LITTAFIN FIQHU DARASI 33



KARATUN FATIHA

Kamar yadda muka ce, du’a’ul is’tif’tah da ta’awizi a ɓoye ake yin su, amma idan karatu a ɓoye ake yi, a ɓoye za a karanta Basmala. Idan kuma karatun a bayyane ake yi za a bayyana karatun Basmala saboda hadisan da Ibn Kasir ya kawo da suke nuna halaccin ɓoyewa, da kuma bayyanawa, inda mai sallah zai ce: Bismillahir Rahmanir Rahim, sai ya fara karatun Fatiha. Karatun Fatiha rukuni ne a cikin sallah domin malamai sun ce karatun Fatiha farilla ne haka tsayuwa domin karatun Fatiha shi ma farilla ne. Akwai kura-kurai da ake samu wajen karatun Fatiha, wajibi musulmi ya je a koya. masa Karatun Fatiha, a gyara masa kurakurai da ake samu a wajan Karatun Fatiha. 
Dole mai yin sallah shi kaɗai ya karanta Fatiha. Idan liman ya karanta Fatiha, mamu ma sai ya karanta Fatiha, idan liman a ɓoye yake karatun. Idan liman a fili yake karatun, mamu za su saurara ba sai sun yi karatun Fatiha ba. Idan ba a jin karatun liman, sai mamu su karanta Fatiha.

Wasu malaman sun ce idan liman ya gama karatun Fatiha ya ɗan yi shiru, shi ma mamu sai ya yi sauri ya karanta don ya sami damar yin karatun. Sai dai wannan ba wajibi ba ne, saboda hadisin da ya ce: “Idan mutum yana bin liman, karatun liman shi ne karatu a wajensa,” duk da saɓanin malamai game da wannan hadisin. Ana kafa hujja da hadisin Abi Bakarata da ya zo masallaci an yi ruku’i sai ya yi sauri ya bi ruku’in. Annabi ﷺ ya gama sai ya gaya masa, “Allah ﷻ Ya ƙara maka kwaɗayi, amma kar ka ƙara.” Malamai suka ce a nan bai karanta Fatiha a wannan raka’a ba kuma bai yi tsayuwa domin karatun Fatiha ba. Da karatun Fatiha wajibi ne a kan mamu da sai a ce masa wannan raka’a ba ta yi ba, domin ba a yi karatun Fatiha a wannan raka’a ba. Wasu kuma suka ce idan ya riski muhallin Fatiha dole ne ya yi, amma idan bai riska ba to liman ya ɗauke masa ba sai ya sake karanta Fatiha ba. Idan liman ya yi ruku’u, mamu zai yanke karatun Fatiha, ya bi shi koda bai gama Fatiha ba.

Idan an gama karatun Fatiha, sai liman ya ce waladdalin mamu kuma su ce, ameen. Faɗin ameen yana da matuƙar muhimanci saboda Annabi ﷺ ya ce, “Idan liman ya ce ameen, kuma ku ce ameen, domin duk wanda ameen ɗinsa ta dace da ta mala’iku za a gafarta masa kurakuransa da suka gabata.” Wata ruwaya ta ce, mu jira idan ya ce, Waladallin sai mu ce ameen. 
Bayan karatun Fatiha da cewa ameen, abin da ya rage shi ne liman ya karanta abin da ya sawwaƙa na Alqur’ani musamman a raka’o’i biyun farko na Asuba da Juma’a da Azahar da La’asar da Magariba da Isha’i. A waɗannan salloli ana karanta Fatiha da sura a raka’o’i biyun farko, amma biyun ƙarshe na Azahar da La’asar da ɗayar ƙarshe ta Magariba da biyun ƙarshe na Isha’i duk ana yin karatunsu a ɓoye ne. Haka kuma, ana iya tsawaitawa ko kuma a taƙaita a raka’o’i biyun farko saboda hadisin Abu Katada (رضي الله عنه) wanda ya ce Manzon Allah ﷺ ya kasance yana karatun Fatiha da sura a raka’o’i biyun farko, yana tsawaitawa a ta farko kuma ya taƙaita a ta biyu, kuma wani lokaci yakan jiyar da aya domin mu ji abin da ake yi.
Yanayin karatu a raka’o’i biyun farko na sallar Azahar, Fatiha da Surah, raka’ar farko yana tsayawa gwargwadon Suratus Sajadah, ta biyu kuma gwargwadon rabin Suratus Sajadah.
Kuma mutum zai iya karanta Fatiha da aya ɗaya tak, saboda Annabi ﷺ ya ta ɓa yin sallah yana maimaita aya ɗaya.

Post a Comment

0 Comments