkhairinka Aameen ya Hayyu ya Qayyum
0 Comments