🤱🏻🤱🏻🤱🏻🤱🏻🤱🏻🤱🏻🤱🏻🤱🏻🤱🏻🤱🏻🤱🏻🤱🏻🤱🏻🤱🏻
Shayarwa lokaci ne da mata kansamu kansu bayan shafe tsawon watanni na goyon ciki domin kula da abunda suka haifa.
Nonon uwa abune mai mahimmancin gaske ga rayuwar jarirai domin dorewar lafiya, rayuwarsu, baya ga walwala, annashuwa, tare da kara dankon zumunci da shaquwa tsakanin uwa da danta.
Rashin wayau da dabara shikesa mace tunanin cewa shayarwa zaisa nononta saurin zubewa.
Zubewar Nono lokaci a cimarki take in bakya cin ingantaccen abinci tare da hutu hatta jikinki dole ya sukurkuce bama nono ba. Amma de wajibi musani yau da gobe ta wuce wasa, dole daga sanda shekaru suka ja akaba 30 baya aga komi ya canza bamu da ikon canza haka saide mui kokarin da zamui mu zamo ram.
Shayarwa akai akai shike kawo saurin tsatstsafowar ruwan nono, Macen dake shayarwa akai akai koda danta na cikin hatsarin fuskantar karancin nono shayarwar da take masa akai akai zata sa bazai fuskanci karancin nonon ba.
Baya ga tarin fa'idoji gareki wajen kareki daga cuttukan nono, cuttukan kwayayen haihuwa, cuttukan jijiyoyin jini, karawa garkuwar jiki karfi, karin ni'ima ajika.
---------------‐----------------------------------‐--------------
IRE-IREN RUWAN NONO YAYIN SHAYARWA
---------------‐----------------------------------‐--------------
1. COLOSTRUM MILK
Wannan nau'in madarar nono ce zallah dake zuwa a matakin farko bayan haihuwa da yan mintoci koma tun yayin nakuda. A wasu colostrum na da launin rawaya, me kauri da kuma maiko, awasu kuma ruwan madara sak me kauri.
Yawanci colostrum na karewa ne daga kwana 2 zuwa 3 da haihuwa.
Mahimmancin colostrum shine: itace madarar dake sanya jariri yin kashin farko aduniya (meconium) cikin awoyi 24 da haihuwa, wato tana bude sassan narkar da abinci tare da sarrafashi na jariri domin fara dogaro da kansa sakamakon sanda yake ciki da komi saide ai masa.
Sannan tana da tasiri wajen kawar da kwayoyin cutar virus da aka iya samu sanadiyyar mura daga uwa ko jikin yan barka dakan daukesa.
Uwa uba tana kare garkuwar jikin jariri, tana taimakawa wajen girman jariri da kuma karin lafiyarsa. Ada iyayen mu kanyi kuskure wajen matse wannan ruwan nonon tare da zubar dashi, saide yanzu da yawa sun fahimci amfanin sa. 🤱🏻
2. TRANSITIONAL MILK
Shine ruwan nonon dake maye gurbi yayin da nau'in nono na farko (colostrum) ya kare bayan kwana 2 ko 3 da haihuwa.
Transitional na daukar tsawon sati 2 ne kacal itama kafin ta kare. Wato daga kwana 2 da haihuwa zuwa sati 2 nan ma nau'in nonon da yaro Kesha kalarsa daban ne.
Transitional ta kunshi vitamins, kitse, da sinadarin lactose.
Normally Jariri ya kanzo da girmansa da kuzari bayan haihuwa, amma bayan kwana uku zuwa hudu da haihuwa akan ga jariri ya rage nauyi, ba kamar sanda aka haifesa ba wanda hakan normal yanayi ne. Toh wannan transitional din shine nonon dake taimakawa jariri maida jikin nasa da nauyin nasa da ya rasa bayan haihuwa. 🤱🏻
3. MATURED MILK
Wato rikakken nono yana farawa daga sanda transitional milk ta Kare har zuwa tsawon watanni ko shekarun da mace zatai tana shayar da jaririnta.
Kaso 90% cikin dari na wannan madarar nonon ruwa ne, amfanin ruwa ajika kuwa shine sanya jikin mutum ko yaushe ya zamto hydrated batare da karancin ruwa ajikinsa ba. Ita ke taimakawa yaro ya kasance tsam-tsam batare da bushewar jiki ba, yayin da ragowar kaso 10% din ta kunshin sinadarin sanya kuzari, Gina jiki, da kuma kitse domin taimakawa girman jariri. Wannan yasa ake wayar dakan mahaifa cewa shayar da yaro nono zallah tsawon watanni shida batare da ruwa ba baya masa wata illah saboda kaso 90 na nononsa ruwa ne.
---------------‐----------------------------------‐--------------
Sannan wannan MATURE milk din ta kasu rukuni biyu yayin tsatsafowarta wato: (fore milk da Hind milk).
A) FORE MILK
Wannan shine nau'in mature milk na nono dake fara zuwa yayin da mace ta zauna zata shayar da yaro. Zuwa tsawon mintuna 2 zuwa 3, duk wannan fore milk dince ke zuba.
Tana da karancin kitse, amma akwai sugar me yawa, vitamin, mineral sai ruwa.
Itace madarar nonon dake magance kishirwar jariri. Amfaninta kenan kawar da kishi ga jariri.
Kunga kenan kuskure ne wasa da ita ta yadda zaka ga wasu suna ba yaro nono suna wani abun karshe bakinsa yake kuccewa tana zuba akasa.
B] HIND MILK
Wannan shine rukunin madarar nono dake zuwa minti na 3 ko 4 zuwa sama bayan zaman fara shayarwa wato bayan fore milk ta Kare.
Tana da nauyi, tana da kitse sosai, akwai sinadarin kara kuzari, da Gina jiki.
Wannan nonon shike magance yunwar jariri wato (it satisfied baby hunger).
Wannan sune jerin abunda ke faruwa yayin shayarwa, kowanne kalar nono da aikinsa wanda da yawa nasan hatta matan ba kowacce tasan haka ba.
Wannan tasa ake ba mata shawarar shayar da nonon uwa zalla na tsawon watanni shida batare da ruwa ba domin nonon uwa na kunshe da duk abinda jikin jariri ke bukata kamar yadda nace
---------------‐----------------------------------‐--------------
DALILAN KARANCIN RUWAN NONO
---------------‐----------------------------------‐--------------
Kamar yadda nai bayani asama, abubuwa kalilan wani lokacin Kän kawo karancin samun wadataccen ruwan nono dakan sa dole sai an hada da baiwa mahaifiya magani ko baiwa yara jarirai madara. A wasu matan suna da karancin karsashin samar da sinadaran prolactin da oxytocin wanda wani sashi na kwakwalwa ke sakinsu ta yadda nonon ke tahowa bayan tsotso (pituitary gland).
Wasu lokutan kuma akan ga ruwan nonon akaron farko amma sai daga baya ace ya dauke, irin Wannan Kän faru ne da yawa sakamakon sakacin iyaye mata.
Ga mahimmai daga cikin abubuwan dake jawo karancin ruwan nono:
■- Rashin shayar da jariri nono akai akai. Ya zamto kirika tunanin tunda ba kuka yake ba bai da bukata, ko kuma ma ko yana kukan kirika jin ke wannan yaron yafiye tsotso da yawa. A'a tsotso baya yawa kuma masu yawan shayarwa keda kanki zaki ga sunfi yawan ruwan nono, don haka in kinason magance matsalar ki shayar dashi iya iyawa akai akai.
Akalla sau kada yai lasa da sau 4, hakan ma zai hanaki saurin kuma daukar ciki a tsakanin watanni 6 da haihuwa
■- Sannan inya zamto kina hada shayarwa da aikace-aikace. Duk sanda ya kasance yaronki na shan nono kina Mika hannu kina wani abun nonon na kuccewa daga bakinsa hakan nasa arasa breast sucking reflexes wanda tsotsowar da yake shikesa glands din dake Samar da ruwan nonon ke kara kaimi wajen aikinsa ya bude. Don haka Anso ki natsu ki zauna ki bar komi har ki gama. Hakan zai hana cikin danki hatta yawan kumbura.
■- In ya zamto nono daya kike bashi ko shi kikafi bashi to wannan matsalar ka iya shafar adadin yawan samar da ruwan nonon duk breast din, kuma dole kiga nononki daya yafi daya girma. Don haka ki kasance kina canza mai nono kowanne ya kama akalla Sau bi-biyu ko 3 adukkan zaman shayarwa. Musamman yadda kukaji nai bayanin kalolin ruwan nonon da amfani kowanne abaya.
Gara in ciwo nonon keyi kike bashi daya amma shima mai ciwon ake matsesa ana ragesa.
■- Matsar ruwan nono kina zubawa a feeder ko bottle kina bashi ko kina bari agida anabashi saboda kina zuwa wajan aiki hakan ma na kawo karancin ruwan nonon saboda duk rintsi babu kamar ace yaronkane ke kama nono... hakan na taimakawa jikinki ma sosai, kuma shi zaisa asami wadataccen ruwan nono da shaquwa, hasali ma yin hakan zai taba lafiyar jaririnki domin kinga zai rasa wasu sinadaran masu yawa koma ya zamto madarar kishirwa kurum take kashe masa, sannan dole kiji nonuwa na miki ciwo.
■ Matan dake samun larurar damuwa bayan haihuwa; wasu suke tsoro ko jifa da jaririn ko turesa gefe yaita kuka suna kin kulasa koma kaga suna wasu abubuwa kamar tababbu koma su rika zasu kashesu, ko suke dukansu... postpartum depression/psychosis.... wannan kan shafi shayarwa saide galibi bayan wasu satuttuka sukan dawo daidai, ko kuma in nazo anga likita.
---------------‐----------------------------------‐--------------
Anso a watanni shidan farko ya zamto zallan ruwan nono kike bashi hakan na taimaka wa asami ruwan nono awadace kuma kike bashi akai-akai akalla kobai yi kuka ba digestion din Jirajirai bai wuce awa daya da minti hamsin (1hr, 50mint) jikinsu kan kuma bukatar nono.
Ya zamto kuma kin iya bayar da nonon kansa, wato ya zamto bakin yaro ya rufe shacin bakin nan na nono rijif sosai, bawai kike sa masa kan nono ba, jariri ba kan nono yake tsotsa ba, karki manta bada lebe yake amfani ba, don haka ki hadesa da jikinki ya zamto gemunsa na dungurar nonon hakan na taimakawa tare da hana sa zukar iska da zata kumbura masa ciki.
Sannan inda hali banda shayarwa akwance adaure ake tashi zaune. Sannan bayan angama shayarwa adora jariririn akafada ana dan jijjigasa ana shafa bayansa har sai anji yai gyatsa.... hakan ke nuna nonon ya tsirga masa, bazaike yawan tumbudi ba.
---------------‐----------------------------------‐--------------
Sannan Maza ina jawo hankali kamar ko yaushe nasan Mata wajen aikata abubuwan takaici amma de ake kai hankali nesa: Muke tuna kwanciyar hankalin iyalan mu na daga garemu, Inka kula da iyalinka toh ýayanka ma dole zasu fita daban cikin al'umma, banda riko, ake yafiya.
Allah Ya kara mana lafiya da abunda lafiyar zataci amin.
0 Comments