๐˜๐€๐‘๐Ž๐ ๐ƒ๐€๐Š๐„ ฦ˜๐ˆ๐ ๐’๐‡๐€๐ ๐๐Ž๐๐Ž




๐Ÿคฑ๐Ÿป๐Ÿคฑ๐Ÿป๐Ÿคฑ๐Ÿป๐Ÿคฑ๐Ÿป๐Ÿคฑ๐Ÿป๐Ÿคฑ๐Ÿป๐Ÿคฑ๐Ÿป๐Ÿคฑ๐Ÿป๐Ÿคฑ๐Ÿป๐Ÿคฑ๐Ÿป๐Ÿคฑ๐Ÿป๐Ÿคฑ๐Ÿป๐Ÿคฑ๐Ÿป๐Ÿคฑ๐Ÿป

Ba ko yaushe bane don jariri ko yaro dan kasa da shekaru biyu na qin shan nono, ko saurin sakin nonon inya fara sha... za'ace bashi lafiya ba, ahau neme-nemen magani ana dura masa. 

Nasha fada magani guba ne kowanne iri muddin aka shasa batare da tabbatuwar ciwon da ya dace da maganin ba! har kuwa su Paracetamol, B-complex, dinnan da multivitamins da ake rainawa.

Don haka kamar yadda lafiya kalau amma saboda wani abu kuke kasa cin abinci shima jariri mutum ne haka yake! Karku dauka don kurum dan mitsi ne hakan na nuna baisan komi ba, sai kun dura masa abinci ko bayaso. 

Wasu lokutan kuke hanasa sha; musamman in yaro baya kuka, baya rikici, baya qwalla, bakuma ya zazzabi hakan na nuna kalau yake wani daliline ya hanashi.

________________________________________

๐†๐š ๐š๐›๐š๐›๐ž๐ง ๐๐š ๐ค๐š๐ง๐ฌ๐š ๐ฒ๐š๐ซ๐จ ๐ฒ๐š๐ฃ๐ข๐ง ๐š๐ข๐ค๐ข๐ง ๐ฌ๐ก๐š๐ง ๐ง๐จ๐ง๐จ ๐ค๐š๐ฆ๐š๐ซ ๐ก๐š๐ค๐š:

■- Karancin tsafta daga uwar! Kila hammatarta babu aski, kokuwa kinyi aiki kinyi zufa kinzo kin dorasa acinya alhalin iska na kado masa tashin matse-matsin hammatarki, koda ya kama nono tabbas zai saki, domin shima yanajin tsamin.

■- Rashin tsaftar hannayenki, kila jikinki tsaf amma kin tabo abu mai karni, ko wari ahannunki kuma kinzo yayin sakarmasa salebar brazier dinki kin dunguri kan nonon nan ma yana iya kin sha. Inkika matsa kuma yasa kuka.

■- Rashin tsaftar rigar nono da kuma rashin wanke ko goge kan nonon sosai bayan yaro ya kammala sha, wasu rigar nonon ce saita shafe yini biyu jikinsu, zufa da kuma normal bacteria din kan fatarki nada tasiri musamman inya zamto dama da kin gama bada nono kurum jan salebar rigar nonon kike ki mayar bakya tsaftace kan nonon, haka anjima zaki ciro ki qara cusa masa abaki... hakan har gudawa yana iya jawoma jaririnki. Don haka sai ankiyaye.

■- Canjin sabulun wanka me karfin kamshi, wani yana kama fata har abaki ajishi... don haka wannan ma na hana yaro kama nono, har sai kin koma irin wanda ya saba dashi mara karfi da baya iya jinsa.

■- Shafa turare me karfi wanda shima bai saba dashi ba, kamar mune kaima akwai turaren da inwani yasa sai kaji kamar zakace wayyo Allah inya tsaya kusa dakai... toh suma hakane, wannan na iya hanasu shan nono.

________________________________________

■- Juyowar kwanakin haila, shima nasa yaro ya kauracewa shan nono domin mizanin sinadarin gishiri-gishiri acikin nono wato sodium & chloride na karuwa, yayin da sinadarin kanwa-kanwa da zaqi keyin kasa wato potassium & lactose wanda kuma su yaro yafiso. Kunga ko a manya in gishiri yai yawa a abinci wani baya iya ci. 

■- Hakanan yayin HAILA koda canjin dandanon nono bai canza ba akan samu adadin ruwan nono yadanyi kasa hakan ma iya sa jariri inyaji baya isarsa yai zuciya ya dena wahalar da bakinsa saboda gajiyar tsotso alhalin babu wadataccen ruwa

■- Hakanan ma samuwar juna biyu alhalin ga wani ana shayarwa shima na iya sa irin wancan canjin da ake fuskanta yayin haila, wanda hakan na iya sa yaro ya yaye kansa.

■- Haka nan wani magani dake uwar kesha walau na hausa kona asibiti, galibi na asibiti shiyasa likita ke tambaya ko kina da ciki ko shayarwa kafin arubuta miki magani, idan kikai masa karya alhalin kina shayarwa irin abunda zai iya faruwa kenan, yaronki yaqi nono kuma kizo nonon yaita ciwo. Haka cin irinsu tafarnuwa ko wani nau'in abinci da ada bakya ci wanda suna iya ratsa ruwan nono.

■- Ko yawan dauke hankalin yaro wato distracting, don wani yaron koya yaji magana ko motsi sai ya waiga, shyasa zakaga suna shan nono suna saki. Irin wannan maganinsu kike shiga inda yake tsit babu hayaniya sai kui shayarwarku anatse, ko atsohe kunnuwan da wani abu kamar auduga kafin agama Inba haka ba koya yaji motsi ba fasa juya zai ba.

________________________________________

Wadannan sune wasu daga mahimman ababen dake sa yaro kauracewa nono. Don haka kiyayewa kurum suke bukata babu bukatar zuwa kita cusawa yaro magani, ki lura da kyau, saide in akwai alamun rashin lafiya toh sai ataho ga likita.

□ Sannan karki manta duk sanda kika gama baiwa yaro nono kike dorasa akafada kina shafa bayansa har sai kinji yayi gyatsa... hakan alamace ta ya koshi, inbai gyatsa ba akuma maida shi kan nono.

□ Ganin jariri na yawan kwalla ko hawaye koda baya kuka haka alamace ta nono baya isarsa, koda kuwa ana bashi kila ruwan nono babu sinadaran da zasu kosar dashi, sai anemo madara wacce take ta yara irin NAN dinnan akara masa da ita.

□ Ganin jariri ko yaro na yawan tsilla fitsari hakan alamace ta yana samun kyakkyawan shayarwa.

Fatan an ilmantu. Burina naga al'umarmu munyi lafiya, rayuwarmu ta canza, birni da kauye ana samun lafiyayyun yara masu tasowa.
________________________________________
✍๐Ÿผ
[Ibrahim Y. Yusuf]

Post a Comment

0 Comments