TSAKANIN JININ HAILA ZUWA WANI JININ HAILAR, KWANA NAWA A KE SAMU MAFI YAWA?:
Wato idan mace ta yi jini ya ɗauke, zuwa kwana nawa ne za a ce sabon jini ya zo ko kuma zuwa kwana nawa ne za a ce a’a wancan jinin na baya ne ya ci gaba da zuba?
A nan shi ma malamai sun yi tattaunawa ta ilimi wajen tantance kwanakin da tsakaninsu ne za a ce an shiga sabuwar haila?
Wasu sun ce sai ya kai kwana takwas. Idan mace ta yi jini ya ɗauke bayan kwana takwas idan wani jinin ya zo, to wannan sabon jinin haila ne ba wancan na baya ne ya ci gaba ba.
Wasu suka ce, a’a idan an sami kwana goma a tsakani, mace ta yi jinin al’ada ya ɗauke ta yi wanka tana sallah, bayan kwana goma sai jini ya zo wannan wani sabon jini ne ya zo.
Wasu suka ce, a’a sai an sami kwana goma sha biyar a tsakaninsu, idan mace ta yi tsarki sai bayan kwana goma sha biyar idan wani jinin ya zo sannan za a ce ga sabon jinin haila nan ya zo. Amma idan kafin waɗancan kwanakin ne sai a ce wancan na biyun ne ya ci gaba da zuwa. Saboda haka da wannan jinin da ta yi na farko da wannan na biyun duk za a ɗauke su a matsayin jini guda ɗaya. Wannan shi ne abin da wasu malaman suka faɗa.
Wasu malaman kuma suka ce, wasu sashin mata sukan tsarkaka daga hailarsu, sannan jini ya dawo musu karo na biyu, wanda bai wuce tsakanin su kwana goma ko kwana goma sha biyar ba, za a ɗauki wannan jinin na biyu a matsayin haila ne ko kuma jinin baya ne ya ɗoru, wato ba sabuwar haila ba ce, waccan ce ta ci gaba? Akwai saɓanin malamai da yawa, amma abin da ya fi shahara shi ne, mafi ƙarancin tsarki tsakanin haila guda biyu shi ne, kwana goma sha biyar ko goma sha uku. Don haka, idan mace ta sami tsarki daga hailarta, sannan sai jini ya sake dawo mata karo na biyu kafin cikar kwana goma sha uku ko sha biyar, ba za ta gina hukuncin a kan cewa haila sabuwa ta zo ba, sai dai ta ɗauka a kan cewa wancan jinin ne na baya ya dawo ko kuma jini ne na ciwo ya dawo mata.
Wasu kuma daga cikin ma’abota ilimi sun ce, babu iyaka tsakanin jinin al’ada guda biyu. Wato idan jini ya zowa mace bayan ta yi tsarki, bayan wasu kwanaki kuma sai jini ya dawo, sai a ce ta shiga haila ta biyu.
Kamar matar da aka sake ta, sai ta yi haila ta kwana shida yadda ta saba, amma bayan kwana biyar sai wani jinin ya dawo, za ta iya cewa ta shiga jini na biyu, kuma bayan kwana biyar sai wani jinin ya dawo, za ta iya cewa ta shiga jini na uku. Za ta iya cewa ta gama iddarta a wata ɗaya, tsakanin kowanne jini a sami ‘yan kwanaki. Wanda kuma a baya mun ce akwai malaman da suka ce, jini sai ya kai kwana goma, ko kwana takwas, ko kwana goma sha biyar wanda shi ne ya fi shahara a tsakanin malamai.
Sun sake kafa hujja dai da ayar nan ta cikin Suratul Baqara (wadda ta ce, “Kuma suna tambayar ka game da jinin haila na mata, ka ce wannan qazanta ne, ku nisanci mata a lokacin da suke jinin al’ada kada ku sadu da su.” A nan Allah ﷻ Ya gina hukunci ne ba tare da ya iyakance wani lokaci na musamman ba . Wannan iyakance lokaci ya samu ne da ƙoƙarin malamai da ijtihadi domin su sauƙaƙawa mutane don su fi saurin fahimta, ba wai don cewa lallai wannan maganar sai an sami kwana kaza ba, maganar Allah ﷻ ce ko ta ManzonSa ﷺ.
Sannan ya zo a hadisin Nana A’ishah (رضي الله عنها) ta ce, “Idan hailarki ta gabato, to ki daina sallah, idan ta ba da baya ta wuce sai ki wanke jinin ki yi sallah.” A nan, Annabi ﷺ ya gina hukuncin haila ne a kan zuwan jini, ba tare da tsayawa zuwa lokaci kaza ba.
Hujja ta uku, wannan ƙaddarawa da malamai suke yi da kwana kaza, duka babu abin da ya zo a cikin littafin Allah ﷻ ko a sunnar Manzon Allah ﷺ kuma da a ce lallai sai an yi la’akari da wannan za a gina hukunci, da Shari’a ta gina hukunci a kai, domin al’amarin jinin al’adar nan yana da alaƙa da manya-manyan ibadu, musamman sallah saboda idan ana jinin al’ada mace ba ta sallah da azumi.Yana da alaƙa da saki, domin ba a sakin mace idan tana jinin al’ada. Mace ba ta sallah ko azumi ko ɗawafi idan tana jinin al’ada. Babu abin da aka gina hukunce-hukunce a kansa irin wannan. Da waɗannan kwanaki da ake iyakancewa suna da muhimmancin gaske da Allah ﷻ da kanSa zai bayyana su a cikin Al-qur’ani mai Girma, ko kuma Manzon Allah ﷺ ya bayyana su a cikin hadisi. Amma saboda abu ne da ya shafi mata, matan nan kuma suna sassauyawa daga gari zuwa gari, ko ƙasa zuwa ƙasa, ko lokaci zuwa lokaci, ko yanayin jiki zuwa yanayin jiki, ko yanayin kwanciyar hankali ko damuwa, ko kuma irin abincin da ake ci, jinin nan yana ƙaruwa ko ya ragu. Don haka sai aka bar abin a bisa kowacce ta yi la’akari da abin da ta sami kanta a ciki.
MENENE MAFI YAWAN KWANAKIN TSARKI GA MACE?:
Babu iyaka dangane da mafi yawan kwanakin tsarki ga mace. Mace za ta iya gama jinin al’ada, kuma sai bayan wata zai zo. Ko ta gama jinin al’ada ba za ta sake yi ba sai bayan wata biyu, ko wata uku, ko shida, ko sai shekara-shekara take yin jinin haila.
Don haka, idan aka sake ta sai ta yi shekara uku sannan za ta gama iddarta. Wata idan an sake ta sai ta yi shekara ɗaya. Wata kuma wata huɗu-huɗu ko wata uku ko wata tara kenan za ta gama iddarta. Saboda haka wannan ya danganta domin kowacce mace akwai yanayin jinin al’adarta.
Akwai ma wadda ba ta yin hailar kwata-kwata a raywurta. Saboda haka wannan ya sa malamai suka ce tun da abin ya danganta da mata, ba za a iya yanke hukunci guda ɗaya ba, sai dai kowacce mace a tambaye ta, yaushe take yin jinin al’ada, kuma kwana nawa take yi, kuma idan ya ɗauke bayan kwana nawa, ko wata nawa, ko sati nawa, ko awa nawa, yake dawowa? Don haka kowacce za a gina mata hukuncinta ne a kan yadda aka same ta da kuma yanayin da ta sami kanta a ciki.
SHIN MACE MAI CIKI TANA YIN HAILA KO BA TA YI?:
Malamai sun yi saɓani dangane da mai ciki cewa idan ta ga jini haila ne ko ba haila ba ne?
Malamai na farko, suka ce mai ciki ba ta yin jinin al’ada kwata-kwata. Saboda haka idan aka ɗauki wannan ƙaulin, (maganar) duk jinin da ya zowa mai ciki, jini ne na rashin lafiya ba zai hana ta ibada ba. Don haka za ta wanke wannan jini ta ci gaba da yin ibadarta kamar yadda ta saba. Kuma wannan shi ne abin da mafi yawan likitoci na duniya suka tafi a kai, kuma ita ce mazhabar Malam Abu Hanifa da Imamu Ahmad da wasu manyan malamai
Na biyu, suka ce ana iya samun mace mai ciki ta yi jinin al’ada, duk da ba kasafai a kan samu ba, amma kowacce mas’ala akan sami abin da yake ya fita daban. Akan sami macen da ta fita daban a cikin mata, ga ta da ciki kuma tana al’ada. Sai dai a nan idan an sake ta ba za a yi la’akari da cewa sai ta yi jini uku ba. Tun da dai tana da ciki lallai sai ta haihu, don haka ba za a yi amfani da wannan al’adarta ba a wajen idda ba, sai dai a yi amfani da ita a wajen ibada. Abin nufi sai bayan wata uku ko bayan wata shida, idan ta ga jini yana fita yadda ya saba zuwa a lokacin al’ada da kalarsa da lokacinsa yadda ta saba, haka take da ciki ma tana al’ada. Wannan sai a yi mata hukunci da abin da ya bayyana daga ɗabi’arta da halinta. Saboda likitoci sun ce ba a yin haila idan mace tana da ciki, ga shi ita kuma ta yi ɗin. Amma fa da wuya a sami mace tana da ciki kuma tana yin haila. Idan kuwa an samu ɗin sai a yi mata hukunci da abin da ya bayyana a gare ta, domin ita ta bambanta da sauran mata: ga ciki ga al’ada. Ana samun ‘yan kaɗan mata masu yin wannan, amma dai asali shi ne, idan mace tana da ciki ba ta jinin haila.
IDAN JININ ALA’DA YA ƊAUKEWA MACE KAFIN LOKACIN AL’ADARTA YA CIKA, YA ZA TA YI?:
Abin da malamai suka ce shi ne matuƙar dai jini ya ɗauke, mace ta je ta yi wanka ta ci gaba da sallah. Wataƙila yanzu daga kwana shida ya dawo kwana biyar, don haka ba za ta ce bari in jira sai kwana ɗayan nan ya cika ba. Matuqar ta duba jinin a lokacin kwanciya ko lokacin tashi ta ga alamar ɗaukewar jini, sai ta yi wanka ta ci gaba da sallah kuma ta ɗauka cewa kwanakin al’adarta ne suka ragu.
MACEN DA LOKACIN AL’ADARTA YA SAUYA YA ZA TA YI?:
Ma’ana, lokacin ya sauya, kwanaki ba su ƙaru ba amma sai lokacin ya sauya ta daina yi a farko, ta koma ƙarshe ko kuma a ƙarshe take yi sai ta dawo baya, ko farko, wannan duka ba zai sauya hukuncinsa da cewa shi jinin al’ada ba ne. Saboda ayar da muka gabatar ta gina hukunci ne a kan jinin al’ada ba tare da cewa a farkon wata ko tsakiya ko ƙarshe ba.
Haka a hadisin Nana A’ishah (رضي الله عنها) cewa Annabi ﷺ Ya ce: “Duk lokacin da kika ga jinin haila, to ki daina sallah.” Bai ce ko a farko ko ƙarshe ba. Saboda haka, ya nuna duk lokacin da jini ya zowa mace, ko lokacin jinin ya sauya, ko adadin kwanakin suka ƙaru ko ragu, ko lokacin ya sauya ya yi gaba ko baya, duka wannan yana nan a jininsa na al’ada kuma za a gina hukunci ne a kan jinin da ɗaukewarsa, zuwansa, ƙaruwarsa da raguwarsa, kamar yadda malamai suka tabbatar da haka.
ƘARUWAR JINI A KAN NA AL’ADA:
Shin idan mace ta saba yin haila kwana shida, sai kuma ya koma kwana bakwai ko kuma ta saba yin kwana bakwai sai ya koma kwana goma, ya za ta yi da wannan qarin kwanakin da ta samu na al’adarta?
A nan ma akwai tattaunawa ta ilimi a tsakanin malamai, amma abin da ya fi rinjaye shi ne, wannan kwanaki da suka ƙaru, shi jinin al’adar ne ya ƙaru, don haka wannan kwanaki da suka qararwa mace na wucewa yadda ta saba al’ada ya qaru da kwana ɗaya ko biyu ko uku ko huɗu, malamai sun yi saɓani.
Wasu sun ce, wannan shi ma jinin al’ada ne, don haka sai ta bari bayan kwana uku sai ta yi wanka ta yi sallah, ko da jinin ya ci gaba da zuba. Wata na biyu ma idan ya zo shi ma haka za ta yi sai ta ƙara kwana uku a kan kwanakin wancan watan. A wata na gaba ma ta qara kwana uku, har ya kai kwana goma sha biyar. Daga nan duk abin da ya ƙaru a kan sha biyar ba jinin al’ada ba ne.
Wasu malaman suka ce, mace za ta yi la’akari da kalar jinin. Idan jinin nan da yake zuba irin na ala’da ne, da ɗabia’rsa da kalarsa da yanayinsa, to kawai za a ɗauka kwanakin al’adarta ne suka ƙaru. Saboda haka za ta yi amfani da cewa yanzu kwanakin al’adarta sun tashi daga kwana shida sun koma kwana goma. Saboda haka sai kwana goman ya cika jinin ya ɗauke sai ta yi sallah. Don haka sai suka kafa hujjoji guda uku:
Ayar da Allah ﷻ Yake cewa: “Suna tambayar ka game da mai al’ada, ka ce, wannan ƙazanta ne” (wato najasa ne). () A nan Allah ﷻ Ya gina hukunci ne a kan samuwar jinin ba wai kwana nawa yake yi ya ɗauke ba, ko kwana nawa yake ya zo, ko ya ƙaru ko ya ragu ba. Duk lokacin da aka sami wannan jini hukunci na nan. Saboda haka hukunci yana zagayawa ne tare da abin da aka gina hukuncin a kai, shi ne jinin al’ada. Idan ba jinin al’ada, ba hukunci, ba tare da lura da cewa kwana nawa ya yi ba.
An ruwaito daga Nana A’ishah (رضي الله عنها) cewa, “Idan hailarki ta gabato ki daina sallah. Idan ta ba da baya, ki wanke jinin, ki ci gaba da sallah.” Suka ce, a nan Annabi ﷺ ya haɗa hukunci ne a kan samuwar jinin haila; zuwansa da ɗaukewarsa.
Saboda haka idan mace ta sami kanta a kan kwanaki suna qaruwa gare ta, matuƙar jinin shi ne ba wai kalarsa ce ta sauya na ciwo ya zo ba.
Idan kuwa ta tabbatar ko tana da zato mai qarfi cewa wannan jinin da ya ƙaru ba na al’ada ba ne, sai ta ginu a kan wannan zato nata mai ƙarfi ko yaƙini nata. Idan ya zo sai ta yi wanka ta yi sallah ta ɗauka wannan kwanakin da suka ƙaru rashin lafiya ce ba jinin haila ba ne. Allah ﷻ Shi ne mafi sani.
Zamu ci gaba insha Allah.
0 Comments