LITTAFIN FIQHU DARASI NA SHA UKU


 

SUNNONIN ALWALA
Abin da ake kira sunnah a wajen malaman fiƙhu shi ne duk abin da yin sa ba wajibi ba ne, amma idan mutum ya aikata shi zai sami lada, idan bai aikata ba babu laifi a kansa. Sunnonin alwala su ne:
1. Yin aswaki a farko kafin mutum ya fara alwala.
2. Wanke kowacce gaɓa sau uku-uku ko biyu-biyu. Idan ko`ina ya sami ruwa a wankewar farko, shi ma sunnah ce ta alwala.
3. A wajen kurkura baki da wajen shaƙa ruwa da facewa, ya haɗe su. Duk ɗebo ruwa ɗaya sai ya raba shi biyu ya zuba rabi a baki ya kurkura, sannan ya shaƙa rabin a hancinsa ya face, ya yi haka sau uku. Kada ya yi baki da ban hanci da ban.
A wajen kurkurar baki ya yi a hankali idan yana azumi saboda kada ruwa ya wuce masa. Amma idan ba ya azumi ya kurkura bakinsa sosai. Ya zubar da ruwan da ya kurkura kada ya haɗiye.
4. Ya fara da dama kafin hagu. Ya fara wanke hannun dama kafin na hagu, a wajen ƙafa ya fara wanke ƙafar dama kafin ta hagu. Nana A’ishah (رضي الله عنها) ta ce, “Manzon Allah ﷺ yana fara komai daga dama har a wajen tsarki da alwala da dukkan lamarinsa.” (Matuƙar ba abin da Shari'ah ta ce a fara da hagu ba ne).
5. A wajen wanke gaɓɓai su jiƙu sosai yadda ko’ina zai sami ruwa.
6. Wajen wanke ƙafa ya kula da iyakar da Shari'ah ta sanya zuwa idan sawu. Mai yin alwala ya kula sosai da wannan, amma babu laifi ya ɗan ƙetare zuwa ƙwauri amma tsayawa inda Shari'ah ta iyakance ya fi dacewa.
7. An hana ɓarnar ruwa a wajen ibada. Don haka wanda zai yi wanka ko alwala, ya tabbatar ya kiyaye ɓarnar ruwa, ya yi amfani da ruwa daidai buƙata.
8. Idan ya gama alwala sai ya yi addu'a, wacce aka ruwaito daga Manzon Allah ﷺ ya ce: “Babu wani mutum da zai yi alwala mai kyau, sannan ya karanta wannan addu'ar face sai an buɗe masa ƙofofin gidan Aljanna guda takwas ya zabi wacce yake so ya shiga.” Addu’ar ita ce:
((أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّداً عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ)).()
Ma’ana: “Ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya bisa cancanta sai Allah, ﷻ Shi kadai ba Shi da abokin tarayya, kuma na shaida Annabi Muhammadu ﷺ bawanSa ne kuma ManzonSa ne ﷺ.” 
Ko kuma ya karanta wannan:
((أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّداً عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ ، اللَّهُمَّ اجْعَلْنِي مِنَ التَّوَّابِينَ وَاجْعَلْنِي مِنَ الْمُتَطَهِّرِينَ)) ().
Ma’anar abin da ka ke faɗa shi ne: “Ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya bisa cancanta sai Allah, ﷻ Shi kadai ba Shi da abokin tarayya, kuma na shaida Annabi Muhammadu ﷺ bawanSa ne kuma ManzonSa ne ﷺ. Ya Allah Ka sanya ni cikin waɗanda suke tuba, kuma Ka sanya ni cikin waɗanda suke tsarkaka.”
Ko kuma ya karanta: 
((سُبْحانَكَ اللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ، أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ، أَسْتَغْفِرُكَ وَأَتوبُ إِلَيْكَ)) ().
Ma’ana: “Tsarki da godiya sun tabbata gareKa ya Allah. Ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya bisa cancanta sai Kai. Ina neman gafararKa. Ina tuba gareKa.”
 9. Idan da hali, duk sanda mutum ya yi alwala ya yi sallah raka`a biyu da wannan alwalar saboda hadisin Bilal (رضي الله عنه).
Allah ne masani
Zamu ci gaba insha Allah.

Post a Comment

0 Comments