ABUBUWA 17 DA SUKE LALATA AURE.




1.KISHI MAI TSANANI. Idan kishi ya yi tsanani da yawa sai ya zama matsala ga mai shi da kuma wanda ake kishin a kansa.

2. SA IDO DA BIBIYA. SA ido muguwar sana'a, duk wanda ya sa maka ido, yake bibiyarka, ya ke neman aibinka ko kuskuran ka ko kasawar ka, ko laifinka, wannan ba masoyin ka bane na gaskiya.

3. NUNA FIFIKO DA ISA AKAN JUNA. Nuna fifiko da isa, yana jawo raini, da wulakanci, da rashin ƙimantawa babu kuwa mai son a wulakanta shi, duk sanda ma'aurata, miji ko mata ya raina abokin zamansa, to zama ba zai yiyuba a wannan hali, dole a sami cikas,

5 YAWAN ZARGI. Yawan zargi ba tare da dalili ba, yana rushe kauna, da aminci tsakanin ma'aurata, daganan sai dangantaka ta yi tsami har ya kai ga rushewar aure.

6. CIN AMANAR AURE. Cin amanar aure, daga miji ko mata, yana cikin manyan matsaloli da suke jawo mutuwar aure, da rashin yarda da juna ko da kuwa, mai aikata haka ya tuba.

7. SUKURKUCEWA ALAƘA DA ALLAH. Yawan sabon da kin bin umarnin Allah, na yi na yi bari na bari yana yin tasiri wajan rashin jin dadin zamantakewa ta aure, domin sabon Allah yana cire albarkar aure, da jin daɗin sa, akwai wani cikin ma gabata yana cewa idan muka sabawa Allah ta'ala, muna ganin sakamakon haka a cikin iyalanmu.

8. SON DUNIYA MAI TSANANI.MUGUN son duniya da rashin ɗaukar aure a matsayin kauna ta gaskiya da amana, ba don neman wani abu ba, yana lalata zaman aure, idan bukata ba ta biya ba.

9. BAYYANA SIRRIN AURE DA KAWAYE KO ABOKAI. Rashin ɓoye sirrin juna tsakanin ma'aurata, yana kawo cikas da taɓarɓarewar aure da sakwarkwacewar sa,

10. ƁANGARAN Ibada. Rashin ilmin addini da rashin kula da ibada musamman salla.

11. Ɓangaran halaye. Munanan halaye da rashin zaman lafiya yana sawa kowa ya gaji da abokin zaman sa har ya zama yana fatan a sami dalilin da zai raba ko mutuwar aure ko mutuwar abokin zaman ɗungurungun.

12.ƁANGARAN SADUWA. Ɓangaran saduwa. Rashin gamsar da juna da rashin ƙwarewar wajan sanin ilmin jima'i yana taka rawa wajan susucewar aure.
13. ƁANGARAN BANBANCIN Ra'ayi. Samun banbancin Ra'ayi na addini ko fahimta, ko siyasa, idan ba a kai zuciya nesa ba yana iya zama ummul abaisan rushewar aure.

14. Ɓangaran zamantakewa. Rashin iya zamantakewa da gane bambanci tsakanin halittar mace da namiji da kowa abinda zai iya da wanda ba zai iya ba, yana daga cikin ginshiƙi na zaman aure idan kuma ba a fahimci haka ba, zama zaiyi wuya.

15. ƁANGARAN TATTALIN ARZIƘI. Aure tsakanin masu arziƙi yana iya zama matsala a wani lokaci domin kowa zai ji shima ɗan wani ne, don haka ba babu risinawa juna yin haka yana bayuwa zuwa ga mutuwar aure.

16. CANGIN RAYUWA . Mutum yana da arziƙi ya talauce ko yana aiki ya rasa aikin, ko yana da lafiya, ya kamu da ciwo, ko yana da mulki ya ƙare, ko ƙarfin sa ya ƙare ko ƙuriciya ta ƙare ya tsufa, ko ya gamu da wata jarrabawa ta shiga wani halin matsi, ko duniya ta juya masa baya, duka waɗannan suna tasiri a cikin rayuwar aure a wasu lokuta har matsala suke zama,
17. RASHIN LAFIYA. Mai tsanani ko kamuwa da wani ciwo mai tsanani, ko wanda zai hana mu'amalar aure,

18. ƘULLA ALAKOKI DA WANI JINSHI. Idan namiji ko mace suka yi aure wajibi su bayyanawa juna wasu alaƙoki da suke yi da wasu mutane maza ko mata, domin kada zargi ya shiga, idan kuwa budurwa ce ko saurayi, dole a yanke wannan alaƙar tunda an riga an yi aure.

SHIGA KAYI REGISTER DA PALMPAY:
https://palmpay8.page.link/HEzP

Share ✅

Post a Comment

0 Comments