LITTAFIN FIQHU (DARASI NA ASHIRIN) :



KIRAN SALLAH DA IQAMAH

Kiran sallah da tayar da iqamah yana cikin mahimman abubuwa da suke qara bayyana girma da buwayar addinin Musulunci, domin kullum sai an kira sallah sau shida, an tayar da iqamah sau biyar, ya zama (sau 2160) kenan a shekara, iqamah (sau 1800) a shekara. Abinda kiran sallah ya ƙunsa shi ne bayyana kalmar shahada, wadda ita ce rukunin farko da a ka gina addinin Musulunci a kansu.
Malamai sun yi magana biyu a kan hukuncin yin kiran sallah; wasu daga ciki suka ce, yin kiran sallah wajibi ne a kan dukkan musulmi, amma idan wani ya yi ya ɗaukewa ragowar. Wasu suka ce sunna ce mai ƙarfi, ya zama ana yin kiran sallah a kowanne gari a kowanne masallaci.
Sallolin farilla da sallar Juma’a kawai ake yiwa kiran sallah. 
Sallolin da ba a yi musu kiran sallah su ne, 1.sallar idi biyu da sallar rokon ruwa
2. sallar kisfewar wata ko rana,
3. sallar jana'iza
4. sallar wutri.
5. Duka sallolin nafiloli ba a yi musu kiran salla.

Ba a kiran sallah sai lokaci ya yi in banda sallar Asuba, wadda ake yi mata kiran sallah biyu, ɗaya kafin lokaci ya yi na biyu bayan lokaci ya yi. Saboda hadisin Bilal (رضي الله عنه) da Manzon Allah ﷺ ya ce: Bilal (رضي الله عنه) yana kiran sallah ne da daddare don haka ku ci ku sha, har sai kun ji kiran sallah daga Ɗan Ummu Maktum (رضي الله عنه) saboda shi makaho ne ba ya kiran sallah har sai an ce masa alfijir ya keto. (Buhari da Muslim). 
1. Za a iya kiran sallah domin rama sallar da ta tsere.
2. Mutum ɗaya idan zai yi sallah zai iya kiran sallah. 
3. Idan mutum zai haɗa sallah biyu, kiran salla ɗaya ya wadatar masa. 
4. Mace ba za ta yi kiran sallah ba, sai idan mata ne kawai a wajen babu namiji da zai jiyo muryarta, kamar yadda Al Imam Annawawiy ya faɗa da fatawar Imam Malik da Imam Shafi’i da wata riwaya daga Imamu Ahmad. () 
5. Kiran sallah ya zo da siga kala kala. Akwai yadda ya zo a hadisin Abi Mahzurah (رضي الله عنه) da hadisan Bilal (رضي الله عنه), duk wanda a ka ɗauka ya wadatar. Amma duk wanda zai zama ladani wajibi ne ya je wajen malaman Musulunci su koya masa yadda ake kiran sallah, domin mafi yawan masu kiran sallah suna kurakurai da yawa. A kwai buqatar a riqa shiryawa ladanai bita a kan kiran sallah da iƙama domin a riƙa gudanar da komai a kan ilimi. 
A ckin kiran sallah na Asuba za a ƙara Assalatu Khairun minan naumi. Wasu malamai sun ce a cikin kiran sallah na farko za a faɗa, wasu kuma sun ce a cikin kiran sallah na biyu ne. Wasu malaman ma cewa suka yi a cikin kowacce kiran sallar za a faɗa, wasu kuma suka ce an bayar da zaɓi. Ma’ana za a iya faɗa a kira na farko ko a na biyu, amma abin da ya fi rinjaye shi ne a cikin kiran sallah na farko za a yi assalatu khairun minan naumi. 

SUNNONIN MAI KIRAN SALLAH
An so ga wanda zai yi kiran sallah ya kula da waɗannan sunnoni kamar haka:
1. Ya zamo musulmi
2. Ya zamo namiji
3.Ya zamo mai hankali.
4.Ya zamo adali amintacce. 
5.Ya zamo baligi mai hankali.
6.Ya zamo masani da shigar lokacin salla da fitarsa.
7. Ya zamo mai murya. 
 8.. Idan zai kira sallah ya zama yana da tsarki na wankan janaba ko da alwala. 
9. . Ya yi kiran sallar a tsaye. 
10. Ya fuskanci Alqibla.
11. Ya sa yatsunsa a cikin kunne ya kama kunnensa. 
 12. Ya dinga waiwaye hagu da dama lokacin da yake faɗar hayya alas salah. 
13.. Ya ɗaga muryarsa ya kyautata ta. 
14. . Idan da dama ya zama a wajen masallaci (ba a ciki ba),
15. Ya hau wuri mai tudu idan babu sifika.
16. A tsaye ake kiran sallah ba a zaune ba. 

ABUBUWAN DA SUKA SHAFI WANDA YA JIYO KIRAN SALLAH
1. Ya faɗi irin abin da mai kiran sallar yake faɗa: 
2. Amma a wajen hayya alas salah, sai ya ce lahaula wala quwwata illa billah. 
3.A wajan faɗar hayya alal falah, sai ya ce lahaula wala quwwata illa billah. 
4.Ya yi wa Annabi ﷺ salati. 
5. Ya yi wannan addu'ar ta roqawa Annabi ﷺ wasila da fadhila. (matsayi da ɗaukaka da fifiko).
6. Ya yi addu'a ta neman buqatar duniya da lahira.
7. Duk wanda yake cikin masallaci, kada ya fita bayan an kira sallah, sai bayan an gama salla, sai idan alwalarsa ce ta warware zai yi wata. 

TAFIYA MASALLACI
Wanda zai tafi masallaci ya kula da waɗannan sunnoni 
1.Ya ta fi da alwala. 
2.Yana zikrin tafiya wajen sallah. 
3.Ya ta fi cikin nutsuwa da hankali. 
4.Idan zai shiga masallacin ya shiga da ƙafar dama ya fara cire takalmin ƙafar hagu.
5.Ya yi addu'ar shiga masallaci. 
6.Ya yi nafila kafin ya zauna.
7. Ya shagala da zikiri kafin liman ya iso ko a tayar da sallah. 
Duka a duba littafin موسوعات الفقه الإسلامي.
الفقه المصفي ،
صحيح فقه السنة.
Zamu ci gaba insha Allah.

Post a Comment

0 Comments