MAZAJE KU NEMI ILMIN ZAMANTAKEWAR AURE...:


TAYA NI, MU GYARA...
MAZAJE KU NEMI ILMIN ZAMANTAKEWAR AURE...

Da yawa yawan Mazaje yanzu wallahi basu cancanci a basu Aure ba, wasu da ka Kurum babu bincike sai a dauki Mace a basu wadda watakila da an tsananta bincike kila ko Iyayen ta basa son ta baza su bashi Auren ta ba. Shikenan da Mutum yazo ya sha Riga da sitati, ya rike mukullin Mota, ya ciko aljihun sa da bugun Habuja, ko yace a wuri kaza yake aiki, ko a wuri kaza yake Kasuwanci, ko yayi karyar Dan Kwangila ne shi, sai kurum a dauki Mace a bashi.

Wata sa'ar kuma Matan ne kamar nanikawa kansu Namiji suke yi, kaji Mace tana cewa ita Allah Allah take yi tayi Aure, ko tace ita fa ji take yi kamar ta kai kan ta gidan Miji, ko kaji wata tana cewa ita koda za'a Aure ta kwana ɗaya a sako ta tana so, kaico! Ya IlaHi Idan Namiji ya san Mace neman kai take yi da kan ka yaya kake zato idan ya Aure ta, musamman idan aka gamu da marar tsoron Allah da rashin sanin darajar Aure. Ga Waliyyai da Wakilai sun koma kamar Dillalai, Dillalai mana, to Dillali ne idan ya hada ciniki daga ya karbe laadar sa shikenan. Wanene ya sayi Gidan ko wanene ya siyar ko wanene zai zauna a Gidan bai shalle shi ba, to haka Aure ya koma yanzu, kawai Waliyyi ko Wakili zai tsaya a Daura Aure ne, daga an daura shikenan shi ya gama aikin sa, yaya zaman Auren zai kasance wannan ba damuwar sa bane.

Shi yasa yanzu daga anyi Aure sai kaji ance an yi saki, to Mazaje ne wadanda basu san darajar Aure ba, Marasa tsoron Allah ake basu Auren. Wani Ango don kurum Amaryar sa tace dashi Gas ya kare yace ta tafi Gidan Uban ta, don Allah wa yake so ta fadawa Gas ya kare. Ga Iyaye da su kan su Matan suna zubar da kimar su da darajar su. Wai har ta kai ga yanzu Ango ne ke zabar wurin da za'a daura masa Aure. Sai kaga Gidan su Amarya yana Unguwar Madabo ko Jakara, nan Ango yaje zance, nan Iyayen sa suka kai kuɗin Aure da kuɗin sa rana dasu Kayan Lefe amma Anzo Daurin Aure yace shi sai dai aje Masallacin Alfurkan ko Umar Bin Khattab ko BUK, wai Mutanen sa da zasu so kada su sha wahalar zuwa wurin Daurin Auren, kuma kaga Iyaye saboda Kurum suna so a Auri Yar su, sun amince da hakan. Yaushe za'a yiwa Mutumin da irin wannan?. Matukar Ango a rashin farko zai fara cewa ga yadda yake so kuma Iyayen Amarya su yadda koda kuwa sun cutu to fa sun siyawa Yar su rashin mutunci tun daga nan.

Kwanakin baya wani Ɗan Gidan hamshakin Mai Kudi yaga Yar wani Bafulatani yana so wai da aka zo batun kai Dukiyar Aure sai Dangin Angon suka ce wai su baza su iya zuwa Garin da Iyayen Macen suke ba, wai Idan suna da Yan Uwa a cikin Birnin Kano sai suzo nan a haɗu a karbi kudin a nan, shi kuwa Uban Yarinyar yace idan har Dangin shi Manemin Yar tasa baza su iya zuwa Garin da yake ba to a hakura. Tilas Iyaye Manemin suka tashi suka je din, to kaga wannan da ace ya yadda da tsarin da suka zo masa dashi yaya kake tsammanin idan an samu matsala Amarya tayi yaji Angon zai je biko ai sai dai su Iyayen Amaryar suzo biko kenan. Da yawa Iyaye sune ke zubar da kimar su, su zubar da darajar Yar su shi yasa Mazajen yanzu suke wulakanta su, su wulakanta Ya'yan nasu. Wai Uba ne yake karɓar rancen kudi a wajen Mijin Yar sa, Don Allah yaya bazai raina ka ba.

Ga wasu Mazajen basa ganin darajar Iyayen su da suka haife su bare su ga darajar Iyayen Matar su. Wai kaji Uba yana cewa shi ma idan yace da Dan sa yazo ba zuwa zai yi ba. Wai Miji ne aka samu sabani ya kora Matar sa gida bayan Iyayen ta sun yi sun yi yazo ya ki, Uban ta yazo wurin nasa Uban ya nemi ya kira Ɗan nasa don aji me ya faru amma sai Uban nasa yake cewa shi ma idan yace yazo ba zuwa zai yi ba. Haka aka yi ta kiran Angon nan da wayar Uban sa amma yaki dagawa daga baya ma sai ya kashe wayar. Don Allah wanda bai mutunta nasa Uban ba ta yaya zaka yi tsammanin zai mutunta Uban Matar sa. Yanzu irin wadannan Mazajen sai ace sun cancanci a basu Aure?

Sannan da yawa yawan su basu ma san wanne nauyi Allah ya dora musu ba na kula da Iyalan su. Wani kawai abinda ya sani Kurum ya Auro Mace ya ajiye ta shikenan tazo yi masa Bauta, babu batun shi ya kyautata mata. Kaji Miji yana cewa da Matar sa ni fa taimaka miki nayi na Aure ki. Ko kaji yana cewa idan fa na sake ki inda zaki kwanta sai ya gagare ki ko sai Abinci ya gagare ki ci. To ita da Iyayen ta sun zubar da kimar su a wurin sa, baya ko ganin su da gashi. Wani Miji wai Unguwa idan zai kai Matar sa a Lifan din sa sai ta zuba masa mai sannan zai Kai ta. Nace Allah yasa su ma Yan Matan da yake goyawa a Mashin din nasa su ma suna biyan sa kuɗin man.

Shi yasa idan naga Mace tana matsawa Namiji ya fito ya Aure ta nake tausaya mata domin wallahi ba duka Maza ne yanzu Yan halak ba. Da yawa Mazajen yanzu sun fi wulakanta Macen da ita take son su ba sune suke son ta ba. Wata sai kaga taki Wanda yake son ta, ta Auri wanda ita take son sa a karshe kuma tazo tana da ta sani. Wallahi Iyaye ku rika tsananta bincike akan wanda yazo neman Auren Yar ku. Ku ma Mata ku guji yin zaɓen tumun dare, ku guji biyewa son zuciyar ku, ku rika baiwa Allah zabi, zabin Allah ya fi. Kuma ku rika yin addu'ar Allah ya haɗa ku da me tsoron Allah, sannan kuma ku zama masu tsoron Allah ɗin. In sha Allah zaku dace.

Mazaje ku tashi ku nemi ilmin Zamantakewar Aure domin a gaskiya yanzu da yawa Maza da ka su ke shiga sabgar Aure. Wai kaga Namiji yayi tambari akan Auri-Saki amma kuma kaga ana ta bashi wasu yana Aura yana saki, kuma ana sake bashi wasu. Wani ance da Lefe daya sai ya Auri Mata uku, ya Auri wannan ya saki, ya karbe Lefen sa ya kaiwa wata, ita ma daga ya dandana ya sake ta, ya karbe Lefen ya sake kai wa wata. Nayi Addu'ar Allah ya gama shi da Mace Yar Ƙungiyar aci Lefe muga yadda zai yi.

Ni cewa nayi ko dai a rika yiwa wadanda za'a basu Aure bita ko kuma su ma yadda ake budewa Amare wuraren koyon zama da Miji to su ma a budewa Mazan wuraren da za'a rika koya musu yadda Zamantakewar Aure take. Allah yasa mu gane, mu kuma gyara. Ameen!

Salisu Abdul

Post a Comment

0 Comments