Miji
Iyaye mata shin wacce tsaraba muke tanadar wa yaranmu a lokacin da za su tafi dakin miji? Amsar da wadansu iyaye ke tunani shi ne tanadin kayan mata ko kayan da’a. Wanda sam ba haka ba ne, ya kamata mu duba a yanzu yadda yawaitar mace-macen aure ke karuwa a kullum kwanan duniya, sai kuma mu tambayi kanmu shin me ke jawo hakan? Sai mu gyara da kanmu. Ba wani da zai zo daga wani wuri ya gyara mana rayuwarmu, mu muka san matsalolinmu haka mu za mu samar da hanyoyin warware ta da kanmu.
Tsaraba ta farko da zamu duba ita ce mu dora auren kansa a kan mizanin da addini ya shimfida tun daga neman auren har zuwa gidan aure. Mu san waye mijin, meye sana’ar sa, ilminsa a kan addini da sauransu. Wani lokaci muna kuskure daga mutum ya fito ba bincike ba komai sai ay i sauri ayi aure a kai yarinya dakin miji ba tare da sanin komai daga gare shi ba. Sannan mu karantar da yarinya ta san mene ne aure ba kawai mu dorata a kan jima’i kawai shi ne aure ba. Muna kuskure matuka.
A koya wa yarinya yadda za ta kula da miji, kamar abincinsa, abin shansa, me yake so meye baya so, kula da yan uwansa da iyayen sa da sauransu. Mu dora ta a kan dabi’ar tsabtar jiki da na muhalli, sai mu kyale yarinya kawai wata ta kware a gyaran jiki amma ba ta kware a gyaran muhalli ba wanda a matsayinta na mace ana bukatar ta iya su duka biyu. Sai iya sarrafa abinci ba kawai na zamani ba har da na gargajiya, domin wani mijin na gargajiya yake so yayin da wani yafi bukatar girke-girken zamani.
Sannan mu koya musu su san cewar su dinnan wata halitta ce masu daraja, ba abin wofintarwa ko wulkantawa ba. Mu koya musu yin gaskiya da kwatanta adalci a cikin gidajen aurensu, su kuma ji tsoron Allah su dauka suna yin komai ne don neman shiga aljanna. Iyaye da yawa kan kyale yara su tafi dakin miji ba tare da sanin komai game da rayuwar aure ba, uwar da ta yi kokari ne ma take hada wa yarinya magungunan kayan mata, wata ma haka za ta kyaleta a kai ta haka nan, da an je kwana biyu a sake ta.
‘Ya mace na bukatar gyara tun da sauran lokaci kafin aure kama daga abincinta, abin shanta da sauransu. Kayan mata ba ya tasiri in babu wadancan abubuwa da na lissafa, amma idan yarinya ta san wadancan ta hada da kayan da’a, to tabbas ta samu “full package” na tsarabar rayuwar aure. Kuma za a rage yawan mace-macen aure a cikin al’umma.
Allah ya ba mu Ikon gyarawa amin.
0 Comments