📚📚📚📚📚📚📚📚📚📚📚📚📚📚
Ciwon Hanta kamar yadda nasha bayani akai; larura ce da kwayoyin cutar birus ke shiga cikin hanta ta hanyoyin jini su rikita kodar, su hargitsa ayyukan hanta.
Kwai nau'ikan ciwon hanta har kala shida wato rukunin 𝑩, 𝑪, 𝑫, 𝑬, da kuma 𝑭.
Amma mafi hatsari wanda kuma sune sukafi yiwa hanta illa sune Hepatitis 𝐇𝐞𝐩𝐚𝐭𝐢𝐭𝐢𝐬 𝐁 & 𝐂.
Sannan banda wadannan rukunin kwayoyin cuta sauran abubuwan da suke lalatawa tare da kashe hanta sune:-
▪︎Giya wato arasa
▪︎Burkutu
▪︎Shan miyagun kwayoyi
▪︎Sha ko shakar wasu nau'ikan guba (poisons) da sauransu.
Saide tunda nau’in hepatits B da C sunfi illah akansu ne zan fadada bayani.
••••••••••~~~▪︎•●●■●●•▪︎~~~••••••••••
𝐑𝐔𝐊𝐔𝐍𝐈𝐍 ���𝐈𝐖𝐎𝐍 𝐇𝐀𝐍𝐓𝐀 𝐁 & 𝐂
Hanyoyin da ake daukar wadannan kwayoyin cuta b&c dake nakasa hanta hanyoyi daya ne da akebi wajen daukar cutar kanjamau wato (HIV).
Hasali ayanzu haka anfi samun mace-mace daga cututtukan hanta fiye dana cutar kanjamau! saboda zarar ciwon yai karfi ajika tohfa babu magungunan ciwon masu karfi kamar yadda aka samar dana kanjamau.
Haka nan duba da fadakarwa da ake tayi akan ciwon kanjamau tare mantawa dana hanta... yasa mutane suna daukar dukkan matakin kiyaye kanjamau din.
Mutane fiye da Miliyan biyu [2Millions] ke mutuwa duk shekara dalilin Ciwon Hanta... amma masu kanjamau mutum miliyan daya ne [1Million] ke mutuwa duk shekara dalilin ciwon. Kunga kenan double figure.
Haka kuma kusan kowa yasan illar cutar kanjamau amma da yawa basu san illar ciwon hanta ba. Shiyasa da yawan mutane idan zasu yi aure sai dai ayi gwajin kanjamau da Genotype kurum batare da hadawa dana ciwon hanta ba, sai yan qalilan.
Abunda ya dace mutane su sani shine; yawanci awurin gwajin jini ne kawai ake iya gano mutum na dauke da kwayar cutar... domin takan iya shekara da shekaru mutum baima san yana dauke da kwayar cutar ba.... sanda zata bayyana kuma sannan an makaro kila.
••••••••••~~~▪︎•●●■●●•▪︎~~~••••••••••
𝐇𝐀𝐍𝐘𝐎𝐘𝐈𝐍 𝐊𝐀𝐌𝐔𝐖𝐀 𝐃𝐀 𝐂𝐈𝐖𝐎𝐍
Hanyoyin da ake daukar wadannan kwayoyin sune:-
■ Jima'i da mai dauke da kwayar cutar zuwa wanda bai dauke da ita walau Miji ko Mata ko dalilin fasiqanci
■- Kuskure wajen karin jinin da ba'ai wa me bada gudunmawar jin gwajin tantance kwayar ciwon hanta ba.
■- Amfani da kayan kaifin da basu da tsabta wato wanda wani mai ciwon yai amfani dasu har jini ya ta6a, kamar; askar wanzaman da ba'a gasata ba, amfani da clipper da ba'ai sterilizing dinta ba ansa sanitizer, ko amfani da rezar da mai ciwon yayi amfani da ita,
■ Amfani da allurar sirinji guda 1 zuwa ga wani mai ciwon, musamman rukunin mashaya dake yiwa kansu da kansu allura acikin jijiya domin su bugu.
■- Sai ta hanyar cin abinci da cokali daya tare da mai cutar, kota hanyar ya gwaguiyi abu da baki ya baka kaima ka dora kamar wajen cin masara, mangoro ds... domin bakin wasu ya kanyi jini.
■- Sai kuma daukar kwayoyin cutar wajen uwa mai kwayar cutar yayin haihuwa ko yayin shayarwa.
𝙺𝙰𝙼𝙰𝚁 𝚈𝙰𝙳𝙳𝙰 𝙽𝙰𝙲𝙴
Kwayoyin cutar shiga cikin hanta suke suita barcinsu, sui likimo... Shiyasa da yawa masu dauke da kwayoyin cutar basajin wasu alamu tsawon shekaru sai ranar da suka farka suka fara cin hantar tare da toshe hanyoyin jinin cikinta sannan alamu zasu fara bayyana.
Amma a wannan tsakanin ne masu ciwon ke yada ta musamman ga abokan zama na aure da kuma ’ya’yansu.
••••••••••~~~▪︎•●●■●●•▪︎~~~••••••••••
𝐀𝐋𝐀𝐌𝐎𝐌𝐈𝐍 𝐂𝐈𝐖𝐎𝐍 𝐇𝐀𝐍𝐓𝐀
𝐒𝐮���� 𝐡𝐚𝐝𝐚 𝐝𝐚:
■- Yawan zazzabi
■- Yawan kasala, da rashin jindadi ko kuzari ajika,
■- Rashin son cin abinci
■- Kaikayin jiki akai akai da yaki jin magani da dabaru, musamman in an wanka
■- Ganin koya mutum yadan quje fatarsa sai jini
■- Jin ciwon kuibin ciki musamman bangaren dama daga kasan hakarkari, zuwa tsakiyar ciki.
■- Yawan tashin zuciya koma ya zamto hade da amai lokaci-lokaci
■- Fitsari me duhu ko kore-kore aga inya diga akaya baya fita yadda ya kamata da
■- Kashi me kalar ruwan kasa-kasa
■- Ganin jijiyoyin jini wajen cibiya sun tashi sunyi rudu-rudu hade da kumburin ciki
■- Kumburin kafafu
■- Canzawar kalar idanu zuwa ruwan rawaya {yellow🟡}
Musamman daga sanda akaga idanu sun kaďa daidai wannan lokaci ne dole a dauki matakin kashe kwayoyin cutar domin kada su nakasar da hantar gaba-daya, wanda babban abin da suke kawowa shine Kurarraji ajikin hanta su sata ta motse ta lalacewa ta zamo yar karama.
Daga nan cikin mutum zai fara tara ruwa ya soma kumbura kamar tanki abunda muke cewa ASCITES shikenan hakan yasa jini yakewa komawa da baya zuwa zuciya domin ba hanya wanda hakan zaisa zuciyar mutum ta sami matsala wato Heart failure wanda inba ai wani abu ba sai mutuwa.
Ciwon hanta zafinsa ya bambanta daga jiki zuwa jiki. Kuma duk wanda ya kamu da Hepatitis B toh zai iya kamuwa da Hepatitis D. Domin ana ganin hepatits D ne kurum a mutanen da suke da Hepatitis B.... kunga kenan Double Trouble domin wadannan kwayoyi rukunin B na iya haddasa cutar kansar hanta wato Hepatocellular carcinoma... daka iya watsuwa ga sauran sassan jiki. Sabanin C da bata sa cancer saide anfi daukarta wajen karin jini amma kuma maimakon cancer ita ke lalata hantar ta sa mata kurarraji ta yadda za'a ga ciki ya kumbura dam... sannan mutum ya hadu da ciwon zuciya.
••••••••••~~~▪︎•●●■●●•▪︎~~~••••••••••
𝐖𝐀𝐊𝐄 𝐂𝐈𝐊𝐈𝐍 𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐑𝐈𝐍 𝐊𝐀𝐌𝐔𝐖𝐀 ��𝐀 𝐂𝐈𝐖𝐎𝐍 𝐇𝐀𝐍𝐓𝐀
• Mutane masu shan barasa/giya/burkutu
• Mutane masu ciwon sugar type2
• Mutanen masu yin zanen tattoos ajika, ko hujin kunnuwa, jiki dasauransuu
• Mutane masu kiba/te6a
• Amfani da sirinji guda daya wajen allura
• Amfani da Kayayyakin kaifi batare da kariya ba
• Masu jima'i batare da matakan kariya ba
• Mutane masu tarihin ciwon hanta cikin dangi
• Karin jini agida, ko kananun asibitocin daba kayan aiki ko doka bata yadda ba.
• Masu saida sinadaran chemicals na maganin kwari walau na noma da sauransu
••••••••••~~~▪︎•●●■●●•▪︎~~~••••••••••
𝐌𝐀𝐆𝐀𝐍𝐈𝐍 𝐂𝐈𝐖𝐎𝐍
Magunguna da alluran da ake amfani da su a ci karfin kwayoyin cutar kafin su kai ga illa suna da matukar tsada sosai, shiyasa mukan ce riga-kafi yafi magani tunda akwai rigakafin ciwon,,, sabanin kwayar kanjamau wadda har yanzu ba'a gano allurar riga-kafinta ba.
■ Idan adadin virus din bai mummunar illa ba ta yadda duk da bayyanar alamun ciwon amma hantar na aiki kusan 50% magunguna masu tsada da shawarwari da allurai na iya aiki wajen farfado da ita. Tunda ita karan kanta tana da kokarin gyara kanta sai in abu yaci tura.
■ Idan already ta yi kurarraji ta kankance wato Cirrhosis, har ciki ya tasa... mafita kurum shine kurum aima mutum dashen hanta. Wato kai addu'a kuma ka jira wani ya mutu yaima ko yan uwansa suima kyautar hantarsa
■ Idan baka samu mema kyauta ba gaskiya ba abunda likitoci zasu iyama a wannan ga6a domin babu hantar roba don haka rashin iya tace guba da sarrafa suga da bata iyawa gubar amonia ce zata bi jini ta tafi kwakwalwar mutum tai halakasa shikenan. Baya ga tsananin jinya da galibi dama in mutum yazo end stage dinnan toh baima san ina kansa yake ba.
Don haka rigakafi yafi magani.
••••••••••~~~▪︎•●●■●●•▪︎~~~••••••••••
𝐇𝐀𝐍𝐘𝐎𝐘���𝐍 𝐊𝐀𝐑𝐈𝐘𝐀 𝐃𝐀𝐆𝐀 𝐂𝐈𝐖𝐎𝐍
1- Kamewa har sai anyi aure, masu aurenma su tsaya ga matansu kawai.
2- Tabbatar da anyi gwajin cutar ga wadanda suke shirin aure, da nuna wa juna takardar shaida kafin a daura auren.
3- Tabbatarwa cewa jinin da za'a kara wa mutum angwada shi a asibiti an tabbatar ba ya dauke da kwayoyin cuta. tare da kaucewa karin jini a gurare ko clinics din da doka bata amince ba.
4- A wurin awon mata masu juna biyu ana auna wannan ciwon. Idan an samu mace da kwayar cutar ana daukar duk matakan da suka kamata wajen kare abin da take dauke da shi. Don haka ake tura mata awo.
5- A yanzu akwai alluran riga-kafin hana kamuwa da wadannan kwayoyin cutar wadanda hukumomin lafisa ke daukar nauyin sawa arika yiwa yara da zarar an haifesu cikin awa 24. sannan a maimaita a watanni na biyu dana shida na rayuwarsu...
6- Rigakafin baga yara ba kurum, har manya wadanda ke cikin hadarin kamuwa za'a iya yi muku allurar riga-kafin. Wadannan sun hada da ma’aikatan lafiya, musamman masu aiki a dakin gwajin jini, likitoci, mata masu zaman kansu, da mutanen dake aikin damara. Haka masu shirin aure wadanda daya ke da kwayar cutar amma daya bashi da ita, shi wanda baya dauke da kwayar cutar sai ayi masa riga-kafi. Ana samun wadannan allurai a asibitocin da Mata ke zuwa awo.
7- A tabbata an tafasa kayan kaifi kamar na wanzamai ko na mai yankan farce ko akonasu da wutar lighter ko a wankesu da sinadarin bleach ko alcohol sanitizer kafin ayiwa mutum amfani dasu. Sai dai idan sabuwa ce daga ledarta aka bare a gaban mutum.
8- Haka ma sirinji da reza, a rika tabbatarwa sababbi fil aka bare kafin amfani dasu.
9- Zuwa cibiyoyin gwaji na kyauta don sanin matsayin mutum na taimaka wa rage yada ciwon.
••••••••••~~~▪︎•●●■●●•▪︎~~~••••••••••
𝐖𝐀𝐒𝐔 𝐒𝐀𝐂𝐄 𝐋𝐈𝐊𝐈𝐓𝐀𝐍 𝐒𝐀𝐔𝐑𝐀𝐍 𝐑𝐔𝐊𝐔𝐍𝐈𝐍 𝐌𝐀 𝐙𝐀𝐌𝐔 ���𝐎 𝐉𝐈𝐍 𝐖𝐀𝐍𝐈 𝐀𝐁𝐔
Sauran rukunin dana bari Hepatitis A, da E suna da saukin yaduwa domin su suna iya yaduwa ta hanyar miyau, ruwan nono, hawaye da sauran body fluid. Amma su basu cika illah ba karara sannan ba'a cika samunsu da yawa ba, sun kuma fi yawa a tsoffi domin dama wasu kan rayu har su mutu batare da Viral load din yai yawan dazai cutar dasu ba. Shiko rukunin Hepatitis D nace muku ba'a samunsa sai ame B.
Amma duk da hakan kamuwa dasu ko ganosu a mai karancin shekaru hakan ba karamin hatsari bane domin suna lalata liver cells ne ahankali sui inflaming dinta wanda ke 6atata tare da karama mutum kusanci da wasu cuttukan shiyasa akeso mutum yai rigakafi dole.
••••••••••~~~▪︎•●●■●●•▪︎~~~••••••••••
𝐋𝐈𝐊𝐈𝐓𝐀 𝐍𝐀𝐉𝐄 𝐀𝐖𝐎 𝐀𝐍𝐆𝐀𝐍𝐎 𝐈𝐍𝐀 𝐃𝐀 𝐇𝐄𝐏𝐀𝐓𝐈𝐓𝐈𝐒 𝐁/𝐂 𝐓𝐀𝐘𝐀 𝐙𝐀'𝐀 𝐊𝐀𝐑���� 𝐉𝐀𝐑𝐈𝐑𝐈𝐍𝐀 𝐖𝐀𝐉𝐄𝐍 𝐇𝐀𝐈𝐇𝐔𝐖𝐀
Idan har aka gano kina dauke da ita alhalin kina da ciki... Abunda za'ai shine za'a saki ki gwajin (HBeAg Testing) wato Envelope na kwayar virus din. Shine zai taimaka aga irin yadda garkuwar jikinki ke mayarwa da kwayar martani, sannan ai (HBsAg Testing) agano yawan Viral load din da karfin Antibody din idan antibody din yai LOW virus din kuma HIGH toh dole tun kafin ki haihu afara baki magunguna koda baki fara nuna alamun ciwon ba domin gab kike da farawa.
Yayin da baya ga maganin anso ai miki Allurar (HBIG) Wato Hepatitis immunoglobulin antibody na kwayar virus din domin rage karfin yadashi zuwa ga jaririn yayin haihuwa. Ita wannan rigakafin tasha bamban da wacce kuke gani anayi a asibiti... yawanci mara lafiya ne zai sayota da kansa, ba iri daya bace data rigakafi. Haka yasa dole akesa mutum ya sayo a ajeta ta zamo Ready...... Zarar kika haihu dole shima jaririn ai masa ita kasa da awa 7 da haihuwa. Sannan akara masa da Hepatitis B vaccination wacce akeyi a asibiti cikin awa 24 da haihuwar jariri.... idan akai hakan toh insha Allahu jariri zai tsira daga ciwon duk da kina dashi.
Amma zarar ya zamto ba ai HBIG din can ba sai bayan Awa 12 da haihuwa toh gaskiya ko anyi bazatai wani tasiri ba domin window period din kwayar ajika bai wuce awa 11 shikenan.
Shyasa itama rigakafin ciwon hanta ake so aima yaro cikin awa 24 domin inya wuce hakan bazatai masa tasiri sosai ajika ba dole sai anbishi da Boosters dose.
••••••••••~~~▪︎•●●■●●•▪︎~~~••••••••••
𝐋𝐈𝐊𝐈𝐓𝐀 𝐙𝐀𝐌𝐔𝐈 𝐀𝐔𝐑𝐄 𝐌𝐔𝐍𝐉𝐄 𝐌𝐔𝐍𝐘𝐈 𝐆𝐖𝐀𝐉𝐈𝐍 𝐊𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐀𝐔𝐑𝐄 𝐀𝐍𝐆𝐀𝐍𝐎 𝐁𝐔𝐃𝐔𝐑𝐖𝐀𝐓𝐀 𝐍𝐀 𝐃𝐀𝐔𝐊𝐄 𝐃𝐀 𝐂𝐈𝐖𝐎𝐍 𝐇𝐀𝐍𝐓𝐀 𝐘𝐀 𝐊𝐄𝐍𝐀𝐍
Kamar yadda nace mukan bada shawarar gwaje-gwaje kafin aure ciki kuwa harda ciwon hanta domin kamar yadda nace zai iya yaduwa ta jima'i.
Abunda ya dace idan angano Macen ko namijin na dauke da virus din bazamu ce ku fasa auren juna ba amma dole zamu bukaci ku jinkirta lokacin auren zuwa watanni 7 harsai anyiwa dayan rigakafi baki daya.
Domin idan ma kunqi... toh karku manta kila yadda virus din yake hayayyafa ajikinki shi inya shiga jikinsa yafi haka saurin hayyafa, domin nace muku zafin ciwon ya bambanta tsakanin jiki zuwa jiki
Don haka anan koma waye dauke da ciwon walau Macen ko Namiji za'a duba (HBeAg) dinsa aga viral load din inyai yawan fara shan magani toh adorasa akai. Idan bai yawan fara shan magani ba toh nan ma za'a iya masa Rigakafin (HBIG) domin rage kaifinsa shikenan mutum ya cigaba da sha'aninsa. Yayin da kai kuma mara virus din za'a fara maka rigakafin ciwon hanta inda zaka karfi Allurai a lokuta mabambanta wato (0 - 1 - 6).
■ 0- Anan na nufin ranar farko na fara allurar da za'ai ma
■ 1- Na nufin bayan wata daya zaka dawo akuma yi
■ 6- Na nufin bayan wata 6 zaka dawo akara yi. Shikenan ka samu kariya.
Kunga kenan shyasa nace za'a jinkirta auren zuwa watanni 7 saboda saikai wata 6 kafin ka kammala dose din... Sannan inkana son karin immunity sosai kaima kana iya sayo immunoglobulin din aima don karin kariya.
••••••••••~~~▪︎•●●■●●•▪︎~~~••••••••••
Sannan da kokari wannan shine dunkulallen bayani akan ciwon hanta.... Kuyi hakuri bayanin yai tsayi amma nasan mahimmancinsa ya cancanci akaranta koda yafi haka. Allah ya kara mana lafiya.
••••••••••~~~▪︎•●●■●●•▪︎~~~••••••••••
💐
[Ibrahim Y. Yusuf]
[𝕴𝖇𝖗𝖆𝖍𝖎𝖒 𝖄. 𝖄𝖚𝖘𝖚𝖋]
0 Comments