Akwai wasu abubuwa da suke canja soyayya bayan aure sai ka ga an sami canje-canje, da ana soyayya kamar a hadiya juna amma da zarar anyi aure bayan lokuta kadan sai ka ga soyayya ta canja. Akwai dalilai da suke kawo hakan gasu kamar haka:
1.Rashin yin aure dan Allah ko kuma an gina soyayya akan karya ko anyi aure dan samun wani abun duniya sai kuma aka rasa. Sai ka ga ana canjawa juna fuska.
2. Rashin abubuwa guda 5, akwai wasu abubuwa guda biyar sune manyan bukatu na dan-adam ba a dakin aure ba koda a gidan kurkuku yake yana bukatar abubuwa 5 a duk inda yake dole ne a samawa mace su in ko ta rasa su to baza ta iya zaman aure ba kuma yanzu soyayya zata canja zuwa mummunan yanayi. Gasu kamar haka:
-Samarwa mata da abunci
-Bata suttura
-Kula da lafiyar ta
-Bata tsaro
-Samarwa mata da mahalli.
Abunci, suttura, muhalli, tsaro da lafiya su zama dole a kulawa mace su da zarar an rasa su sai kaji ana kace nace tsakanin ango da amarya.
Masu iya magana suka ce abu uku basu haduwa a azauna lafiya, suka ce ango da amarya da kuma yunwa.
3. Gina aure akan sha’awa. Da zarar an gama rayuwar angwanci karsashin sha’awa ta gushe sai ka ga an canjawa juna fuska.
4. Wasu canje janje da suke shafar mace bayan tayi aure. wato kamar lokacin hailar mace kan jin dan damuwa da kunci, hakan kanshafi zamantaker aure.
(samunciki da goyo )suma kan takurawa mace ta ji damuwa har hakan ya shafi zamantakewar ta ta aure.
5. Rashin bawa samari da ‘yanmata cikakken bayani da sirrin rayuwar aure tunkafin suyi aure.
6. Rashin daukar aure amatsayin ibada.
7. Rashin kwanciyar hankali,imma daga ‘yan’uwan miji ,uwar miji.
Kasha 95% na matsalolin ma aurata bayan aure wadan nan matsalolin ne nasaba.
Taya za a magance su?
Kada ayi aure har sai an cika sharudan shari’ah kamar samun sana’a,iya samar da mahalli, abunci, suttura, lafiya, tsaro. Yin aure dan Allah da daukarsa a matsayin ibada kamar sallah, azumi. Bawai zaman hutuba dole ne a ware cibiya ta musamman mai wayarwa samari da ‘yanmata kai akan harkar zamantakewa akan hakkin ma’aurata da yadda zamantakewa take. Yana da kyau maza su san cewa mata masu ciki ko haila suna dan samun canji a jikin su dan haka ana hakuri da su a lolacin.
Wace ce Mace?
Mace dai ta kasance tamkar wani furen fulawa. Wanda idanun mutum suke sha’awar kallo a koda yaushe, ita fulawa ta kasance abu ce mai kamshi.
Haka bayan kyawun kallo, tana da bukatar kasancewa a cikin inuwa, domin idan aka sanya ta a rana za tayi yaushi. To tamkar haka mace kan kasance a wajen sanyaya zuciya, da sanya farin ciki a zuciyar abokin rayuwarta.
Wannan kuma tun ran gini tun ran zane, domin kuwa mace, tun tana ‘yar karamar yarinya ta kasance mai kokarin son yin hidima ga wani, domin hatta wasanta na yarinta ba ya wuce na kula da jaririyarta (‘yar baby), ta kara ce, ko ta roba. Tare kuma da son taya mahaifiyarta aikin gida. Kuma a gaba haka za ta kasance har bayan ta girma tayi aure inda take zama rumfa, kuma ta zama garkuwa ga dukkan mutanen gida ta hanyar sadaukar da rayuwarta domin ta faranta masu da haskaka masu hanyar rayuwa.
Wannan ya ta’allaka tun daga mijinta da ‘ya’yanta da dangin mijinta da makotansu. Za ta kasance cikin hidimarsu ta yadda takan kasance tamkar wata baiwa wadda ita ba ta ma san wani abu jin dadi ba. Haka za ta rika gudanar da hidima ga iyalinta, kowa ya riga ta kwantawa domin yin bacci, kuma ta riga kowa tashi don ta share masu fagen fara rayuwa a wannan sabuwar rana.
Da irin haka kuruciyarta za ta tafi cikin hidimar gyaran al’ummarta, kyawunta da kuruciyarta da karfinta da komi nata a hankali haka za su gushe amma ba ta damu ba, manufarta daya ce rak wato sanya wa kowa farin cikin rayuwa da mika su zuwa ga ingantacciyar rayuwa har su kai ga burinsu.
Mace duk a cikin wannan tashi fadin da take yi abu daya kawai take nema wato shi ne a nuna mata kauna da soyayya ta gaskiya ba tare da an ci amanarta ba ta kowace fuska.
Allah sarki, mace ke nan, baiwar Allah. Sai dai hakan yana gagara a wajen da yawan mu maza. Yayin da wasun mu suka dauke ta wata abu kawai ta biyan bukata, wacce ba ta da wani gata da daraja illa kawai ta biya wa mutane bukatunsu, ta gusar musu da sha’awarsu. Wannan ya yi kama da yadda aka dauki mace a zamanin jahiliya.
Yayin da su kuma Turawan yanzu suka dauki mace a matsayin wacce za ta kure kyawun fuskarta, ta bude adonta da wasu daga cikin ni’momin da Allah ya yi a gareta, kawai domin jama’a su gani su yi dariya, su ji dadi, akan haka suka mai da ita ‘yar aikin banki, ko kuma yar aikin shaguna, ko ‘yar fim. Koma mai watsa shirye-shirye a cikin tashoshin talabijin, ko ta watsa daddadar muryarta a cikin rediyo jama’a suna saurare. Ko ma ta koma wacce za a saka hotunanta a cikin abubuwan sayarwa, ta rika kwaye tsiraicinta tana fitinar al’umma da kyawun surarta, tana sayen fushin Allah ga kanta da sauran mutanen duniya.
Su manufarsu kawai ita ce, domin ta janyo musu kasuwa ga abin da suke sayarwa, ita kuma ta nemarwa kanta mummunan karshe tun a nan duniya. Wacce za ta hadu da azabar Allah a gobe kiyama, ta kasance daga cikin makamashin Wuta. Allah ya tsaremu.
Yayin da shi kuma addinin gaskiya na Musulunci tun farkon zuwansa ya karrama ta, ya ‘yantar da ita, ya ba ta hakkinta tamkar namiji wajen samun sakamako a kan wahalhalunta tun ma a nan duniya.
Mata ku gode wa Allah a kan zuwan addinin Musulunci, kuma ku gode wa Allah idan har ya hallicce ku Musulmai, ku bi Allah, ku bi sunnar Annabinsa, ku yi koyi da iyayen Muminai domin ku shimfida rayuwa ingantacciya. Kuma ku samar da ‘ya’ya na gari, ku ba su tarbiya ta gari, a karshe su zama jama’a ta gari, a samu shuwagabbani na gari da ma’aikata na gari, ko ‘yan kasuwa na gari, ko malamai na gari. Kun ga dalilin ku sai a samu al’umma ta gari. Allahu Akbar!Mace ta gari ta sa duniya duk ta zama ta gari.
Mu kuma maza mu lura da yadda addininmu ya karrama mace, ya ba ta girma da daraja, wanda shi ne dalilin da ya sanya muka dauke ta da daraja. Mu yi nazarin rayuwar Annabawa, da salihan bayin Allah, yadda suka yi zamantakewarsu da matansu suka yi hakuri da su suka faranta musu rayuwa, suka nuna musu soyayya ta gaskiya ta tsakani da Allah. Idan muka yi nazarin a kan wadannan abubuwan za mu sauke nauyin da Allah ya dora mana a kan mata.
Kuma idan aka tambaye mu a kan abubuwan kiwon mu wadanda mata suna cikin su, to, a nan za mu bayar da amsa muna masu farin ciki da jin dadi. Annabin (S.A.W.) ya ce, dukan ku masu kiwo ne, kuma za a tambaye ku a kan abin da aka ba ku kiwo a kansa.
Lallai magabatan mu sun yi adalci wajen nuna girman ‘ya mace, kuma sun nuna matsayin ta da sadaukarwar ta. A karshe, Allah ya sa mu kasance masu riko da gaskiya ba son ran mu ba.
0 Comments