LARURAR AMAI DA GUDAWA [CHOLERA]




•••••••••••••••••▪︎○○●○○▪︎••••••••••••••••••

Kwai bayanai dake nuni da bullar annobar Amai da zawo a wadu yankunan Arewacin Nijeriya wanda dama galibi hakan yafi afkuwa lokacin damuna, ina fatan wannan bayanin zai amfanar musamman duba da yadda zan fadi magunguna cikin bayanin.

Amai da gudawa na kwalera na daga larurar dake kisan farat daya domin inta afku duk jinkirin sekons guda na agogo kara tsanantar jigatar wanda ke fama da larurar ne. Za'aga mutum na tsilla zawo akai akai ta yadda har sautin fitarsa anaji.

••••••••••••••••▪︎○○00○○▪︎•••••••••••••••••

ABINDA KE JAWO CIWON KWALERA

Ciwon na faruwane dalilin ci ko shan gurbataccen ruwa ko abinci wanda suka riga suka gauraya da kwayar cutar ta bakteriya

□ Ko cin gurbataccen ďanyun kayan lambu da suka gauraya da najasar wanda ya kamu da ciwon, ko 

□ Shan ruwan rafi, ko ruwan rijiyar da ruwan sama ya koro najasa ta shiga ciki (rijiya kusa da bola/juji, ko shadda), ko rijiyar wajen gari da ake shan ruwa ko debo ruwa ciki

□ Ko shan ruwan kududdufi wato ruwan da yake bame tafiya ba, ruwan rijiyar rafi musamman lokutan damina dama ko yaushe wanda wannan yasa ba'ason kashi ko fitsari agefen tituna ko cikin gonaki da mutanen mu galibi na karkara keyi. 

□ Hakama amfani kankara (ice block) wacce taxo daga ruwan pipe na famfon da ya gurbata, domin pipe din ta cikin nazasa yake a binne inya jima yana iya tsatsa ya huje.

□ Haka ma abin ka iya faruwa dalilin shakar kwayoyin cutar cikin iska dalilin amai, gudawa da fitsarin masu ciwon kamar yadda yanzu ake fama. 

••••••••••••••••••▪︎○○0○○▪︎••••••••••••••••••

DALILI: 

Wadannan kwayoyin cuta ba abune da idon mu zai iya ganinsu ba kuru-kuru, Shiyasa cutar inta fantsama cikin mutane bakyau, lokaci guda daruruwa na iya kwanciya saboda kafin wani ya nuna alamu a sanar da wasu tuni saura sun kamu suma.

Ciwon Kwalara na karar da ruwan jiki tare da illata kodar mutum nan da nan, shiyasa ciwon ke kisa. Wannan kuma tasa in aka samu 6arkewar annobar abun bai 6oyuwa saida kowa yasan anshiga masifa. 

Saboda idan mutum 1 ya kamu dalilin fitsari, amai da kashinsa duk gidansu na iya kamuwa, in gidan suka kamu kazantarsu kudaje (flies) nahawa kai zasu iya yadasu gidajen makota nan da nan canma.sai aji ta harbu, kafinnkace me abu ya waďe gari.

••••••••••••••••••▪︎○○1○○▪︎••••••••••••••••••

ALAMOMIN CUTAR KWALERA

Alamun ba boyayyu bane sun hada da; 

▪︎Tashin zuciya da amai akai-akai
▪︎Gudawa haka ɓakatattan za'a
▪︎Yamushewar Fata da kasala
▪︎Bushewar baki, da makogoro
▪︎ Murdawar ciki da kuginsa
▪︎Yawan son shan ruwa, karancin fitsari
▪︎Bugawar zuciya far-far-far da sauri tare da ganin jiri wasu lokutan
▪︎Saukar karfin bugun jini (low BP)

Ba dole ne duk sai anji wadannan alamun ba, amma de fitattu dune amai da zawo da kasala.

••••••••••••••••••▪︎○○2○○▪︎••••••••••••••••••

MEKE JAWO MACE-MACE DALILIN CUTAR

Babban abunda ke kashe Mutane kamar yadda nace shine karancin ruwa ajika (Dehydration), bawai kwayar cutar ba, domin kana ta kwara amai tare da tsilla gudawa nan da nan electrolytes dinka su sodium, potassium, magnesium, calcium, da sauransu zasui kasa baki daya.

Electrolytes nayin kasa jini zai dena wadatar da jikinka baki daya za'a sami karancin iska acikin jini, wanda hakan zaisa duk sassan jikinka su Hanta, Huhu, zuciya, Koda da kwakwalwa su fara shut down kamar yadda laptop ke kashe kanta.

Farkon organ din da zai ta6u itace Kidney domin kunsan ita ke sarrafa magani, tace guba, abinci da dukkan datti ajika tare da saita wadancan electrolytes din, kunga tana tabuwa zai zamto ta kasa wancan aikin nata nan da nan jiki zai rikice.... kwakwalwa ko ana samun karancin iska na sama da minti 3 Brain cells zasu fara mutuwa...

Daga nan kwatsam sai aga babbar alamar mutuwa wato:
■ Canzawar kalar fata zuwa kalar blue-blue🟦 alamun karancin iska cikin jini sai mutuwa... Wannan tasa ake ma mutuwa dalilin kwalara lakabin "BLUE DEATH"

Shiyasa amai da zawo ba abune na juriya ko dauka da wasa ba komi kuruciyarka kuwa ajika, masifa ce da kisan baya kyau, da kaji gudawa hade da amai yi maza ka nufi asibiti ko wajen jami'in lafiya domin bakasan me zai biyo baya ba. 

Shi yasa zakuga mutum tun yana iya tashi yaje bandaki da kansa in abun yaci tira sai yakai ga kasa tashi, ko kuma inya mike ya rika tafiya daga-daga zai fadi ko yake faduwa saboda electrolytes yai depleating. Wani saide ma ya tare a bandaki aje daukosa domin bazai iya dawowa da kafarsa ba. 

••••••••••••••••••▪︎○○3○○▪︎••••••••••••••••••

WAYAFI HATSARIN KAMUWA

In annoba irin wannan ta shigo cikin al'umma babu wani wanda yafi karfin kamuwa da koea, tana iya shafar kowa duk lafiyarsa kuwa, saide akwai wanda tafi saurin halakasu kamar yadda muke gani: Yara, tsoffi, masu juna biyu da mutane masu wasu larurorin ajika da dama suke shan magani kullum-kullum

Wadannan rukunin mutane 4 din anfi samun mace-mace atsakaninsu musamman yara kanana da tsoffi. 

••••••••••••••••••▪︎○○4○○▪︎••••••••••••••••••

LALLAI AKAI KOKE GA HUKUMA [RISE ALARM]

A duk sanda aka sami mutum sama da 4 na fama da zazzabi, amai da gudawa da ake tunanin cholera ko shan wani abune, ai hanzarin sanar da jami'an lafiya inbabu asanarwa da sarki ko maiunguwar gari su kuma su sanar da ofishin kula da lafiya na karamar hukuma domin daukar matakin da ya dace. 

Situation ne da rasa rai ba wuya, kamar wasa zakaji ana wane ya mutu, wance ta mutu in akai sake. 

••••••••••••••••••▪︎○○5○○▪︎••••••••••••••••••

MAHIMMIN ABUN YI LOKACIN BARKEWAR AMAI DA ZAWO

Na sha fada cikin wasu rubututtukana cewa; musamman ga kananun ma'aikatan lafiya, tsayar da gudawar bashine mahimmin abunyi ba, Hasali yanzu standing order ba'a yadda kaba me gudawa maganin tsaida ita ba, yin hakan zakaiwa mutum illar da tafi ta ciwon.

Domin gudawa ai gubar da kwayar cutar ta zubane cikin hanjinsa ta sakar da jikin don haka wannan ruwan gudawar dake fita electrolytes ne hade da kwayoyin cutar, idan ka bada magani ka hana gudawar fita tofa mutuwa na iya biyo baya kwayoyin cutar zasu canza hanya su shiga jini kaga ai yafi illah  

Gishiri da sugar shine kurum abunda zakuita yi har akaraso asibiti asama karin ruwa. Katku damu ku barshi yaita gudawarsa. Amma kar kubasa komi naci ko sha sai ORS, koda antibiotics ko wani magani karku bashi sai anzo asibiti ko ankira likita gidan.

••••••••••••••••••▪︎○○6○○▪︎••••••••••••••••••

KAI TSAYE KAMAR YADDA KUKAJI

Tsaka da amai da gudawa din ai maza a nemo ruwan gishiri da sugar wato (ORS) ahada aba mutum yaita sha kafin akwasosa zuwa asibiti. Duk sanda yai amai ko gudawa toh adauki ruwan abasa, koda duk minti guda sai ya kwato aman ne, aita bashi koda gudawar ta tsaya.... har sai anfa alamun karfin jiki ya fara samuwa. 

Duk faket din ORS guda 1 za'a hadasa da ledar pure water 2 ko 3 idan ledar kanana ce. idan kuma babu purewater to a sami ruwa axuba a tukunya a tafasashi inyai zafi sai asauke abarsa ya huce sai asami kofin shan ruwa 4 ahada ledar ors din dashi aita baiwa mutum yana maida electrolytes din da ya rasa wannan shine mahimmi.

Kada a damu da gudawa bata tsaya ba, in toxins din sun gama fita zata tsaya don kanta kude karku yadda gudawar take shafar jikinku asami katon foo asawa mutum ko mutum in muta na iya tashi toh yai kusa da bandaki da ya fito asami ruwan omo ko toka akwara abandakin.

Idan babu ORS walau hali na rashin kudi ko kuma kila babu chemist kusa agari toh ahada ruwan gishiri da sugar din local na hannu ake baiwa mutum.

Yadda ake hadawa shine; asami cokalin madara irin wanda kuke gani a hoton kasa; bawai babban cokali irin na cin abincin Manya ba, a'a cokali na yara... bayan an tafasa ruwa awuta ansaukesa ya huce, sai ajuye a kwanon sha ko dogon kofi wanda yawan ruwan anaso yakai cikin kofin shan ruwa 5 wato LITER 1 ko babbar robar ruwan FARO, sai adauko wancan karamin cokalin 🥄(teaspoon) na yara a debi sikari cikin cokalin 6 [🥄🥄🥄🥄🥄🥄] 
Sannan kuma sai a debi gishiri rabin cokalin [½🥄] sai azuba... ajuya a karkada sai arika bawa mutum yana sha. Inya kare aka hada wani aita maimaitawa har sai gudawar ta tsaya don kanta.. Musamman idan asibiti yakai ga cika ba hali abunda za'aita yi kenan agida. Inda ORS kuma toh aita hadasa.

Kada kuji ina atafasa ruwa ku dauka dole ne, a'ah idan har angamsu da tsaftar ruwa shikenan basai an tafasa ba kafin ahada ORS din.

Ga kananun yaran da ake shayarwa nono in sun kamu a cigaba da shayar dasu akai akai domin kar suma su zamo dehydrated.

••••••••••••••••••▪︎○○7○○▪︎••••••••••••••••••

AI HANKALI DA WANNAN

Kada baiwa me amai da zawo komi inba ORS ba, hatta abinci ko farau-farau kar asha, abari duk ya kasayar da komi... ors kurum zai sha.

Sannan ga jami'an lfy da masu shan magani daka ma akwai wasu Magunguna antibiotics guda da kuma opiods lallai kada a kuskura aba mutane masu cholera su; wato ciprofloxacin, Bismuth subcylicinate, Limotil, da Loperamide wadannan magungunan na iya kaiwa ga illata kwakwalwa (enecphalopathy) ko ruguza kwayoyin jini (hemolysis).

Na fada kada abaiwa mai cholera Anti-diahorrea na tsaida gudawa ko na tsaida amai wato (anti-emetics).

••••••••••••••••••▪︎○○8○○▪︎••••••••••••••••••

IDAN TA KAMA DOLE SAI ANYI AMFANI DA MAGANI

Tunda muna hali na emergency zan kama sunan magani.

Akwai magani da ake kira ZINC SULFATE yana zuwa a tablets wato na kwaya duk daya a 20MG 

▪︎Ga Yara yan kasa da shekaru biyar (under 5yrs)masu gudawa su kadai aka yadda ai musu amfani da zinc. 

Yadda kuwa za'a bayar shine:

■ Yan kasa da watanni shida (6 months) ake 6alla kwayar zinc 1 ana basu rabi wato 10MG, in kuma me 5Mg ne sai ake basu kwaya biyu... Tunda yara basa iya hadiyar tablets sai adorasa acokali adiga ruwa akai har ya narke sai abaiwa yaro. Yana da zaqi don haka baza suqi sha ba. Koda gudawa ta tsaya sun sami lafiya aci gaba da basu kullum jar tsawon kwana 10 saboda gudun kuka juyowar ciwon don kwayoyin cutar inbasu gama macewa ba suna iya re-activating din kansu.

■ Daga yara yan wata 6 zuwa shekara 5 kuwa: abasu ZINC din me 20MG kwaya tak, sai acigaba da basu 1 kullum ko 20MG kullum har tsawon kwana 10 koda ta tsaya kuwa sun warke suma. Karde abada ya wuce haka. Sai acigaba da bada ORS.

[Idan gudawar nada ďoyi/wari sosai very frothy ana iya karawa da METRONIDAZOLE da akafi sani da FLAGYL a auna nauyin mutum ko yaron duk 1kg daya abada 50MG, kunga yaro me nauyin 10KG za'a basa 500MG na flagyl kenan arana, ya rage abashi 25G da safe, 250MG da yamma ko kuma abayar lokaci daya tak 500MG Kullum na tsawon kwana 3 ko 5

■ GA MANYA: kuwa wato Adult; Ana iya basu DOXYCYCLINE 300MG wato tunda yana zuwa 100MG sai asha kwaya 3 lokaci 1 shikenan. Inbabu ana iya amfani da AZITHROMYCIN 1GRAM wato 500MG kwaya 2 lokaci 1 shikenan.

Hakanan ana iya karawa Manya ma da FLAGYL amma kada ya wuce 2Gram wato 500MG kwaya hudu, 2 safe, 2 yamma tsawon kwana 3 kacal

■ Batun ORS koda mutum nada hawan jini zai iya sha duk da akan bukaci rage cin gishiri a masu shi saboda ayanzu rashin sha zaifi illar shan yawa. Aita shan ORS har sai gudawa ta tsaya.

■ Haka yayin da mutum yake kwance wajen kafafunsa sunfi bukatar matashi maimakon kansa, saboda daga kafafun saisa kwakwalwa tafi samun jini musamman idan akwai matsalar low Bp koda kuwa da igiyar karin ruwa ruwa mutum.

■ Daga nan sai ma'aikatan lafiya su mange sauran larurorin mutum, walau typhoid, malaria, karancin jini ko wasu alamomin.

••••••••••••••••••▪︎○○9○○▪︎••••••••••••••••••

MAHIMMAN MATAKAN KARIYA

■- Ai hakuri da zuwa gaida masu larurar amai da gudawa wannan shine babban matakin dakile yaduwa, musamman mutanen mu na karkara sai aga kamar rashin zuwan lefi ne A'a ai hakuri sai anshawo kan abun.

■- A lura afahimci ta inda ciwon ya samo asali domin baiwa Jami'an lafiya cikakken bayani insunzo tambayoyi.

■- Ake wanke hannu da kyau lafin ashiga da bayan fitowa bandaki, ai amfani da omo, sabilu ko tokah wajen wanke hannun. Kada kuma agama wsnke hannu ace za'a goge laima ajika ko towel, abar hannun ya bushe da kansa, kurum a yarfe a iska. 

■- Sannan a wanke kayan marmari su ganyayyaki da vegetables da kyau kafin ayanka. Ba laifi bane asa gishiri aruwan wankesu. 🍋🥕🥬🥒🍍🍌

■- A tabbatar an dumama kwanannen abinci, ko kuma wanda ya jima abude ake kokonton ingancinsa, Sannan ake dafa abinci ya dahu sosai, babu zancen wai dahuwar nan irin HALF DONE, kuskure ne domin akwai kwayoyin cutar da sai sunji wuta sosai 

■- Rukunin wadancan mutane 4 masu ciki, tsoffi da yara a kiyaye abunda za'a basu suci kosu shan har sai wanda aka tabbatar da ingancinsa hakanan akangesu ahanasu fita zarar akaji labarin bayyanar annoba irin wannan, banda cewa za'a gaida mara lafiya.

■- Mahauta masu saida nama da masu sana'ar sayar da kayan rafi "sea foods" irinsu kifi suma su lura da tsaftar guraren sana'oinsu sosai, ake samun musayar iska (ventilation) tare da lullube kayan da farar leda don kore kudaje.

■- Ake rife shadda, koda nu na kauyuka asami murfi adrna barinta bude kudaje na yawo abakinta, in suka dauko najasa nan zasu taho su sauka kan abincin mu.

■- Matasa adena kashi a hanyoyin ruwa ko gonaki, inta kama dole ake tafiya da abu ai rami in angama amaida kasa a binne.

■- Sannan asanar da wanda baisan wannan bayanin ba ya sani shima matakin kariya ne wato yada ilimi atsakanin juna.

Allah shi tsare mu amin.

☆☆☆
✍🏼
[Ibrahim Y. YUSUF]

Post a Comment

0 Comments