ME KA SANI KAN "SHIRKA" ?



SAKON MUSULUNCI:




MA'ANAR “SHIRKA DA ALLAH” ([1])

Tambaya: Menene ma'anar shirka?
Yaya kuma tafsirin faxin Allah maxaukakin sarki ya ke:
ﭽ ﮯ ﮰ ﮱ ﯓ ﯔ ﯕ ﯖ ﯗ ﭼ المائدة: ٣٥
Amsa: Shirka yana nan ne kamar yadda sunansa ya nuna, Ma'ana: Shi ne hada ko gama wanin Allah tare da Allah a cikin bauta, kamar bawa ya roqi gumaka ko makamantansu, ko kuma ya yi "istigasa" –neman agajinsu-, ko ya aiwatar musu da bakance, ko ya yi musu sallah, ko azumi, ko ya yi musu yanka, misali kan haka shi ne: bawa ya yi yanka ma Al-badawiy, ko Al-aidarus a yankin Yemen, ko ya yi sallah ga wane, ko ya nemi taimakon neman xauki daga manzo ko daga Abdulkadiri ko daga Al-aidarus ko wassunsu na daga mutanen da su ka riga su ka mutu, da waxanda basa hallare da shi, Wannan dukkansa ana kiransa: Shirka.
Haka kuma lamarin ya ke idan da zai roqi taurari ko aljani, ko ya nemi agajinsu, ko neman xauki daga gare su, ko makamancin haka, saboda haka; idan bawa ya aikata wani abu daga cikin waxannan ibadodi ga daskararrun abubuwa ko ga matattu, ko ga waxanda basa halarce To hakan ya zama shirka ga Allah mabuwayi da xaukaka, Allah yana cewa:
ﭽ ﮰ ﮱ ﯓ ﯔ ﯕ ﯖ ﯗ ﭼ الأنعام: ٨٨
Ma'ana: "Da za su yi shirka da duk abin da su ka kasance su ke aikatawa ya ruguje musu", [Al-an'ami: 88], har ila yau Allah subhanahu yana cewa:
ﭽ ﮯ ﮰ ﮱ ﯓ ﯔ ﯕ ﯖ ﯗ ﯘ ﯙ ﯚ ﯛ ﯜ ﯝ ﭼ الزمر: ٦٥
Ma'ana: "Kuma haqiqa an yi wahayi zuwa gare ka, da kuma waxanda su ka kasance gabaninka cewa da za ka yi shirka To da aiyukanka sun ruguje, kuma da ka kasance daga cikin masu hasara", [Az-zumar: 65].
            Yana kuma daga cikin shirka: Bawa ya bauta ma wanin Allah ibada cikakkiya, shi wannan aikin ana iya kiransa shirka kamar yadda ake kiransa: kafirci; Don haka duk wanda ya kawar da kansa ga barin bautar Allah kwata-kwata, ta fiskar sanya bautarsa ga wanin Allah, kamar bishiyoyi ko duwatsu ko gumaka, ko aljanu, ko kuma sashen matattun da su ke kiransu da waliyyai, suna masu bauta a gare su, ko suna yi musu sallah ko azumi, tare da mance Allah gabadaya To wannan shi ne mafi girma kafirci, mafi kuma tsananin shirka. Allah ya kiyashe mu.
            Haka kuma waxanda su ke musanta "samuwar Allah"; harma su ce: Babu wani Allah, ita kuma rayuwar duniya a wajensu ita ce kawai (ma'ana: babu tayar da mutane bayan sun mutu don sakayya da hisabi), kamar yan gurguzu, da mulhidai masu inkarin samuwar Allah, Wadannan gabadayansu sune suka fi kowa girman kafirci, kuma sune mafi bacewa ma gaskiya, tare da girman shirka. Allah ya kiyashe mu. Manufa dai anan ita ce: Lallai wadannan akidu da makamantansu ana kiransu shirka, kamar yadda ake kiransu: kafirce ma Allah mabuwai da daukaka.
            Da yawa daga cikin mutane suna yin kuskure a wannan gavar; ko don saboda jahilci, sai su kira: rokon mamata da neman agaji a wajensu da: Wasila, sai kuma yi zaton halaccin hakan, Wannan kuma kuskure ne mai girma; saboda waxannan aiyukan na daga cikin manya-manyan shirka ma Allah, koda kuwa wassu jahilai ko mushirkai sun kira su da: Wasilah. Wannan kuma shi ne addinin mushirkai wanda Allah ta'alah ya zambe su akan aikata su, ya kuma aibanta su da shi, kana kuma ya aiko manzanni ya saukar da littatafa domin a hani mutane aikata shi, a kuma tsawatar musu.
            Amma "Wasilar" da aka ambata a cikin faxinsa mabuwayi da xaukaka:
ﭽ ﮯ ﮰ ﮱ ﯓ ﯔ ﯕ ﯖ ﯗ ﭼ المائدة: ٣٥
To, ma'anarta shi ne: Neman kusanci zuwa ga Allah ta hanyar yi masa biyayya, Wannan kuma shi ne ma'anarta a wajen ma'abota ilimi gabaxayansu; Sallah abu ne da ake kusantar Allah da ita; don haka ita: Wasila ce, Yin yanka don Allah shi kadai shima: Wasila ne, kamar: layya da hadaya, azumi ma wasila ne, suma sadakoki wasila ne, haka kuma zikirin Allah da karatun alqur'ani suma wasila ne, Wannan kuma shi ne ma'anar faxinsa maxaukakin sarki:
ﭽ ﮯ ﮰ ﮱ ﯓ ﯔ ﯕ ﯖ ﯗ ﭼ المائدة: ٣٥
Ma'ana: "Ya ku waxanda su ka yi imani ku ji tsoron Allah, kuma ku nemi kusanci izuwa gare shi", [Alma'idah: 35]. Ma'ana: Ku nemi kusanci izuwa gare shi ta hanyar aikata biyayya a gare shi, haka Ibnu-kasiir da Ibnu-jariir, da Albagawiy da wassunsu su ka faxa daga cikin jigajigan maluman tafsiri. Don haka ma'anar ita ce: Ku nemi kusanci izuwa ga Allah da yi masa xa'a a ko-ina ku ka kasance, daga cikin abubuwan da Allah ya shar'anta muku na sallah da azumi da sadakoki da makamantan haka.
            Haka kuma faxinsa a cikin xaya ayar:
ﭽ ﯥ ﯦ ﯧ ﯨ ﯩ ﯪ ﯫ ﯬ ﯭ ﯮ ﯯ ﯰ ﯱﯲ ﭼ الإسراء: ٥٧
Ma'ana: "Waxancan su ne waxanda su ke addu'a da bauta, suna masu neman kusanci izuwa ga ubangijinsu, wanene daga cikinsu zai fi tsananin kusanci, suna kuma fatan samun rahamarsa, suna tsoron azabarsa", [Al-isra'i: 57].
Haka nan lamarin annabawa da salihan bayi ya ke kasancewa; suna neman kusantar Allah da hanyoyin da ya shar'anta, kamar jihadi da azumi da sallah da zikiri da karatun alqur'ani, da wassun haka na sauran nau'ukan wasilah.
            Amma zaton wassu mutane da ke cewa ita "Wasila" ita ce: ratayuwa da matattu, da neman agajin waliyyai, wannan zaton kam kuskure ne kuma varna, Wannan kuma shi ne aqidar mushirkai da Allah ya ke magana akansu a cikin faxinsa:
ﭽ ﮢ ﮣ ﮤ ﮥ ﮦ ﮧ ﮨ ﮩ ﮪ ﮫ ﮬ ﮭ ﮮ ﮯ ﭼ يونس: ١٨
Ma'ana: "Kuma suna bauta ma wanin Allah waxanda basa iya cutar da su, ba kuma sa iya amfanar da su, suna masu cewar: Waxannan su ne masu cetonmu a wurin Allah", [Yunus: 18]. Sai Allah ya mayar musu da martini a cikin faxinsa:
ﭽ ﮱ ﯓ ﯔ ﯕ ﯖ ﯗ ﯘ ﯙ ﯚ ﯛ ﯜﯝ ﯞ ﯟ ﯠ ﯡ ﭼ يونس: ١٨
Ma'ana: "Ka ce da su: Shin kuna labarta ma Allah ne abin da bai sani ba a cikin sammai ko a cikin qassai! Tsarki ya tabbata masa, kuma ya xaukaka akan abin da ku ke masa shirka", [Yunus: 18].

Post a Comment

0 Comments