LITTAFIN FIQHU DARASI NA BIYAR




YAUSHE MACE TAKE FARA JININ HAILA KUMA YAUSHE TAKE QAREWA?

Malamai sun yi saɓani dangane da iyakance daga wanne shekaru mace za ta fara jinin al’ada kuma zuwa wanne shekaru zai ɗauke.

1. Wasu malamai sun ce mace za ta fara jinin al’ada ne daga shekara tara (9) kuma za ta ƙare daga shekara hamsin (50). Saboda haka, duk jinin da mace ta gani kafin shekara tara (9) da wanda ta gani bayan shekara hamsin (50) wannan ba jinin al’ada ba ne, jinin ciwo ne.

2. Wasu malaman na biyu suka ce jinin al’ada shi ne jinin da yake zuwarwa mace, saboda haka duk lokacin da jini ya fara zuwarwa mace, ta kai shekara tara ko ba ta kai ba, ko da shekararta takwas (8) in dai jini ya dinga zuwar mata na al’ada, a lokacin al’ada ɗin, sai a ɗauka wannan matar ta fara al’ada kafin shekara tara (9). Sannan ana kuma samun ‘yan kaɗan daga cikin mata da suke fara al’ada kafin lokacin da mafi yawan mata suke farawa. Kuma akan sami wasu matan su gama al’ada lokacin da ragowar mata ba su gama ba, ko kuma ragowar mata sun gama su kuma su ci gaba da yin jinin al’ada. 

Saboda haka, muna iya kasa maganganun malaman zuwa kashi uku:
 Waɗanda suka ce babu iyaka dangane da fara jinin al’ada ko ɗaukewarsa. Don haka, duk jinin da mace ta gani kafin shekara tara (9) da bayan shekara hamsin (50) matuƙar ya zo a kan yadda ya saba na ala’da, wannan jinin al’ada ne.

Lallai fara jinin al’ada mafi yawa ko rinjaye a kan fara shi daga shekara tara (9) kuma a ƙare shi a shekara hamsin (50). Don haka dukkan jinin da mace ta gani kafin shekara tara (9) ko bayan shekara hamsin (50) wannan ba jinin al’ada ba ne, jinin ciwo ne; za ta ci gaba da neman magani, ta ci gaba da ibada.

Malamai na uku suka ce za a yi la’akari ne da al’ada da yanayin wuri. Idan ‘yan matan garin ko wurin sun saba yin al’ada kafin shekara tara (9) ko bayan shekara hamsin (50) to duk jinin da mace ta gani sai ta yi amfani da shi cewa jinin al’ada ne, saboda sa’anninta, ƙawayenta da ‘ya’yan maqota da suke yin hakan.

Wasu kuma suka ce abin ya danganta ne da yanayi na jikin mace da yanayi na ƙasar da take; wurin mai zafi ne ko mai sanyi ne, ko kuma yanayi na halitta, ko irin abincin da take ci, ko kuma irin gatan da take samu da kwanciyar hankali, wannan yana sa a fara al’ada da wuri ko ya ɗauke da wuri. 
Saboda haka dai a taƙaice, babu wani hadisi qwaya ɗaya tabbatacce wanda ya iyakance lokacin da za a fara al’ada, ko lokacin da za a gama. Saboda haka, abin ya ginu ne a kan bincike.

 Duk jinin da ya zowa mace, aka tabbatar ya zo a kan tsari na al’ada, sai a ɗauka al’adar ne ba tare da la’akari da shekarunta nawa ba. Haka idan jini ya ɗaukewa mace (ya daina zuwa), za a ɗauka cewa ta daina jinin al’ada ba tare da la’akari da shekarunta nawa ba.

Malaman da suke da wannan ra’ayi sun kafa hujjoji guda uku:
Hujja ta farko ya zo a nassin Al-qur’ani inda Allah ﷻ Ya ce:
﴿ وَيَسْأَلُونَكَ عَنِ المَحِيضِ قُلْ هُوَ أَذًى ﴾ () 
Ma’ana: “Suna tambayar ka game da al’ada, ka ce wannan ƙazanta ne.” Saboda haka, Allah ﷻ Ya gina hukunci ne a kan samuwar wannan jinin na haila, wanda Ya ce idan an same shi hukunci na nan, idan ba a same shi ba, hukunci ba ya nan, ba tare da la’akari da shekaru ba.

Hujja ta biyu ita ce hadisin Nana A’ishah (رضي الله عنها) lokacin da aka tambaye ta me ya sa mata masu yin haila idan sun gama suke rama azumi amma ba sa rama sallah? Sai ta ce, haka yake a zamanin Annabi ﷺ. Ya umarce mu mu rama azumi, amma ba ya umartar mu da mu rama sallah.” 

Hujja ta uku ita ce hadisin Nana A’ishah (رضي الله عنها) ta ce, “Manzon Allah ﷺ ya ce: “Idan hailarki ta gabato, to ki daina sallah, idan hailarki ta wuce, sai ki wanke wannan jinin, ki yi wanka, ki yi sallah.” 

Don haka a nan, Annabi ﷺ ya gina hukunci ne a kan zuwan haila da kuma ɗaukewar ta, ba tare da la’akari da shekaru nawa ba ne. Don haka a taƙaice jinin al’ada dangane da shekaru ba shi da iyakar yawa ko iyakar ƙaranci, an gina hukunci ne a kan samuwar jinin. Idan jini ya samu, hukunci yana nan, idan kuma babu jini babu hukunci, ba tare da la’akari da shekarun mace nawa ba ne.
Zamu ci gaba insha Allah.

Post a Comment

0 Comments