Ya kamata ango da amarya ku sani cewar Aure ba wasa bane. Ibada ce mai zaman kanta, domin kowanne mutum da ka sani an samar dashi ne ta hanyar aure.
Sabida haka kenan, a haka kuma ake tsammanin zaku tara zuriyya MAZA da MATA. Wadda manzon Allah saw zaiyi Alfahari da ita.
👉Ango ka yarda da cewar matarka tamkar Abokiyar Arzikinka ce. Ba an kawo Maka ita bane Dan Sabida iyayenta basa sonta bane. A’a an baka ita ne domin Ku yada zuriyya a tsakanin danganta da danginka, domin Su zama dangi guda daya.
👉 Ango ya kamata Ka sani cewar iyayen matarka tamkar iyayenka ne. ya zama wajibi ka girmamasu, ya zama wajibi ka kallesu a matsayin manyan mutane.
👉 Amarya ya kamata ki sani cewar. A bangaren hakki, miji yafi uwa da yafi uba girman hakki.
Dole sai da izininsa zaki fita, dole sai da izininsa zaki aikata kowanne abu, dole sai da izininsa zaki yanke wani hukunci.
👉 Amarya, kada ki shigar da wani zargi tsakninki da mijinki. Ta Dalilin wayar hannu ki kira wani ko wani yana kiranki ko kina chatting da wani wanda ba mijinki ba, ko ki baiwa wani dama ya shiga gidan mijinki, ba tare da izinin mijinki ba ko kina magana da wani, ba tare da izinin Mijinki ba. Duk wadannan suna haifar da Zargi.
👉 Amarya ki sani cewar, Kawaye mutane ne da zakiyi zumunci dasu, amma ba koda yaushe ba, tinda a yanzu kin zama matar aure. Sabida haka sai kin rage committement da Kawaye, musamman ma wadda bata da aure.
Wasu kawayen suna lalata aure, ta hanyar zuga ko hada rigima da fitina. Sabida haka anan sai amarya ta kiyaye.
👉 Amarya ki sani cewar. Yan uwan mijinki, yan uwanka ne, idan kikace sai yan uwanki ne kawai mutane, yan uwansa ba mutane bane. To baki so zaman lafiya ba.
👉 ‘yayan mijinki tamkar yayanki ne. Daga ranar da kika nuna bakya son daya daga cikin yayansa. Tamkar kince bakya son mijinki ne. Ana chanja mace, amma ba’a chanja ‘ya’ya.
👉 Ango da amarya. Zaman aure sai da hakuri. Idan babu hakuri to fa babu maganar zaman aure.
Amarya. Kada ki sake koda da wasa ki kai karar mijinki gidanku. Duk abinda yayi miki idan kikayi hakuri zaku daidaita. Matukar dai akwai soyayya a tsakaninku. Yanzu a gidan miji ake yaji ba gidan iyaye ba.
👉 Amarya, kada ki sake ko da wasa ki tafi gidanku YAJI, yaji yana rage martabar Aure da martabar miji a idon iyayenki.
Wani mijin kuma da zarar kin tafi yaji, xai aika miki takarda gidanku. Kinga ba haka aka so ba.
👉 Amarya, idan kina da kishiya, karki dauka cewar wai an kaiki don kuyi fada da ita ne, ba haka bane, kishiya yar uwa ce. Ba Abokiyar fada bace. Abokiyar zama ce, itace ma wadda zata fara zuwa wajenki a daidai lokacin da kika nemi taimako, Sabida itace tafi kowa kusanci dake.
👉 Amarya ki kiyaye masu zuga mace su cuceki, daga baya koko kina da na sani, ba wuya masu zuga Sun fitar dake daga gidan mijinki.
Duk wadda ta zuga ki akan kishiyarki ko mijinki, sai ki kalleta ki gani. Ita din Tana da aure? Ko kuma bata da aure?
Idan har tana da aure, me yasa ita bata kashe nata auren ba, sai naki?
Idan kuma bata da aure, to ki kaddara cewar so take ta kashe naki Auren, ki dawo gida ki zama irinta. Sabida haka karki yarda.
Daga karshe. Ango ka sani cewar sai Allah ya tambayeka akan amanar da ya danka Maka. Haka amarya kema sai Allah ya tambayeki akan zamantakewar ki da mijinki da kishiyarki da yayan mijinki da duk wanda yake wannan gidan. Duk wanda kika zalunta daidai da rana daya, sai Allah ya saka masa.
Sabida haka lalle ya kamata mu kiyaye gabaki daya.
Allah ya kawo mana zaman lafiya mai dorewa.
Share this:
0 Comments